...Daga Bakin Mai Ita tare da Salisu S. Fulani
...Daga Bakin Mai Ita tare da Salisu S. Fulani
Salisu S. Fulani shahararren jarumi ne kuma mai ba da umarni a masana'antar fim ta Kannywood, kuma shi ne baƙonmu a filin ...Daga Bakin Mai Ita na wannan makon.
An haifi jarumin a unguwar Bolari da ke garin Gombe na jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ya karatun firamare a Gombe, kafin daga baya ya ƙarasa sakandare a garin Kano kuma ya samu shaidar NCE. Ya kuma yi karatun aikin jarida a Jami'ar Bayero ta Kano.
Ya faɗa wa BBC cewa kusan gadar fim ya yi saboda Hussaina Ibrahim da aka fi sani da Tsigai 'yar'uwarsa ce kuma ta dalilinta ya koma birnin Kano da zama.
Ya fara fitowa a fim mai suna Jahilci ya fi Hauka na Ibro.



