Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ci alwashi ci gaba da tabbatar da ƴanci addini ga dukkanin al'umar ƙasar, inda ya ce ba kamata wani ɗan ƙasar ya fuskanci matsala ba saboda addininsa ko ƙabilarsa.
Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na bikin kirsimeti a ya aike wa ƴan Najeriya, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin kare martabar addini da tsaron ƴan ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi fatan alheri ga kiristoci da sauran ƴan ƙasar, sannan ya ce "bayan bikin, ina sake tunatar da kiristoci cewa su yi koyi da halayen ƙwarai na Yesu da ma yin amfani da saƙonsa na zaman lafiya."
Ya ce tun bayan ɗarewarsa karagar mulki yake ta ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar, "ta hanyar tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya. Duk ƴan Najeriya suna da ƴancin rayuwa da gudanar da ibadarsa da kuma neman abin da suke so."
Tinubu ya ce babu wani ɗan ƙasar da ya cancanci fuskantar ƙalubale ko barazana saboda addininsa ko ƙabilarsa, "saboda dukkan addinai suna bayyana muhimmancin son Allah da mutunta ɗan'adam. Don haka waɗannan abubuwan da suka haɗa mu ɗin ne ya kamata mu ci gaba da ɗabbaƙawa sama da abubuwan da suka raba mu domin cigaban ƙasarmu."
Ya ce ya samu damar tattaunawa da jagororin manyan addinai na ƙasar, "tun bayan da aka fara batun muzgunawa wani ɓangare da kuma batun matsalar tsaro, kuma za mu ci gaba da tattaunawa tare da samar da haɗin kai domin daƙile barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya."