Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 8 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Sojojin Syria sun tsananta hare-hare a yankin Aleppo

    Sojojin Syria sun tsananta hare-haren da suke yi a wasu sassan Aleppo, a yayin da suke ci gaba da gwabza faɗa da mayaƙan Ƙurɗawa.

    An shiga kwana na uku ke nan da ake faɗa a birnin, tsakanin dakarun gwamnati da SDF. Dubban mutane sun rasa matsugunansu, kuma sojoji na ci gaba da kira ga fararen hula su fice daga wasu yankuna.

    Har yanzu ƙungiyar SDF ce ke iko da yankuna da dama na arewa maso gabashin Syria, kuma sun ki amincewa su haɗe da gwamnatin ƙasar da ke amfani da tsarin musulunci.

    Wata mazauniyar birnin kenan ta ce komai ya lalace, akwai mutane dayawa da suka so su tsere, amma suna fita aka soma harbi, dole suka koma gida.

  2. Bobi Wine ya buƙaci a dakatar da tallafin kuɗi da ake bai wa gwamnatin Museveni

    Babban ɗan takara na jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Uganda da za a yi a mako mai zuwa, ya yi kira da a dakatar da duk wani tallafin kuɗi da ƙasashen waje ke bai wa gwamnatin shugaba Yoweri Museveni.

    Bobi Wine ya ce tallafin ƙasashen waje na taimakawa wajen musgunawa ƴan adawa gabanin zaɓe.

    Tsohon mawaƙin da ya rikiɗe ya zama ɗan siyasa, ya zargi jam'ian tsaro da ci zarafin shi, ya kuma ce an tsare ɗaruruwan magoya bayansa a lokacin yakin neman zaɓe.

    Ya ce ƙasashen Yamma na da dokokin da za su iya amfani da su wajen lafta takunkumai kan ƙasashen da ke take haƙƙin biladama, da masu yi wa dimokradiyya zagon ƙasa, amma abin taƙaici ba su yi hakan ba.

  3. An tsare tsohon ministan Nijar Mamoudou Djibo kan zargin fyaɗe

    Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta ba da umurnin tsare Farfesa Mamoudou Djibo, tsohon minista a gwamnatin Bazoum, tare da miƙa shi gidan yari na Kollo, bisa zargin yi wa wata ɗaliba a makarantar sa fyaɗe.

    Iyayen ɗalibar ne suka shigar da ƙara inda suke zargin farfesan da aikata wannan laifi.

    Bayan gurfanar da shi, alƙaliyar kotun ta ba da umarnin tsare shi don ci gaba da bincike.

    Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma, inda wasu ke ganin bita da ƙullin siyasa ne, yayin da wasu kuma ke ganin lamarin abin damuwa ne wanda ya kamata a ɗauki mataki don kare haƙƙin ɗalibai 'yan mata daga cin zarafi da malamai ko wasu masu irin wannan ɗabi’a.

  4. Tawagar Super Eagles ta tafi Marakech domin buga wasan kwata-fainal

    Ƴan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya sun tafi birnin Marakech domin buga wasan kwata-fainal da za su fafata da tawagar ƙasar Aljeriya.

    Da farko dai an samun rahotannin da ke cewa ƴan wasan sun yi barazanar ƙin buga wasan matuƙar ba a biya su kuɗaɗen alawus ɗinsu ba.

    Sai daga baya shugaban hukumar wasanni ta Najeriya, Shehu Dikko ya ce an shawo kan matsalar, sannan jim kaɗan aka ga ƴan wasan suna hawa jirgi za su tafi birnin da za a buga wasan.

  5. Wace ce Renee Nicole Good, matar da jami'an tsaron Amurka suka harbe?

    Jami'an hukumar shigi da ficen Amurka da ke aiki a Minneapolis ne suka harbe Renee Nicole Good, wadda mahaifyar yara uku ce da ba ta daɗe da komawa garin da zama ba.

    Good mai shekara 37 fitacciyar mawaƙiyar baka ce, kuma mai sha'awar kaɗa jita, kamar yadda sanata mai wakiltar Minnesota, Tina Smith.

    Shugabanni a yankin sun bayyana Good a matsayin wadda take cikin masu sa ido kan ayyukan jami'an tsaro domin hana su wuce makaɗi da rawa, amma gwamnatin Trump ta bayyana ta da "ƴar ta'addar cikin gida.

  6. Amurka ta dakatar da duk wani tallafi ga Somaliya

    Hukumomin Amurka sun sanar da dakatar da duk wani tallafi da suke bai wa Somaliya, inda suka kawo dalilin zargin cewa wasu jami’an gwamnatin ƙasar sun lalata wani ɗakin ajiya da Amurka ta bayar da kuɗin gina shi sannan suka ƙwace ton-ton na abincin taimakon da aka nufa ga al’umma masu rauni.

    An rawaito cewa jami’an gwamnatin Somaliya ne suka bayar da umarnin lalata ɗakin ajiya a tashar jiragen ruwa ta Mogadishu ba tare da sanar da ƙasashen da suka bayar da gudummawa ba.

    Wannan lamari ya fusata hukumomin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, waɗanda suka ce idan har Somaliya tana son a dawo da bayar da tallafi, toh sai ta ɗauki alhakin abin da ya faru.

    Ba a bayyana adadin tallafin da wannan dakatarwa zai shafa ko tsawon lokacin da zai ɗauka ba.

    Wannan mataki zai ƙara wa ƙasar wahala a wani lokaci da take fama da matsalar yunwa sakamakon rage tallafi na kwanan nan.

    Har yanzu hukumomin Somaliya ba su mayar da martani kan zargin ko kan dakatarwar tallafin ba.

  7. Sojojin Lebanon sun fara shirin kwance ɗamarar Hezbollah

    Rundunar sojin Lebanon ta ce ta kammala mataki na farko a shirinta na kwance ɗamarar ƙungiyar Hezbollah, sai dai isra'ila ta yi gargaɗin cewa akwai babban aiki a gaba.

    Sojojin sun ce a yanzu haka an ƙwace dukkanin makaman da ba a hannun gwamnati suke ba a kudancin ƙasar.

    Hezbollah ta daɗe da mamaye yankin, har ta amince da tsagaita wuta da Israila a 2024.

    Sai dai ƙungiyar ta yi ta ƙin amincewa ta miƙa makamanta a wani ɓangare naa yarjejeniyar.

    Ana ta samun rahotanni a Isra'ila da ke nuna cewa shugaba Trump ya bai wa Firaminista Benjamin Netanyahu, damar faɗaɗa ayyukunsa na soji kan Hezbollah a Lebanon.

  8. An kama tsohon ministan kuɗin Ghana, Ken Ofori-Atta a Amurka

    Hukumar Shige da Fice ta ƙasar Amurka (ICE) ta kama tsohon ministan Kudin Ghana, Ken Ofori-Atta, sakamakon wasu matsaloli da suka shafi bizarsa ta shiga ƙasar

    Lauyoyinsa na Ghana, Minkah-Premo da Osei-Bonsu, Bruce-Cathline da Abokan Huldarsu (MPOBB), sun bayyana a wata sanarwa ranar Laraba cewa tsohon ministan na bai wa hukumomin Amurka haɗin kai yayin da tawagar lauyoyinsa a Amurka ke aiki tukuru don tabbatar da sakin sa.

    Sanarwar ta kara da cewa, tsohon ministan kuɗin ya miƙa takardar neman a gyara masa bizarsa domin samun damar ci gaba da zama a ƙasar ko da wa'adin bizar ya ƙare

    A Ghana, Ofori-Atta da wasu na fuskantar tuhume-tuhume guda 78 na cin hanci da rashawa da sauran laifuka, ciki har da shirin aikata zamba a harkar sayen kaya da janyo asarar kuɗi ga gwamnati.

    Ana zargin tsohon ministan da yin amfani da muƙaminsa wajen biyan kamfanin Strategic Mobilisation Ghana Limited (SML) fiye da dala miliyan ɗaya ba tare da hujjar ayyukan da aka yi ba.

    Hukumomin Ghana sun nemi a miƙa shi ga ƙasar, amma lauyoyinsa sun ƙalubalanci hakan.

    Ghana dai na da kyakkyawar dangantaka da Amurka, kuma a baya bayan-nan ƙasashen biyu sun yi aiki tare wajen mayar da ‘yan Afirka ta Yamma gida.

    Ofori-Atta ya yi balaguro zuwa Amurka ne domin neman magani.

  9. Ƴan kasuwar dabbobi a Katsina sun koka kan ƙarin haraji

    Ƴan kasuwar dabbobi da hatsi a jihar Katsina sun nuna damuwa kan ƙarin harajin da gwamnatin jihar ta yi, inda suka ce bai dace ba ganin halin da kasuwanci ke ciki.

    Gwamnatin jihar dai ta sabunta dokokin tattara kuɗaɗen shiga domin daidaita su da yanayin farashin kayayyaki a jihar, sai dai ‘yan kasuwar sun bayyana cewa ƙarin ya yi yawa fiye da ƙima.

    Abdu Abdu, mai hada-hadar dabbobi a kasuwar Mai’Adua, ya ce: "Yanzu ba lokaci ne na ƙara wa kasuwanci nauyi ba, lokaci ne na kawo dabarun bunƙasa kasuwanci da tattalin arziki."

    Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa da masu rajin ci gaban al’umma reshen karamar hukumar Mai’Adua, Muhammad Yusuf ya ce duk da cewa suna maraba da tsarin, ba haka ya kamata a fara aiwatar da shi ba.

    Sai dai shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jihar, Alhaji Muhammad Isyaku, ya bayyana cewa dole ne a ci gaba idan aka yi la’akari da canje-canjen harkokin kasuwanci.

    "Manufarmu ita ce samar da isassun kuɗaɗe domin gwamnati ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kyautata kasuwanni da inganta harkokin tsaro," in ji shi.

  10. Mece ce matsayar ACF kan ƴantakarar shugaban ƙasa ga Arewa a zaɓen 2027?

    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF, ta bayyana wasu tsare-tsare kan arewa ga masu neman takarar shugaban kasa a zaɓen 2027.

    ACF mai fafutukar kare muradun yankin arewaci ta ce ba za ta fito fili ta nuna goyon baya ga wani ɗantakarar shugaban ƙasa daya ba a zaben 2027, kamar yadda Farfesa Tukur Muhammad-Baba sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ya shaida wa BBC.

    Sai dai ya ce za su diba kuɗurorin ƴantakarar da manufofinsu da kuma alƙawuran da suka ɗauka.

    Ya ƙara da cewa nan da watanni masu zuwa ACF za ta gana da masu neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar ɗaya bayan ɗaya, don ta tantance manufofi da tanade-tanaden da kowannesu ya yi wa yankin na arewa idan ya ci zabe.

  11. Venezuela za ta sayi kayayyakin Amurka da kuɗin man fetur ɗinta - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Venezuela ta amince ta yi amfani da kuɗin da za a samu daga sayar da manta, ta rinka sayen kayan da aka yi a Amurka kawai.

    A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta Trump ya ce, kayan da za ta rinka saya, za su haɗa da kayan gona, da magunguna, da kuma na'urori don inganta cibiyoyinta na samar da makamashi.

    A halin da ake ciki kuma ministan harkokin cikin gida na Venezuelar, Diosdado Cabello, ya ce mutum 100 da suka haɗa da fararen hula, suka mutu a harin da Amurka ta kai ranar Asabar, lokacin da ta kama Shugaban ƙasar Nicolas Maduro, ta yi gaba da shi zuwa kasarta.

    Ya ce matar Maduron, Cilia Flores ma ta ji rauni a kai a lokacin da sojojin ke kama ta.

  12. Majalisar jihar Rivers ta sake ƙaddamar da shirin tsige Fubara

    Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake ɗaukar zafi bayan majalisar dokokin jihar ta sake ƙaddamar da shirin tsige gwamna Siminilaya Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu.

    An bijiro da maganar tsige gwamna ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026.

    Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya karanta takardar neman majalisar ta ƙaddaamar da shirin tsige gwamnan, bisa zargin shi da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.

    Ya ce sun yi la'akari da sashe na 188 ne na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tattarawa da tantace laifukan da suke ganin gwamnan ya yi, waɗanda kuma suke ganin sun saɓa da doka.

    Daga cikin laifukan da suke zargin shi da aikatawa akwai:

    • Rushe majalisar dokokin jihar
    • Kashe kuɗin da ba a kasafta ba
    • Riƙe kuɗin gudanar da ayyukan majalisa
    • Ƙin yin biyayya ga umarnin kotun ƙoli na bai wa majalisar ƴancin kanta
    • Naɗa muƙamai ba tare da amincewar majalisar ba

    Ƴan majalisar guda 26 ne suka sanya hannu a takardar buƙatar, sannan shugaban masu rinjayen ya miƙa takardar ga shugaban majalisar.

    Shugaban majalisar, Amaewhule, ya ce za su miƙa takardar zuwa ga gwamnan a cikin kwana bakwai.

  13. Jami'an shige da ficen Amurka sun kashe wata mata a yunƙurin kamata

    Jami’an shige da ficen Amurka (ICE) sun harbi wata mata mai shekaru 37, Renee Nicole Good, a birnin Minneapolis yayin da suke yunƙurin kamata abin da ya haifar da zanga-zanga a daren ranar Laraba.

    Hukumomin tarayya sun zargi cewa matar ta so ta take jami'an da motarta ne a yanƙurin kaucewa kamata.

    Amma kuma magajin garin Minneapolis a Amurka, ya yi watsi da bayanan da gwamnatin Trump ta bayar na yadda jami'in ya harbe ta a birnin.

    Jacob Frey, ya ce, hoton bidiyon yadda lamarin ya faru ƙarara ya saɓa da bayanan da fadar gwamnatin Amurkar ta fitar cewa jami'in ya harbi Renee Good ne domin kare kansa.

    Hoton bidiyon dai ya nuna yadda jami'in ya harbi matar, da rahotanni suka ce 'yar Amurka ce, a lokacin da take kokarin tserewa a mota, yayin da jami'an shige da ficen ke kokarin tsayar da ita.

    Daruruwan mutane ne suka yi cincirindo, domin nuna alhini da Allawadarai a wajen da aka harbe ta, suka kunna kyandira tsawon dare.

    A birnin New York ma an gudanar da zanga-zanga.

    FBI na gudanar da bincike kan lamarin.

    An tura daruruwan jami’an ICE zuwa Minneapolis, a jihar Minnesota ne a wani ɓangare na matakan fadar White House na hukunta masu shige da fice cikin ƙasar ba bisa ka’ida ba.

  14. ICPC za ta ci gaba da binciken shugaban NMDPRA duk da Dangote ya janye ƙorafinsa

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike kan tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA), Farouk Ahmed, duk da cewa attajiri mafi kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya janye ƙorafin da ya shigar a kansa.

    Lauyan Dangote, Ogwu Onoja, ne ya aika takardar janye ƙorafin zuwa ga ICPC.

    Dangote dai ya buƙaci hukumar ta binciki Ahmed a watan Disamban 2025 kan zargin amfani da muƙaminsa wajen satar kuɗaɗen gwamnati, inda ya ce yana da hujjoji da suka tabbatar da zarginsa.

    Sai dai, mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya bayyana cewa duk da janyewar ƙorafin, hukumar za ta ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiya da adalci da kuma yaƙi da cin hanci a Najeriya.

    Odey ya ƙara da cewa ci gaba da binciken zai nuna cewa hukumar na yin aikinta ba tare da la’akari da matsayi ko shaharar mutum ba.

  15. Iran ta rataye mutumin da ake zargi da yi wa Isra’ila leƙen asiri

    Sashen yaɗa labarai na ma'aikatar shari’ar Iran ya sanar da rataye wani mutum mai suna Ali Ardestani bisa zargin yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad, aiki.

    An yanke hukuncin ne a a jiya Laraba.

    A cewar Mizan, Ardestani ya kasance “babban jigo” na Mossad a cikin Iran, inda ya tattara tare da tura muhimman bayanai game da ƙasar zuwa Isra’ila.

    Rahoton ya ce yana ɗaukar hotuna da bidiyo na wasu wurare na musamman tare da tattara bayanai kan batutuwa masu matuƙar muhimmanci, sannan ya miƙa su ga Isra’ila domin musayar kuɗin intanet ta Crypto, da nufin samun bizar Birtaniya da ladan kuɗi har dala miliyan ɗaya.

    Ma'aikatar shari’ar ba ta fitar da hotonsa ba, kuma ba ta bayyana lokacin da aka kama shi da tsawon zaman da ya yi a tsare ko wurin da aka aiwatar da hukuncin ba.

    Wannan shi ne karo na biyu da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa kan irin wannan zargi cikin ‘yan watannin baya, bayan rataye Aqeel Keshavarz a ranar 19 ga Disamba bisa zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri da ɗaukar hotunan wuraren soja da tsaro.

  16. Iran ta gargaɗi Amurka kan taimaka wa masu zanga-zanga a ƙasar

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da kuma bayyana goyon bayan da manyan jami’an Amurka ke nunawa ga zanga-zangar da ke faruwa a ƙasarta a kwanakin baya a matsayin “tsoma baki da kuma yaudara.”

    A cikin wata sanarwa da gwamnatin Iran ta fitar, ta ce: "Matakan da Amurka ke ɗauka ba wai saboda tausayi ga mutanen Iran bane,sai dai domin sanya matsi da yin baraza da kuma katsalanda a al'amarun cikin gida na Iran domin tayar da tarzoma da tashin hankali, da haifar da rashin tsaro a ƙasar."

    Iran ta kara da cewa, "Abin da gwamnatin Amurka ke yi a yau ba kawai yaƙin tattalin arziki bane, har ma da yaƙi na tunani da yaɗa labaran ƙarya da barazanar shiga kai tsaye na soja, da kuma ƙarfafa tashin hankali."

    A cikin kwanaki 12 da suka gabata, manyan jami’an Amurka, ciki har da Shugaba Donald Trump, sun yi kira ga gwamnatin Iran da ta daina “kashe” masu zanga-zanga.

    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce zanga-zangar na nuna “fushin mutanen Iran” kan rashin iya samar masu rayuwa mafi kyau."

  17. Trump ya ba da umarnin ficewar Amurka daga hukumomin duniya 66

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu a wata takarda da ke ba da umarnin janyewar ƙasar daga wasu hukumomi na duniya har guda 66.

    Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa daga cikin hukumomin da abin ya shafa akwai 31 na Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda ta ce ayyukansu ba sa tafiya da muradun Amurka.

    Sauran hukumomin MDD da ke cikin jerin sun haɗa da masu kula da shirye-shiryen lafiyar iyali da lafiyar mata da yara da wanzar da zaman lafiya da kuma yaƙi da cin zarafin mata a lokutan rikice-rikice.

    Wasu daga cikinsu kuma na aiki ne kan batutuwan sauyin yanayi da ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

  18. Ƙasashe biyar da Trump zai iya kai wa hari bayan Venezuela

    Babban abin da ke ɗaukar hankali a wa'adin mulkin shugaban Amurka Donald Trump na biyu shi ne muradunsa na harkokin ƙasashen waje.

    Ya aiwatar da barazanar da ya yi wa Venezuela ta hanyar kama shugaban ƙasar da matarsa a gidansu da ke Caracas a wani hari da Amurka ta kai ƙasar cikin dare.

    Amurka dai ta gabatar da Shugaba Maduro da mai ɗakinsa a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda huɗu masu alaƙa da safar miyagun ƙwayoyi da makamai.

    Sai dai Mista Maduro ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa.

    Baya ga Venezuela akwai ƙasashe da dama da Trump ke nuna wa yatsa, wani abu da masana ke hasashen cewa komai zai iya faruwa da su.

  19. Assalamu alaikum

    Barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin na labaran BBC Hausa kai-tsaye.

    A yau ma za mu ɗaura ne daga inda muka tsaya a jiya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.