Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wasu jerin matakai da gwamnatinsa za ta ɗauka domin kawo
sassauci ga al’ummar jihar sanadiyyar matsin rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar.
Matsin
rayuwar da al’ummar Najeriya ke ciki dai ya janyo zanga-zanga a wasu jihohin
ƙasar, ciki har da Kano da Oyo da kuma Osun.
Ana ɗora
alhakin tsadar rayuwar da mutane ke fuskanta ne a kan matakan da gwamnatin
tarayyar ƙasar ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta
tantance farashin dalar Amurka.
Lamarin
ya haifar da tashin gwauron-zabi na farashin kayan abinci da na masarufi da
kuma rashin albarkar kuɗin da ke hannun al’umma.
Sanadiyyar
hakan ne gwamnan jihar Legas a ranar Alhamis ya gabatar da jawabi ga al’ummar
jihar tare da sanar da ɗaukan wasu matakai, waɗanda ya ce za su
taimaka wajen rage ƙuncin rayuwa da al’umma ke fuskanta.
Wasu daga cikin
matakan su ne:
Rage ranakun aikin
gwamnati zuwa uku a mako
Gwamnan Sanwo-Olu ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnati
daga mataki na 1 har zuwa na 14 za su fara zuwa aiki kwana uku a mako.
Ma’aikata daga mataki na 15 zuwa 17 kuma za su riƙa
zuwa aiki sau huɗu a mako.
To
sai dai matakin bai shafi malaman makaranta ba, inda ya ce su, za su ci gaba da
zuwa aiki na tsawon kawa biyar a mako.
Gwamnan Sanwo-Olu ya
ce gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ƙara wa malaman makarantar
tallafin sufuri.
Ciyar da mutum 1000 a
kowace rana
Gwamnan ya kuma bayyana aniyar gwamnatin ta ciyar da mutanen da ke rayuwa a jihar aƙalla 1000 a kowace rana.
Ya ce “Za
mu zabi masu sayar da abinci (Mama Put) domin samun damar ciyar da aƙalla mutum
1000 a kowace rana a ƙananan hukumomi 20 na jihar tsawon kwana 30 zuwa 60.”
Samar da kasuwannin sayar da abinci cikin rahusa
Gwamnan ya ce
gwamnatin Legas za ta samar da kasuwannin sayar da abinci waɗanda ake yi wa
laƙabi da ‘Sunday Markets.’
A cewar sa: “Za mu buɗe
kasuwanni Lahadi a manyan kasuwanni 42 da aka zaɓo a faɗin jihar.
A irin waɗannan kasuwa
za ku iya sayen abinci cikin farashi mai rangwame.”
Ya ƙara da cewa “za a iya sayen kayan abinci waɗanda ba su zarce na naira 25,000 ba ne kawai.”
Gwaman ya ce a yanzu
kuma gwamnati za ta ɗauki nauyin mata masu haihuwa a asibitocin jihar.
Ya ce za a gudanar da
hakan ne a asibitocin gwamnati.
Haihuwa kyautar za ta
haɗa har da waɗanda za a yi wa tiyata a lokacin haihuwa.
Haka nan gwamnati za
ta yi rangwame a kan farashin wasu magunguna a asibitocin gwamnatin jihar.
Sanwo-Olu ya kuma
sanar da yin ragowa kan farashin sufuri na kashi 25%.
Rangwamen, wanda zai
fara aiki a ƙarshen makon nan zai shafi masu sufuri ne ta motocin safa da jiragen
ƙasa da na ruwa na gwamnati.
Haka nan gwamnan ya ce
gwamnati na tattaunawa da ƙungiyoyin sufuri domin shawo kansu su rage nasu
farashin.
Gwanman dai ya ce
gwamnati na sane da halin ƙunci da da al’umma ke ciki kuma ba ta manta da su.
- Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
- Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya