Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC. Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya nuna mana.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 22 ga watan Yuli, 2025.
Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC. Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya nuna mana.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Mutane na amfani da hannu wajen tono mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa sakamakon ruftawar wurin haƙar ma'adinai a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo.
Akwai rahotannin da suke ce an zaƙulo aƙalla gawarwaki 12, kuma ba a kammala tantance masu haƙar ma'adinai nawa ne suka ɓata ba.
Ranar Lahadi ramuka da dama sun rufta a wurin haƙar zinare na Lomera Gold.
Wani rahoton ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya ya gano yadda ƙungiyar ke samun dubban daloli kowanne wata ta hanyar karɓar harajin ma'adinai da ake aika wa Rwanda, zargin da ƴantawayen M23 da gwamnatin Kigali suka ƙaryata.
Da alama tsagaita wuta mai rauni na ci gaba a lardin Sweida bayan rikicin makwonni da ya kashe sama da mutum 1200.
Yankunan mabiya addinin Druze sun zargi gwamnatin Syrya da raɓewa da Larabawa mazauna karkara don kashe farar hula mabiya addinin Druze.
Ganau sun bayyana yadda aka jefo mutane daga rufin asibitin birnin Sweida ya kuma yadda aka harbe majinyata.
Wakilin BBC da ya ziyarci asibitin ya ga gomman jakunkunan ƙunshe gawarwaki yayin da ake fita da su.
Jam'iyyar hamayya a Najeriya, African Democratic Congress wato ADC ta batun da gwamnatin Najeriya ke yi cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar wato GDP ya bunƙasa, ba zai amfani ƴan ƙasar ba, lamarin da jam'iyar ta ce yaudara ce kawai gwamnatin ke yi ta hanyar fitar da lambobi.
Kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ne bayyana hakan wata sanarwa da jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito, inda ya ce cewa cewa tattalin arzikin ciki na ƙasar ya bunƙasa, "kwaskwarima" ne kawai, wanda ba ya inganta rayuwar ƴan ƙasar a zahiri, ballantana ya inganta tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce a daidai lokacin da gwamnatin ke murnar tattalin arziki na cikin gidan ya bunƙasa, "miliyoyin ƴan Najeriya na cigaba da fama da hauhawar farashin kayayyaki da ƙangin talauci da rashin abubuwan more rayuwa."
"Haɓakar tattalin arziki ta wuce fitar da lambobi domin nuna tamkar gwamnati na ƙoƙari. Bunƙasar tattalin arziki ba shi da amfani matuƙar mafi yawan ƴan ƙasar ba su gani a ƙasa ba wajen samun abinci mai rahusa da samun sauƙin kayayyaki," in ji ADC.
Ƴanbindiga sun kashe wasu mutane, waɗanda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a iya ƙididdigewa ba, sannan suka yi garkuwa da wasu da dama a ƙaramar hukumar Bakura ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Kafar Daily Post mai zaman kanta ne ta ruwaito hakan, inda ta ce maharan sun kai harin a garuruwan Dogon Madaci da Tungar Lawal da Rafin Samu a ranar 21 ga watan Yulin, kamar yadda kafar ta ruwaito daga wani mai suna Bakatsine a shafin X.
Zamfara na cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro a arewacin Najeriya, inda ƴanbindiga da Boko Haram da ƴan Lakurawa.
Ƙungiyar kare haƙƙi Bil'Adam ta Amnesty International ta nemi a binciki mummunan harin da Isra'ila ta kai wani gidan yari a Iran a watan da ya gabata a matsayin laifin yaƙi.
Hukumomin Iran sun ce mutum 79 aka kashe a gidan yarin na Evin, wanda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'Adama suka ce yana ɗauke da fursinonin siyasa da ƴan ƙasashen waje.
Amnesty ta dage cewar harin ba shi da nasaba da dokar sojoji kuma ya karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Iran ta ce mutum 1062 aka kashe ya yin fafatawar kwana 12 da Isra'ila.
Mutum 28 aka kashe a ɓangaren Isra'ila, wadda ta ce ta kai hari Iran ne don ta hana ƙirƙirar makaman nukiliya.
Tehran dai ta dage ta na shirinta na nukiliya ne don zaman lafiya.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da wani ƙarin bayani kan ƴan Najeriya da ke son zuwa Amurka da kuma waɗanda ke zaune a can.
Ofishin ya ce yana koƙarin ganin ya yi yaƙi da zamba da kuma shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
A wani bayani da ofishin jakadancin ya wallafa a shafin sada zumunta, ya ce za a haramta wa duk wani da aka kama da laifin aikata rashin gaskiya wajen samun takardar shiga Amurka - shiga ƙasar har abada.
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce aƙalla 33 ne suka mutu sakamakon tsananin yunwa a yankin cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Shugaban Hukumar Kula da ƴangudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya samu rahotannin yadda jami'ai da likitoci da ƴanjarida suka suma saboda yunwa da wahala.
Philippe Lazzarini ya bayyana cibiyar rabon kayan agaji mai sarkakiya wadda Amurka da Isra'ila ke goyon baya a matsayin tarkon mutuwa, biyo bayan yadda aka kashe ɗaruruwan mutanen da ke neman taimako. Ƙungiyar Likitoci ta Isra'ila ya nemi sojojin Isra'ila su bari kayan agaji su isa cikin Gaza.
Hukumomi a Bangladesh sun ce adadin mutanen da suka mutu a ya yinda wani jirgin yaƙi ya rikito a wata makaranta ranar Litinin ya kai 31, kuma da dama daga cikinsu yara ne.
Haka kuma wasu 165 sun samu raunuka a kwalejin Milestone da ke Dhaka.
An gudanar da zanga-zanga a yankin da jirgin ya faɗo yayinda fusatattun ɗalibai suka yi wa mashawarta firaministan riƙon ƙwaryar Bangladesh ƙawanya.
Wakiliyar BBC ta ce azuzuwan makarantar za su iya ɗaukar ɗalibai 30 zuwa 40, lokacin da jirgin ya rikito ɗalibai da dama na ciki tare da malamai.
Tuni dai jami'ai suka ce jirgin ya fuskanci tangarɗar na'ura.
Ministan tsaron Ghana ya ce gwamnatin ƙasar za ta ƙaddamar da bincike kan yadda 'dubban harsasan sojojin ƙasar suka ɓace' kafin babban zaɓen ƙasar da aka yi a watan Disamban 2024.
Dr Edward Omane Boamah ya bayyana haka a taro bayyana nasarorin ma'aikatun gwamnatin ƙasar, inda ya ce, "muna ba tsaron ƙasarmu muhimmanci, don haka dole mu bincika yadda aka fita da dubban harsasai gab da zaɓen 2024."
Dr Omane Boamah ya bayyana wa ƴanjarida cewa, “ma'aikatar tsaron Ghana ce ta ba sakatariyar tsaron ƙasar umarni binciken abin da ya faru."
Tun a watan Fabrairu ne shugaban ƙasar, John Mahama ya yi gargaɗin cewa ana samun ƙaruwar yawaitar makamai a hannun mutanen ƙasar.
Zirin Gaza na cigaba da fama da ƙuncin rayuwa a sanadiyar rashin shigar da isasshen kayan agaji tun bayan da Isra'ila ta fice daga yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.
Ga wasu hotunan layin ruwa, wanda ke nuna halin da zirin ke ciki.
Jam’iyyar ADC mai hamayya a Najeriya ta soki yadda gwamnatin APC ta shugabar Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da jan kafa wajen nada jakadun kasar a kasashen waje, tun bayan janye jekadun 109 a shekarar 2023.
Jam’iyyar ta gargadi kasar da cewa wannan matakin zai iya bata kimar Najeriya a idon duniya. Sai dai tun tuni gwamnatin ta bayyana matsalar kudi a matsayin babban dalilin faruwar hakan.
Alhaji Ladan salihu, ɗaya ne daga jiga-jigan jam'iyyar ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ƙsar ba ti yi wa ƴan Najeriya Adalci ba harda waɗanda suke zaune a ƙasashen waje da harkoki da ayyukan diflomasiyya waɗanda suka dogara kacokan kan kasancewa waɗannan jkadun.
"Idan aka tuna, an samu masaloli kan batun biza a kwanakin nan a tsakanin Najeriya da Amurka wanda ya fi ƙamari a ɓangaren Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa."
BBC ta tuntuɓi ɓangaren gwamnatin Najeriya kan wannan batu, amma hakan ta ci tura.
Amma a wata hira da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da gidan talabijin ta Arise ya ce gwamnatin shugaba Tinubu na fuskantar babban matsalar kuɗi da na tattalin arziƙi wadda ita ce silar kasa naɗa jakadun.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta bayyana sabbin alƙaluma kan mace-macen Falasɗinawa sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Wata mai magana da yawun ma’aikatar ta ce mutum 33, ciki har da yara 12 ne suka mutu cikin sa'o'i 48 da suka wuce.
Ta ƙara da cewa, jimillar mutanen da suka mutu sakamakon yunwa tun bayan fara yaƙin a shekarar 2023 ya kai 101, inda daga cikinsu yara 80 ne.
A ranar Litinin ne Datti Baba-Ahmed ya kai wa ɓangaren shugabancin Julius Abure na jam'iyyar Labour ziyara a Abuja.
Datti wanda ya yi ya jam'iyyar ta LP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shugaban Najeriya na 2023, ya ce zai jagoranci tattaunawar sasanci tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar a 2023, Peter Obi da kuma wasu masu ruwa da tsaki, da nufin sake haɗa kan jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
"Labour ba jam'iyya ba ce da mutum zai fice daga cikinta," in ji Datti yayin da ya gana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Abure.
Julius Abure shi ke jagorantar wani ɓangare na jam'iyyar LP da ke iƙirarin zama sahihin shugabancin jam'iyyar, wanda kuma ke takun tsaka da ɓangarensu su Peter Obi.
A ranar Talata ne jami’an tsaro suka hana jerin gwanon motocin sanata Natasha Akpoti-Uduaghan shiga zauren majalisar tarayya, lamarin da ya sa ta sauka daga motarta ta taka ta shiga harabar majalisar tare da wasu magoya bayanta.
Sanatar wadda aka dakatar da ita na watanni shida ta yi niyyar komawa bakin aiki yau Talata - bayan kotu ta umarci majalisar ta mayar da ita.
Sai dai lokacin da motarta ta isa majalisar, jami’an tsaro sun hana ta wucewa abin da ya janyo ce-ce-ku-ce yayin da magoya bayanta suka fara ihu suna ƙoƙarin kutsawa zuwa cikin majalisar.
Wani alƙalin kotu a Amurka ya ɗage wata dokar kariya da ke hana gwamnatin Amurka kwashe dubban 'yan Kamaru da Afghanistan daga ƙasar.
Wannan mataki na iya bai wa gwamnatin damar fara ƙoƙarin mayar da su zuwa ƙasashensu.
Dubban 'yan ƙasashen biyu na da wannan kariyar wanda ke hana a mayar da su saboda fargabar rashin tsaro a ƙasashensu. Sai dai wannan hukunci na iya fuskantar ƙalubale daga kotu a gaba.
Manoman shinkafa da masara a Najeriya na fargabar za su iya tafka asara sakamakon tsadar taki da sauran kayan aikin noma.
Wasu manoman kuwa sun hakura da noman shinkafar kacokan sun koma noman wani abu daban, saboda a cewarsu tsadar taki ba za ta bari su samu riba ba.
Wannan dai na zuwa ne duk da iƙirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta rage farashin takin zamani ga manoma a sassan ƙasar don tallafawa harkokin noma.
Wani manomi a jihar Jigawa, Alh. Muhammad Idris ya shaida wa BBC cewa ya kashe kuɗi har naira miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas wajen siyan taki da zai yi noma da shi da kuma kuɗin banruwa a kowacce kadada.
"Duk da kuɗin da na kashe wajen noma, gaskiyar magana itace babu ribar da zan samu idan aka yi la'akari da tsadar taki da ya tashi da kuma shi kansa shinkafar, nawa ake sayar da ita yanzu?" in ji Alh. Idris.
"Aƙalla, mafi ƙanƙanta na shinkafa idan aka noma a samu buhu daga 40 zuwa 60 a hecta, saboda haka idan mutum ya duba kuɗin da ya kashe, mutum zai ga babu wata riba."
Rahotanni daga sassan Najeriya na cewa wasu manoman sun dena noman masara da shinkafa inda suka koma noman gero da dawa da rogo da kuma riɗi gadan-gadan.
Alh. Idris ya kuma ce yana kira ga gwamnatin ƙasar ta duba harkar noma ta waiwaiyo kan manoma ta hanyar saka tallafi kan taki domin sun dinga siyansu cikin sauƙi da kuma samar musu da maganin ciyawa cikin sauƙi.
Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya dakatar da shugaban sashin masu gabatar da ƙara na lardin Gauteng, Andrew Chauke daga bakin aikinsa.
An dakatar da shi ne saboda zarge-zargen gazawarsa wajen gudanar da bincike kan manyan laifukan cin hanci da rashawa na siyasa.
A jiya da darene shugaban ya dakartar da shi.
Ramaphosa ya ce kasancewarsa a ofis na iya ɓata sunan hukumar gabatar da ƙara ta ƙasa yayin da ake jiran bincike don tantance ko yana da cancanta ya ci gaba da riƙe mukamin.
An yanke wa wani tsohon dansanda farar fata a Amurka hukuncin ɗaurin watanni talatin da uku a gidan yari bayan samunsa da laifin hannu a farmakin yansandan da ya kai ga harbe wata baƙar fata mai suna Breonna Taylor.
Kisan da aka yi shekaru biyar da suka gabata ya haifar da zanga-zanga da neman yin gyara ga tsarin ƴansanda.
Mista Hankinson, wanda aka yankewa hukuncin ya yi iƙirarin cewa ya yi harbin ne domin kare abokan aikinsa bayan da saurayin Ms Taylor ya buɗe masu wuta.
Hankinson ya yi harbi sau goma a lokacin farmakin, amma bai samu Miss Taylor ba.
An same shi da laifin ƙeta hakkinta
Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun ce suna iya dakatar da ayyukansu na samar da wuta saboda tarin bashin da ya haura naira tiriliyan 5.2 da har yanzu gwamnati ba ta biya su ba, wanda ke barazana ga cigaban aikinsu na samar da lantarki a ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da lantarkin, Dr. Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun jima suna nuna kishin kasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.
Ta ce akwai sabon bashi da ya kai naira tiriliyan 1.2 daga wutar da aka samar a farkon rabin shekarar 2025, wanda ya ƙaru kan bashin da suke bin gwamnati zuwa naira tiriliyan 5.2.
Wannan ya haɗa da naira tiriliyan 2 daga shekarar 2024 da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 da ya kai naira tiriliyan 1.9.
A cewarta, “Kuɗin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kai wa naira biliyan 250, amma gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗi ba.”.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce "gwamnati na ƙoƙarin rage wani bangare na bashin, amma ba a bayyana yadda hakan zai faru ba.