Kotun MDD ta ce ƙasashe na iya kai juna ƙara kan sauyin yanayi

Asalin hoton, Getty Images
Wani muhimmin hukunci da wata babbar kotu ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke, ya share fagen shigar da ƙarar da ƙasashe za su iya yi kan juna bisa batutuwan da suka shafi sauyin yanayi.
Sai dai mai shari'a a kotun duniyar da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands a ranar Larabar da ta gabata ya ce sanin wanda ya haddasa wani ɓangare na sauyin yanayi zai iya zama da wahala.
Ana yi wa hukuncin kallon nasara ce ga ƙasashen da ke fama da matsalar sauyin yanayi, waɗanda suka zo kotu bayan da suka ji takaicin rashin samun ci gaba a duniya wajen tunkarar matsalar.
Waɗansu ɗaliban shari'a ne daga kasashen Pacific masu ƙaranmin ƙarfi ne suka shigar da karar da ba a taba ganin irin ta ba a kotun duniyar (ICJ) a shekarar 2019.
Ana yi wa ICJ kallon kotun ƙoli a duniya kuma tana da hurumin yanke hukunci kan al'amuran da suka shafi bangarori daban-daban na duniya. Lauyoyi sun shaida wa BBC cewa za a iya amfani da hukuncin nan da mako mai zuwa.


















