Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Haruna Kakangi

  1. Sai da safe

    Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin na ranar Alhamis.

    Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu sababbin labaran daga sassan duniya.

    Umar Mikail da Usman Minjibir ne ke muku fatan alheri.

  2. Ni ma na sha yin zanga-zanga amma ta lumana - Bola Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce shi ma ya sha shiga zanga-zanga a lokacin mulkin soja "amma ba tare da tashin hankali ba".

    Shugaban na magana ne yayin da gwamnatinsa ke ta roƙon masu shirya zanga-zanga game da tsadar rayuwa da su ƙara mata lokaci don maganace matsalolinsu cikin ruwan sanyi.

    "A lokacin mulkin soja, mun yi adawa da 'yan kama-karya, kuma ina cikin mutanen da suka dinga zanga-zangar lumana ba tare da ƙone-ƙone ba," a cewar shugaban lokacin da yake karɓar baƙuncin Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Jr. a yammacin yau.

    Ya ci gaba da cewa "mun yi bakin ƙoƙarinmu wajen tabbatuwar shekara 25 ta mulkin dimokuraɗiyya a jere kuma zan yi cigaba da rainon wannan dimokuraɗiyyar", kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.

    Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasar, DSS, ta yi gargaɗi dangane da shirin zanga-zangar tana mai cewa "burinsu shi ne kifar da gwamnati".

  3. Majalisar dattawa za ta binciki zargin yi wa man fetur ɗin Najeriya zagon ƙasa

    Sanatocin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bayyana aniyarta ta gayyatar babban bankin ƙasar da sauran jiga-jigan da ke kula da harkokin man fetur game da zargin yi wa ɓangaren man zagon ƙasa.

    Shugaban kwamatin wucin-gadi kan zargin lalata harkokin mai kuma shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele, ya ce kwamatin nasa zai binciki biliyoyin dala da aka kashe wajen gyaran matatun mai na ƙasar.

    An tsara gudanar da zaman jin ra'ayin jama'a ranar 10 ga watan Satumba, inda 'yankwangilar da ke aikin gyaran matatun za su hallara domin amsa tambayoyi.

    Kazalika, kwamatin mai mambobi 14 zai ziyarci jihohin Legas da Rivers da kuma Bayelsa domin ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin man fetur.

    A jawaban da suka gabatar, 'yan kwamatin sun ci alwashin yin aiki ba sani ba sabo domin daƙile matsalolin da ke addabar sashen shekara da shekaru.

  4. Babu wurin zanga-zanga a Abuja - Wike

    Nyesom Wike

    Asalin hoton, FCTA

    Ministan Babbanbirnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zangza-zangar da ake shirin yi wa gwamnati mai ci ranar 1 ga watan Agustan 2024, ta dace da ranar da zai karrama sarakunan gargajiyar babban birnin.

    Wike ya bayyana hakan ne ranar Alhmis lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar tsaro na babban birnin.

    “Ga waɗanda suke son yin zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta, ba su da wurin gudanar da ita a babban birnin tarayya. Ranar ta dace da ranar da shugabannin ƙananan hukumomin birnin tarayyar suke bikin karrama sarakunan gargajiyarsu.

    “Saboda haka ba za mu bar ranar da gabaɗayan Abuja za su karrama sarakunansu. To a hakan kuma wani ya ce zai hana faruwar wannan biki." In ji Wike.

  5. Gwamnatin Sudan ta musanta batun yunwa a ƙasar

    Ministan noma na Sudan ya yi watsi da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi na cewa yunwa na kunno kai sakamakon yakin basasar da ake yi a kasar.

    Abubakr al-Bushra ya nuna shakku kan bayanan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ke nuna cewa sama da mutum 700,000 ne ke fama da matsananciyar yunwa.

    Ya kara da cewa wannan ba wani babban kaso ba ne a yawan al'ummar kasar. Ya kuma ce gwamnatin sojan Sudan ba za ta amince da matsin lamba daga kasashen duniya na bude mashigar kan iyaka domin shigar da kayan agaji yankunan da ke karkashin ikon dakarun RSF ba.

    A watan da ya gabata wani bincike na MDD ya nuna cewa rabin al'ummar Sudan miliyan 50 na fama da matsananciyar yunwa, kuma yankuna 14 na fuskantar barazanar fari.

  6. Inec a shirye take ta jagoranci zaɓuka a ƙananan hukumomi idan aka ba ta dama - Mahmood Yakubu

    Mahmood Yakubu

    Asalin hoton, Inec

    Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya ya ce a shirye suke su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar idan aka ba ta damar yin hakan, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

    Kalaman na Farfesa Mahmood Yakubu na zuwa ne 'yan makonni bayan Kotun Ƙolin Najeriya ta bai wa ƙananan hukumomin 'yancin cin gashin kansu a harkokin kuɗi, tare da umartar gwamnatin tarayya kada ta bai wa kowace ƙaramar hukuma kasonta matuƙar babu zaɓaɓɓen shugaba.

    Daga nan ne kuma wasu 'yanmajalisar tarayya suka fara yunƙurin goyon bayan dokar da za ta ƙwace alhakin gudanar da zaɓen hukumomin daga hannun gwamnatocin jiha zuwa hukumar zaɓe ta ƙasa Inec.

    Sai dai da yake magana lokacin da ya bayyana a gaban kwamatin majalisa kan harkokin zaɓe, Farfesa Yakubu ya koka kan kuɗaɗen gudanar da zaɓuka a ƙasar.

    A shekarar nan Inec za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Ondo da Edo da ke kudancin ƙasar, kuma abin da ya kai shi majalisar kenan a yau Alhamis.

  7. 'Yansanda sun sake kama masu zanga-zanga 70 a Uganda

    Uganda

    Asalin hoton, Reuters

    An kama masu zanga-zanga da dama wadanda suka halarci wani haramtaccen gangami da aka gudanar a Kampala babban birnin Uganda, inda suka yi yunƙurin yin tattaki zuwa majalisar dokokin kasar.

    Wata kungiyar bayar da agaji ta ce 'yansanda sun kama mutum 73.

    Masu zanga-zangar sun samu ƙwarin gwiwa ne daga zanga-zangar da matasa suka jagoranta a makwabciyarsu Kenya, wadda ta tilasta wa gwamnatin kasar yin watsi da kudirinta na kara kudaden haraji.

    Masu zanga-zangar a Uganda na kira ne da shugaban majalisar dokokin kasar ya yi murabus bayan Amurka da Birtaniya sun same shi da laifin cinhanci da rashawa.

  8. Manufar masu zanga-zanga ita ce "kifar da gwamnati" - DSS

    ..

    Asalin hoton, DSS

    Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ta yi gargaɗi dangane da shirin zanga-zangar matsin rayuwa a Najeriya.

    Hukumar ta DSS ta ce tuni ta riga ta gano waɗanda suka kitsa ta da masu goyon bayan zanga-zangar, inda suka gargaɗe su da su sanya kishin ƙasa su dakatar da shirin zanga-zangar.

    Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya ya aike wa manema labarai.

    Sanarwar ta ce hukumar ta DSS ta gano cewa wasu ɓatagari na shirin karkatar da akalar zanga-zanagr da manufar tayar da zaune tsaye a Najeriya.

    Dakta Afunanya ya kuma yi zargin cewa burin masu kitsa zanga-zangar shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.

    "Masu kitsa zanga-zangar na son yin amfani da haddasa hatsaniya domin shafa wa gwamnatin tarayya da na jihohi kashin kaji da ɓata musu suna domin haɗa su da talakawa. Burinsu shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya." In ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ta duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.

    Daga ƙarshe hukumar ta nemi iyaye da shugabannin gargajiya da malamai su ja hankalin mabiya da ƴaƴansu da ɗalibai da su guji shiga wannan zanga-zangar.

    Sai dai kuma duk da haka hukumar ta ce za ta yi aiki tare da sauran jami'an tsaron ƙasar wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

  9. Aƙalla 'yan cirani 41 ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwale a tekun Yemen - MDD

    ..

    Asalin hoton, ..

    Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Yemen ta ce mutum huɗu ne kacal suka tsira bayan wani jirgin ruwa ɗauke da aƙalla 'yan gudun hijira 45 ya kife a gaɓar tekun Yeman.

    Hukumar ta ce lamarin ya auku ne saboda iska mai ƙarfi da kuma nauyin mutanen da ya fi karfin jirgin.

    A watan da ya gabata akalla yan cirani 49 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da 140 suka ɓace, bayan da jirgin ruwan da suke ciki, da ya taso daga Somaliya ya nutse a gabar tekun Yemen.

    Tun daga shekarar 2014, fiye da yan cirani 1,800 ne suka mutu ko kuma suka ɓace yayin da suke ƙoƙarin ƙetarawa daga gabashin Afirka zuwa ƙasashen yankin Gulf.

  10. China da Rasha sun fara atisayen jiragen yaƙi a kusa da Amurka

    Atisayen jiragen yaƙi

    Asalin hoton, RUSSIAN DEFENCE MINISTRY

    Bayanan hoto, Jiragen yaƙin China da na Rasha sun yi shawagi a kusa da sararin samaniyar jihar Alaska ta Amurka.

    Ƙasashen China da Russia sun ƙaddamar da atisayen jiragen yaƙi na haɗin gwiwa arewacin Tekun Pacific a kusa da jihar Alaska da ke Amurka.

    A baya ƙasashen biyu sun sha aiwatar da sintirin a yankin, inda Rasha ta riƙa shawagi da jirajenta masu harba boma-bomai.

    Sai dai sintirin na ranar Laraba shi ne na farko da ya haɗa jiragen yaƙin ƙasashen biyu a arewacin Tekun na Pacific.

    Ƙasashen biyu sun ce ba su da wata niyya ta amfani da sintirin don takalar wata ƙasa, yayin da hukumar kula da sararin samaniyar Amurka da Canada da yankin arewacin Amurka, NORAD ta ce ba ta ganin atisayen a matsayin wata barazana.

    To sai dai Sanatar jihar Alaska a majalisar dokokin Amurka, Lisa Murkowski ta bayyana atisayen a matsayin takalar faɗa da ba a taɓa ganin irinta ba a yankin.

    Tana mai cewa wannan ne karon farko da ƙasashen biyu ke gudanar da atisayen haɗin gwiwa a yankin.

    Ƙasar China ta ce atisayen ba shi da alaƙa da rikicin da duniya da ma yankin ke ciki

  11. Guguwar Typhoon Gaemi ta auka gaɓar tekun China

    Guguwar Typhoon Gaemi ta auka gaɓar tekun kudu maso gabashin ƙasar China, inda tuni hukumomi suka yi gargaɗin shirya fuskantar mummunan bala’i.

    Tuni dai aka kwashe fiye da mutane 150,000 daga kudancin lardin Fujian.

    Guguwar ta riga ta kashe mutane da dama tare da raunata wasu ɗaruruwa a yayin da ta ratsa yankuna a ƙasashen Philippines da Taiwan.

    Amma yanzu al’amura sun fara daidatuwa a waɗannan ƙasashen.

    A Taiwan har yanzu ba a dawo da sufurin jiragen sama ba, amma guguwar ta riga ta wuce kuma al’amura sun fara komawa yadda suke a babban birnin ƙasar.

  12. Ba mu san abin da ya sa 'yan Najeriya za su yi zanga-zanga ba - Gwamnonin APC

    .

    Asalin hoton, HOPE UZODIMMA/FACEBOOK

    Ƙungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC ta ce ba ta san dalilin da ya sa wasu 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga ba.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban ƙungiyar - wanda shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Udozinma - ya ce ''mu ba mu san dalilin da ya sa suke shirin yin zanga-zangar ba, inda mun sani za mu gayyace su don zama da su domin samun maslaha''.

    “Mu a matsayinmu na jagorori muradinmu shi ne haɗin kan ƙasar nan, muna maraba da duk wani abu da zai kawo wa ƙasarmu da al'umarmu ci gaba ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata da ke kammala karatu'', in ji shugaban gwamnonin na APC.

    Uzodinma ya ƙara da cewa rashin wayewa ne a ce za a shirya zanga-zanga a Najeriya a wannan hali da ake ciki, yana mai kira ga 'yan ƙasar da su kaurace wa yunƙurin zanga-zangar.

    Gwamnan ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya su yi wa gwamnati haƙuri, yana mai cewa gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta don magance matsin tattalin arzikin da ƙasar ke fama da shi.

  13. Sojojin Isra'ila sun gano gawarwakin Isra'ilawa biyar da ake garkuwa da su a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawarwakin 'yan ƙasarta biyar da ake garkuwa da su a Gaza, tun bayan harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    An gano gawarwakin mutanen - malamar makarantar renon yara, Maya Goren da sojoji huɗu, mai muƙamin Manjo ɗaya da masu muƙaman sajan uku - a yankin Khan Younis lokacin da sojojin na Isra'ila suka kai samame yankin.

    Sojojin na Isra'ila sun ce suna da yaƙinin cewa an kashe malamar makarantar a lokacin da take hannun waɗanda suka yi garkuwa da ita, yayin da aka kashe sojojin a yayin gumurzun da ka yi ranar 7 ga watan Oktoba, sai kuma aka tafi da gawarwakinsu.

    Da wannan sanarwar kenan har yanzu akwai Isra'ilawa 111 a hannun masu garkuwar, daga cikin mutum 251 da aka yi garkuwa da su a Isra'ila, ciki har da mutum 39 da sojoji suka ce sun mutu.

  14. Amnesty ta yi kira ga ƙasashen duniya su daina sayar wa Sudan makamai

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga ƙasashen duniya su daina sayar wa Sudan makamai bayan bincikensu ya nuna shigar da makaman cikin ƙasar ne ke ƙara rura wutar yaƙi, inda wasu ƙungiyoyi ke amfani makaman wajen cin zarafin bil-adama.

    Rahoton ƙungiyar ya ce shigar da makamai Sudan, inda aka kashe fiye da mutum 16,000 tare da raba fiye da miliyan 10 da muhallansu, na haifar da fargaba a faɗin ƙasar.

    Amnesty ta kuma zargi ƙasashen China da Serbia da saɓa wa dokokin duniya kan cinikin makamai.

    Ƙungiyar ta ce ƙasashen duniya sun kasa martaba dokar hana shigar da makamai cikin Darfur, wadda ta jima da wanzuwa.

    Kan haka ne muke buƙatar faɗaɗa dokar zuwa ƙasar Sudan baki-ɗaya domin daƙile yaɗuwar makamai a ƙasar.

    Haka kuma ƙungiyar ta yi nazarin alƙaluman shirajen ruwan da ke shigar da kayyaki ƙasar, inda ta ce bincikenta ya gano cewa ana shigar makamai da harsasai masu yawa cikin ƙasar daga ƙasashen China da Rasha da Serbia da Turkiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Yemen.

  15. Olympics: 'Yan matan Najeriya za su kara da na Brazil

    ..

    Asalin hoton, NFF

    A yau Alhamis ne ƙungiyar Super Falcons ta 'yan ƙwallon matan Najeriya za su kara da takwarorinsu na Brazil a gasar Olympics.

    Za a take wasan ne da misalin ƙarfe 6 na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Stade de Bordeaux da ke Faransa.

    Karawar za ta zama ɗaya daga cikin manyan karawa da za su ja hankali a gasar, yayin da ake yi wa tawagar Brazil kallon ɗaya daga cikin wadanda za su iya lashe gasar.

    Sifaniya da Japan ne sauran ƙasashen biyu da ke cikin rukunin C, waɗanda za su fara kece raini da misalin ƙarfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.

  16. Adadin mutanen da suka mutu a zaftarewar ƙasa ya kai 257 a Ethiopia

    Alƙaluman baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a zabtarewar ƙasa a gundumar Gofa na kudancin Ethiopia ya kai 257.

    Majalisar ta ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa zuwa 500.

    Fiye da mutum 15,000 na waɗanda zabtarewar ta shafa na buƙatar sauya musu muhalli, a yayin da suke ci gaba da fama da matsalolin da annobar ta haifar a ranakun Lahadi da Litinin.

    A yau Alhamis ne ake ci gaba ƙoƙarin gano mutanen da ƙasar ta rufe musu.

  17. Ba za mu bari masu zanga-zanga su wargaza ƙasarmu ba - Sojojin Najeriya

    Defence Chief

    Asalin hoton, Defence HQ

    Bayanan hoto, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, CG Musa

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi masu shirin shirya zanga-zanga tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da su guji jefa ƙasar cikin ruɗani.

    Cikin wata sanarwa daraktan yaɗa labaran ma'aikatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar ya ce duk da cewa 'yan ƙasar na da 'yancin gudanar da zanga-zangar, rundunar tsaron ƙasar ba za ta lamunci tayar da fitina a ƙasar ba.

    Ya ce rundunar ta fahimci masu shirya zanga-zangar na yunƙurin kwaikwayar abin da ya faru a Kenya, inda zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

    ''Kodayake 'yan Najeriya na da 'yancin bayyana abin da ke damunsu, sojoji ba za su lamunci duk wani abu da zai iya janyo tashin hankali a ƙasar nan da sunan zanga-zanga ba'', in ji sanarwar.

    Ya ƙara da cewa, sojojin sun bankaɗo shirin wasu 'ɓata-gari' da ke ƙoƙarin amfani da zanga-zangar wajen farmakar 'yan ƙasar da ba su ji ba su gani ba.

    “Yayin da 'yan ƙasa ke da 'yancin gudanar da zanga-zangar lumana, ba su da hujjar shirya wani abu da ka iya tayar da tarzoma ko aikata laifuka'', in ji Manjo Janar Buba.

    “Mun dai ga abin da ya faru a Kenya, inda wasu ɓata-gari suka mayar da zanga-zangar lumana zuwa tashin hankali, wanda kuma aka kasa magancewa'', in ji shi.

    Ya ce sojojin ƙasar sun sha zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashe makwabta musamman ƙarƙashin shirin samar da tsaro na yammacin Afirka, ECOMOG, kuma sun san yadda al'umomin ƙasashen ke faɗawa cikin mawuyacin hali sakamakon tashe-tashen hankulan, don haka ba su so hakan ta faru a Najeriya ba.

  18. Hotunan ɓarnar ambaliyar ruwa a birnin Manila

    Mazauna ƙasar Philippines na kokawa da ambaliyar ruwa da ta afka wa babban birnin kasar, Manila.

    Ga wasu hotunan da ke nuna ɓarnar da ambaliyar ta yi wa gidajen mazauna yankin.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  19. An gano gawar ma'aikacin jirgin dakon man Philippine da ya nutse

    Masu ceto a Philiphines sun gano gawar ragowar ma'aikacin da ba a gani ba bayan nutsewar jirgin dakon mai.

    Tun da farko ma'aikatan sun ceto ma'aikatan jirgin 16 daga cikin 17.

    Jirgin dakon man, ɗauke da litar mai kusan miliyan ɗaya da rabi ya nutse ne a ƙasar Philippines.

    Kawo yanzu ba a san dalilin nutsewar jirgin ba.

    .
  20. Mutum uku sun mutu bayan rushewar gini a Legas

    gini

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum uku a lokacin da wani gini ya rufta a rukunin gidajen Arowojobe da ke yankin Maryland a jihar.

    Da yake tabbatar wa kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, rushewar ginin, Babban sakataren hukumar, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Alhamis.

    Ya ce mutane ukun da suka mutu a lokacin faruwar lamarin duka ma'aikatan gini ne.

    “Bayan samun labarin faruwar lamarin, jami'an hukumarmu sun gazaya wurin tare da gaggauta fara aikin ceto, inda suka zaƙulo gawarwakin mutum uku duka maza, da wasu mazan biyu da aka zaƙulo da ransu sai kuma wani mutum guda da ya maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin da shi ma aka ceto shi'', in ji shi.

    Ya kuma ƙara da cewa tuni aka garzaya da mutanen da aka ceto zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

    Tuni aka kai manyan motocin tono domin faɗaɗa aikin ceton.

    Rushewar gini wata matsala ce da ake yawan samu Najeriya. Ko a farkon wannan wata ma, an samu ruftawar ginin wata makaranta a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yara fiye da 20, tare da raunata gommai.