Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 10/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Rabiatu Runka, Isiyaku Muhammad, da Umar Mikail

  1. Yadda ake aikin ceto mutane daga ɓarnar harin Isra'ila

    Beirut

    Asalin hoton, EPA

    Hotunan da muka samu daga kamfanonin dillancin labarai na nuna yadda ma'aikatan agaji ke ta ƙoƙarin zaƙulo mutane daga ɓaraguzai a Beirut bayan harin Isra'ila.

    Harin ya lalata wasu gidaje a tsakiyar birnin.

    Wakilin BBC a Beirut ya ce suna ganin mutane na dudduba ɓaraguzai a cikin duhu da zimmar ceto waɗanda gini ya danne.

    Zuwa yanzu mutum 18 ne suka mutu tare da raunata wasu kusan 100, a cewar hukumomin Lebanon.

    Beirut

    Asalin hoton, EPA

    Beirut

    Asalin hoton, EPA

  2. Labarai da dumi-dumi, Mutanen da suka mutu a harin Isra'ila na Beirut sun kai 18

    Cikin 'yan mintunan da suka gabata, Isra'ila ta kai hari tsakiyar birnin Beirut na Lebanon.

    Da farko an bayar da rahoton mutuwar mutum 11, inda a yanzu hukumomin ƙasar suka ce mutanen sun zama 18.

    Kazalika, waɗanda aka raunata a harin sun kai 90.

    Karo biyu jiragen yaƙin Isra'ila na kai wa unguwar Bachoura hari - wata unguwar 'yan Shia da Hezbollah ke da jama'a.

    Harin ya girgiza dogayen gine-ginen da ke tsakiyar birnin.

  3. NNPCL ya nemi afuwar 'yan Najeriya kan ƙarin kuɗin mai

    NNPCL

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPCL ya kare matakin da ya dauka na ƙara kuɗin man fetur a karo na biyu cikin wata guda.

    Lawal Sade, shugaban NNPCL Trading - sashen kasuwanci da cinikayya na kamfanin - ya nemi afuwar 'yan Najeriya game da matakin ƙarin.

    Ya ce hakan ta faru ne saboda yanayin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma yanayin canjin kudin waje.

    Sai dai ya ce NNPCL na wa 'yan Najeriya albishir cewa farashin zai iya saukowa idan sauran matatun mai na cikin gida suka fara aiki gadan-gadan.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari bayanin da ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku saurari bayanin da ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:
  4. Binciken MDD ya ce Isra'ila da Hamas sun aikata laifukan yaƙi

    Wani kwamatin bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta kafa ya ce ya gano hare-haren da Isra'ila ta dinga kaiwa kan cibiyoyin lafiya da a Gaza da kuma wulaƙanta Falasɗinawan da aka tsare laifukan yaƙi ne.

    Cikin rahoton sabon binciken da tsohon shugaban hukumar kare haƙƙi ta MDD, Navi Pillay, ya ce "Isra'ila ta tsara lalata fannin lafiyar Gaza a matsayin yaƙi, inda ta aikata lafukan yaƙi da na lalata rayuwar ɗa'adam ta hanyar kai hari da gangan".

    Rahoton ya ce an tsare dubban mutane ciki har da yara, kuma aka "dinga cin zarafinsu akai-akai" ta hanyar azabtarwa, da fyaɗe.

    Haka nan, ya gano cewa an ci zarafin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza, "ciki har da duka, da lalata, da tilasta musu zaman kaɗaici, hana su tsaftace jikinsu, hana su ruwan sha da abinci, da yi musu barazana da wulaƙanci".

    MDD ta ce Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa sun aikata laifukan yaƙi da kuma kuma lalata rayuwar ɗan'adam.

  5. Sojojin MDD da Isra'ila ta raunata 'yan Indonesia ne

    Dakarun rundunar Unifil

    Asalin hoton, UNifil

    Mun samu rahotonnin da ke cewa dakaru biyu na MDD da Isra'ila ta raunata a kan iyakar Lebanon 'yan ƙasar Indonesia ne.

    Wani mai magana da yawun MDD ne ya tabbatar da hakan.

    Ƙasar ta Indonesia ta fi kowacce bayar da gudummawar dakaru a rundunar Unifil da dakaru sama da 1,200.

    Zuwa yanzu ba mu ji daga bakin gwamnatin ƙasar ba sakamakon rahoton da rundunar ta bayar a yau cewa sojojin Isra'ila "sun sha harbin" inda Unifil ke zaune cikin awa 24 da suka wuce.

  6. Kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada dakatar da kasafin kuɗin da Gwamnan Rivers Fubara ya yi

    Gwamna Fubara

    Asalin hoton, Rivers State Government

    Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun tarayya da ya ba da umarnin dakatar da kasafin kuɗin da Majalisar Dokokin jihar Rivers ta amince da shi ƙarƙashin jagorancin Edison Ehie.

    Kotun ta kori ƙarar ce wadda Gwamna Siminalayi Fubara ya ɗaukaka bayan 'yanmajalisar jihar biyar da ke biyayya gare shi sun amince da shi kasafin na naira biliyan 800.

    Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda rashin cancanta.

    Ta ƙara da cewa gwamnan ya janye bayanan da ya gabatar wa kotun ƙasa game da lamarin, a saboda haka ba zai yiwu ya ɗaukaka ƙara ba kan batun da bai ƙalubalance shi ba tun da farko.

    Rikici tsaknin Gwamna Fubara da tsohon maigidansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, na ci gaba da ruruwa, inda a makon da ya gabata ma gwamnan ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi da ke yi masa biyayya bayan sun ci zaɓe a jam'iyyar APP.

    Hakan ta faru ne bayan sun fice daga jam'iyyarsu ta PDP mai mulkin jihar, yayin da ake kokawar gwada iko tsakaninsa da Wike, wanda Fubara ya gada a mulkin jihar.

  7. Harin Isra'ila ya jikkata dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon

    UNIFIL

    Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Labanon sun ce wata tankar yaƙi ta Isra'ila ta yi luguden wuta kan sansaninsu ​​da ke kudancin kasar.

    Rundunar UNIFIL ta ce dakarunta biyu sun ji raunuka lokacin da tankar ta bude musu wuta a kan hasumiyar da suke aikin tsaro a Naqoura, lamarin da ya yi sanadin fadowarsu.

    Tun da farko jami'an kasar Lebanon sun ce wani harin da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe ma'aikatan lafiya biyar a kudancin kasar.

  8. Atiku ya caccaki Tinubu kan ƙarin farashin man fetur

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan abin da ya kira gazawarsa wajen tafiyar da sha'anin makamashi.

    Atiku Abubakar wanda ya yi takara da Tinubu a zaɓen 2023, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis cewa gwamnatin Tinubu ta lalata al'amura da sunan cire tallafin mai.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya danganta matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta da irin tsarin gwamnatin Tinubu na "ta ci barkatai" kan yadda take tafiyar da sha'anin makamashi.

    Atiku ya kuma bayyana damuwa kan ƙamarin da hauhawar farashi ya yi a ƙasar inda ya ce al'amarin da matuƙar ƙuntata wa ƴan Najeriya.

    “Riƙon sakainar kashi da wannan gwamnatin ke yi wa tsarin cire tallafin mai shi ne babban dalilin da ya sa muke cikin yanayin ƙunci da muke ciki a ƙasar nan.

    “A yanzu haka, babu wani fata dangane da hauhawar farashin kaya wanda ya karya ƙarfin tattalin arziƙin ƴan Najeriya.

    “Abin takaici ma shi ne yadda al'amarin ba ya damun T-pain,” Kamar yadda Atiku ya rubuta.

  9. Ku tuba ko mu aika ku lahira - Matawalle ga masu ba ƴanbindiga bayanai

    Matawalle

    Asalin hoton, Zamfara Govnor Bello Matawalle/Facebook

    Ƙaramin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle ya yi gargaɗi ga masu ba ƴanbindiga bayanai da su tuba, ko kuma su aika su lahira.

    Matawalle ya yi wannan bayanin a ƙauyen Gundume da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto a lokacin da ya kai ziyarar aikin da sojojin ke yi a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Ministan ya ce, "wannan ƙauyen a da cike yake da mutane, inda ake gudanar da hada-hada sosai. Ina tabbatar muku cewa za a samu zaman lafiya. Za mu kafa sansanin soji a nan.

    "Amma kuma dole ku ji tsoron Allah. Masu ba ƴanbindiga bayanai a kan jami'an tsaro da zirga-zirgar mutane su daina. Ko dai ku daina, ko mu aika ku lahira," in ji shi.

    Tun farko kuma a ranar Laraba a wajen ƙaddamar da aikin soji na "Fansan Yamma", ministan ya yi kira da a ba jami'an tsaro haɗin kai domin samar da zaman lafiya a yankin.

  10. Harin Isra'ila ya kashe gomman mutane a Gaza

    Ma'aikatan lafiya a Gaza ta ce fiye da mutum 20 aka kashe, wasu da dama suka jikkata a wani hari da Israila ta kai ta sama kan wata makaranta da ke tsugunar da Falasɗinawa da suka rasa muhalansu a Dir- al Balah da ke tsakiyar yankin.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutane suka riƙa gudu domin taimakawa waɗanda suka ji raunuka yayinda hayaƙi da kura suke tashi.

    Shaidu sun shaida wa BBC cewa hari ne da aka kai ta sama, sau biyu a kan wasu ɗakuna biyu da ke cikin makaratar, wadda ta cika maƙil da iyalan da suka rasa muhallansu.

    A cikin wata sanarwar rundunar sojin Israila ta ce ta kai hari a cewarta a kan ƴan ta'adda da ke aiki a wata cibiyar tattara bayanai da ke yankin

  11. Mahaukaciyar guguwar Miltan ta doshi tekun Atlantika daga jihar Florida

    Hurricane Milton

    Asalin hoton, St Pete Police

    Mahaukaciyyar gugguwar Milton ta doshi tekun Atlantika bayan ta yi kaca- kaca da wurare da dama a jihar Florida ta Amurka.

    Guguwar ta afkawa gabar tekun kudancin Tampa Bay kuma ta ci gaba da tafiya da iska mai karfin gaske yayinda ta ratsa jihar ta Florida.

    An samu Rahotanin da ke cewa an samu asarar rayuka.

    A wani taron manema labarai shugaban hukumar yansanda ta Tampa Bay, Lee Bercaw, ya jinjinawa jami'an yan sanda da suka ceto iyalan da suka makale a lokacin da guggur ta afka mu su.

    Ya ce " Yan sanda fiye da 12 sun rasa muhalansu amma wannan bai hanasu zuwa aiki domin su taimaka wa wadanda guguwar Milton ta shafa ba."

    Gugguwar ta kuma raba gidaje da cibiyoyin kasuwanci fiye da miliyan uku da wutar lantarki

  12. Hukumomin Libya na ci gaba da tsare ƴan Najeriya da Nijar sama da 900 - Rahotanni

    ƳAN-CI RANI

    Asalin hoton, AFP

    Wasu rahotanni daga kasar Libiya na cewa, wani bangare na hukumomin kasar, sun kama wasu ƴan kasashen Afrirka bakin haure bakaken fata yawanci ƴan asalin kasar Jumhuriyar Nijar da Najeriya sama da 900.

    Sama da wata daya da ake rike da wadannan mutane sai dai har zuwa yanzu babu wani cikaken bayani game da inda suke.

    Tuni wasu da suka galabaita daga ciki suka fara mutuwa.

    Wani daga wadanda suka tsira a lokacin da aka kai samamen da jami'an tsaro suka kai a lokacin da suka kama ƴan Afirkar ya shaida wa BBC cewe " Ranar 6 ga watan Satumba ne jami'an tsaron suka kai samame, suka kama mutanen Nijar da Najeriya, " Nima ina cikin mutanen amman na gudu ne shiyasa ba a kama ni ba, amman sun dauki mutanen da suka kai 500 a lokacin."

    "Daga baya cikin wadanda suka kama din basu anshe amsu wayoyi ba, sune suka kira suke fadin cewa adadin mutanen da aka kama sun kai 900 kuma yawancinsu ƴan Nijar ne" cewar mutumin.

    Wasu daga cikin farar hula na Nijar din na ci gaba da kira ga hukumomin ƙasar da su sanya baki kan lamarin.

  13. An kwashe jarirai daga asibitin arewacin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, medical aid/palastenians

    An kwashe jariran da ke dakuna bada kulawa ta musamman daga asibitin Kamal Adwan dake sansanin ƴan gudun hijira Jablia na arewacin Gaza bayan da tankokin yaƙi sojojin Isra'ila suka mamaye yankin.

    Wata ƙungiyar bada agaji ga Falasdianwa mai mazauni a Birtaniya wadda ke bada tallafi ga bangaren da ke kula da jariran ce ta kwashe jariran zuwa asibitin Birnin Gaza wanda shima ƙungiyar ke tallafawa.

    Ƙungiyar ta ce "An tilasta asibitin dakatar da ayyukansa, sai dai har yanzu ɓangaren bada agajin gaggawa na ci gaba da ansar mutanen da hare-hare suka jikkata."

  14. Yaushe farashin mai zai daina hauhawa?

    ..

    A ranar Laraba ne ƴan Najeriya suka wayi gari da sabon farashin mai na naira 1,030 a gidajen man NNPCL a da ke Abuja maimakon 897, inda a Legas kuma farashin ya koma 998 daga 885.

    Duk da cewa cewa kamfanin na NNPCL bai faɗi dalilin ƙarin ba amma ana danganta shi da bayanan da suka nuna kamfanin ya zare hannunsa daga dillancin man kamfanin Ɗangote.

    Zare hannun NNPCL daga dillanci dai na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin da ake samu ko kuma biyan tallafi na naira 133.

    Tuni kuma gidajen mai na ƴankasuwa a Abuja suka ƙara farashin su ma inda yake farawa daga naira 1,040 zuwa sama.

    A sauran jihohi kuwa musamman na arewacin Najeriya farashin man ya kan kai har har zuwa kusan naira 1,300, sannan kuma har yanzu akwai dogayen layukan ababan hawa a gidajen man.

    Wannan ne dai ƙarin farashin mai na biyu a cikin wata ɗaya.

    Hakan ne ya sa ƴan Najeriya ke tambayar ko wannan farashin shi ne na ƙarshe ko kuma haka za a yi ta tafiya duk wata ana samun ƙari? Sannan kuma ko cire tallafin da NNPCL ke bayarwa zai kawo ƙarshen dohayen layukan mai a Najeriya?

    Ga amsar tambayoyinku a cigaban labarin >>>> Yaushe tsuguno zai ƙare dangane da farashin mai a Najeriya?

  15. Rafael Nadal zai yi ritaya daga wasan tennis

    Nadal

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitaccen ɗan wasan tennis, Rafael Nadal, ya sanar da cewa zai yi ritaya da wasan a ƙarshen kakar bana.

    Ɗan wasan ɗan ƙasar Spain zai yi ritaya ne a matsayin ɗaya daga cikin zaratan wasan, inda yanzu haka ya samu nasarar lashe babban kofin wasan tennis wato grand slam guda 22.

    Mai shekara 38, Nadal wanda ya fara wasan tennis a matakin ƙwararru a shekarar 2001 ya lasha gasar grand a shekarar 2005 ne, inda ya doke ɗan wasan Argentina Mariano Peurta a wasan ƙarshe na French Open.

    Ya lashe gasar ce a karon farko da ya fafata, inda ya zama ɗan wasa na biyu da ya lashe gasar a fafatawar farko.

  16. Ukraine ta nemi ƙarin tallafi daga Birtaniya

    Prime Minister Sir Keir Starmer and Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Firai ministan Birtaniya Sir Kier Starmer ya tattauna da shugaba Zelensky na Ukraine a birnin London.

    Ziyarar ta Zelensky Birtaniya wani bangane ne na rangadin da yake a Turai a kokarinsa na ƙara samun tallafi ga kasarsa.

    Shugaba Zelnsky ya ce zai gabatar da daftarin samun nasara a yaƙinsa da Rasha yayin da mista Sir Keir ya jaddada goyon bayan shi ga Ukraine.

    Tattaunawa na zuwa ne bayan da yaƙin Ukraine da Rasha ya shiga cikin shekara ta uku, kuma adaidai lokacin da ake hasashen cewa Donald Trump wanda ake kallo a matsayin wanda baya goyon bayan Ukraine sosai ka iya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka

  17. Ayyukan ɗan adam na ci gaba da kawo tarnaƙi ga rayuwar dabbobi - WWF

    Kungiyar agaji don raya halittun ubangiji ta WWF, ta yi gargadin cewa ayyukan dan Adam na ci gaba da zama wani tarnaki ga rayuwar dumbin dabbobi.

    A cikin rahotonta na baya-bayan nan, ta gano cewa yawan namun daji ya ragu da kashi uku cikin hudu a cikin shekaru hamsin da suka gabata.

    Kungiyar agajin ta ce adadin kunkuru da giwayen a Afirka da kuma nauin kifin dolphin a Brazil na raguwa cikin sauri.

    WWF na kira da a samar da ƙarin wuraren kariya ga namun daji, da kuma daukar matakan ganin sun bun kasa.

  18. Harin Isra'ila a makaranta ya kashe mutum 16

    Aƙalla mutum 16 ne suka rasu a wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a inda iyalai da dama masu neman mafaka ke zaune a garin Deir al-Balah da ke Gaza, kamar yadda jami'an lafiya suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Kafafen watsa labaran masu alaƙa da ƙungiyar Hamas sun rawaito cewa mutum 22 ne suka mutu ba 16 ba.

    Rundunar sojin Isra'ila dai ba ta ce uffan ba amma a watannin nan rundunar ta ƙaddamar da hare-hare a makarantu- da aka mayar sansani, inda suke cewa Hamas na amfani da su ne a matsayin wuraren kitsa kai hare-hare.

    kungiyar Hamas dai ta musanta cewa tana da makarantun da ma sauran gine-ginen jama'a wajen kai hare-hare.

  19. Bidiyon yadda mahaukaciyar guguwa ta yi ragaraga da manyan ginene a Amurka

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon yadda guguwar ta kwashe rufin babban filin wasan jihar

    An umarci al'umar birnin Plant City da ke gabashin Tampa da su kula da kansu saboda gagarumar ambaliyar ruwa da guguwar ta haifar.

    Magajin garin, Bill McDaniel ya ce an yi nasarar ceto mutane 35 da sanyin safiyar yau Alhamis.

    Ya ce wasu daga cikin manyan titunan yankin sun lalace ba a iya amfani da su.

    "Bai dace mutane na fita waje ba a wannan lokacin, kamata ya yi kowa ya zauna cikin gida"

    Bayanan bidiyo, Yadda babbar na'urar ɗaga abubuwa masu nauyi ta faɗo a Florida
  20. Hezbollah ta harba gomman makaman roka zuwa Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Hezbollah a ƴan sa'o'in da suka gabata tana ta harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila.

    Dakarun Isra'ila sun sun gano makamai 40 waɗanda rokoki ne da masu linzami daga aka harba daga Lebanon zuwa yankin Galilie.

    Rundunar ta ce na'urorinsu sun tare wasu daga cikin makaman amma wasu sun faɗa a yankunan.

    Ƙungiyar Hezbollah ta tabbatar da cewa ta harba rokoki a kan sojojin Isra'ila da ke Ma'ayan Baruch kibbutz da Beit Hillel waɗanda duka suke kan iyakar Lebanon.

    Ta kuma ce ta harba ƙarin rokokin zuwa Kiryat Shmona, inda hare-haren nasu na ranar Laraba ya kashe mutum biyu.