Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Haruna Kakangi
An samu hatsaniya a majalisar dokokin jihar Zamfara
Asalin hoton, Zamfara State Gov.
A Najeriya, yauwasu 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun harzuka, game da abin da suka kira 'gazawar gwamnatin jihar wajen magance matsalar tsaro da ta addabi sassan jihar'.
Har ma sun ayyana rufe majalisar dokokin, sai al'amuran tsaro sun inganta a jihar.
Sai dai kuma wani bangare na 'yan majalisar dokokin jihar ya musanta wannan batu, yana mai cewa gwamnan jihar yana yin iya bakin kokarinsa ta fuskar tsaron, kuma majalisar na nan bude.
Da alamu dai an fara zama irin na ’yan marina a majalisar dokokin jihar Zamfara, har wani bangare na 'yan majalisar ya bayar da sanarwar rufe majalisar, harsai yadda hali yayi.
Ga rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
‘Yan sanda sun wargaza gungun masu fasa ƙwauri a Jamus
Asalin hoton, Europol
'Yan sanda a Jamus sun
ce sun "ruguza" daya daga cikin gungun masu fasa kwabri da ke aiki a
ƙasashen Turai.
An kama mutane
19 a Jamus bayan wani bincike da 'yan sandan Jamus da Faransa da Belgium suka
yi na tsawon shekara guda.
An gano ƙananan
kwale-kwale masu yawa da rigunan kariya a yayin samamen a da aka kai wurare 28.
Rundunar ‘yan sandan
Europol ta ce gungun masu fasa kwaurin na iya aikawa da jiragen ruwa takwas
zuwa Burtaniya a kowace rana.
Daga cikin wadanda aka kama har da shugbannin
gugun guda biyar,waɗanda ake zargi da shirya miyagun ayyuka ciki har da safaran
ƴan’adam.
Europol ta ce
’yan ƙungiyar sun cusa mutane kusan 55 a cikin wani kwale-kwale da aka ƙera don
ɗaukar mutum 10 kuma sun karɓi tsakanin Yuro 1,000 ($1,082) zuwa Yuro 3,000 kan
kowanne mutum ɗaya.
'Yan kungiyar
sun haɗa da 'yan asalin ƙasashen Iraki da Siriya kuma Kurdawa in ji masu
binciken a ranar Alhamis.
Cutar zazzabin Lassa ta bulla asibitin sojoji na Kaduna
Asalin hoton, ..
Gwamnan jihar Uba Sani ya bayar da umarni ga ma'aikatar lafiyar jihar ta gudanar da bincike a asibitin sojoji da ke jihar sakamakon labarin bullar cutar zazzabin Lassa.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Muhammad Lawal Shehu, ya fitar ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin bullar cutar zazzabin Lassa a asibitin sojoji na '44 Nigerian Army Reference Hospital' da ke birnin Kaduna.
Sanarwar ta ce kawo yanzu cutar ta kashe mutum hudu a cikin harabar asibitin, yayin da aka samu mutum uku da ke nuna alamun kamuwa da cutar.
Tuni dai jami'an lafiyar jihar da hadin gwiwar hukumomin asibitin suka dauki matakai domin dakile bazuwar cutar.
An dai dauki samfurin jinin mutanen da ake tunanin sun kamu da cutar domin aika wa hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasar don gudanar da bincike.
Alamomin cutar sun hada da zazzabi da gajiya, da ciwon kai da ciwon makogoro da ciwon tsoka da ciwon kirji da amai da gudawa da tari da kuma ciwon ciki.
Ƙungiyar ƴan arewa na son Tinubu ya dawo da tallafin man fetur
Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK
Wata Ƙungiyar arewa da ke sanya idanu kan harkokin tattalin arziƙi (Arewa Economic Forum), ta yi
tsokaci kan halin da tattlin arzikin ƙasar ke ciki, inda ta yi kira ga
shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake nazari kan manufar cire tallafin
man fetur da kuma dakatar da raba kuɗaɗen da ake yi wa gwamnonin jihohi.
Shugaban ƙungiyar,
Alhaji Shehu Ibrahim Dandakata, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar
Alhamis a Abuja, ya ce rashin bin diddigi da kuma rashin mai da hankali kan
muhimman abubuwa da gwamnoni ke yi shi ya sa talauci da yunwa suka yi ƙamari a ƙasar.
A madadin sake dawo da biyan tallafin man fetur,
ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa da ya nemo hanyoyn da za a tabbatar da
cewa gwamnonin jihohi sun yi amfani da rarar kuɗaɗen da ake kasafta musu ta
hanyoyin da suka dace domin kuɗaɗen su yi tasiri kan al’umma.
Dandakata ya
kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta duba halin da darajar kuɗin ƙasar ke ciki,
ta kuma binciki dalilin da ya sa farashin dala ke tashi bayan duk wani taron
kwamitin raba arzikin ƙasa (FAAC).
'Yan kasuwar chanji da ke Abuja sun ce sun rufe kasuwar musayar kudin kasar waje da ke babban birnin kasar Abuja.
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Abdullahi Abubakar Dauran ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne sakamakon yadda gwamnati ta bukaci hakan daga garesu.
A baya-bayan nan dai jami'an tsaron kasar sun yi ta kai samame kasuwar a wani yunkuri na dakile tashin farashin dala a kasar.
Shugaban 'yan kasuwar ya ce a bangarensu sun yi biyayya ga umarnin gwamnati, domin yana da yakinin cewa gwamnatin ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Babban hafsan sojin Najeriya ya gargaɗi masu neman a yi juyin mulki
Asalin hoton, X/Defence HQ Nigeria
Bayanan hoto, Babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa, inda ya ce haƙuri abu ne mai muhimmanci a mulkin dimokuraɗiyya.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da yake ganawa da ƴan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine.
Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina.
An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi.
Najeriya na fama da hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga.
Bugu da ƙari darajar takardar kuɗin naira na ci gaba da zubewa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wadda ke da matuƙar tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi na ƙasar.
Ana dai ɗora alhakin wahalhalun da al'ummar ta Najeriyar ke fuskanta kan matakin shugaban ƙasar, Bola Tinubu na cire tallafin man fetur a ranar da ya karɓi mulki.
Wannan dai ba sh ne karo na farko ba da sojojin Najeriya ke gargadin 'yan kasar da ke kiraye-kirayen juyin mulki a kasar.
Sojojin Najeriya sun kashe kasurgumin dan fashi a Kaduna
Asalin hoton, KDSG
Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe wani ɗan
bindiga da aka fi sani da Boderi Isyaku.
Rahotanni sun ce
an kashe shugaban ‘yan bindigar ne da wasu mayakan sa a wani artabu da dakarun
sojojin Nijeriya, a yankin Bada/Riyawa da ke ƙananan hukumomin Chikun da Igabi
na jihar Kaduna.
Boderi ya shafe
kusan shekara goma yana gudanar da munnan ayyuka yankunan a jihohin Kaduna da
Neja, ta hanyar kai hare-hare, da kuma garkuwa da mutane.
An alaƙata shi
da kai hare-hare da dama a yankunan da suka haɗa da Sabon Birni da Rigasa da Buruku
da Rijana da Kateri da hanyar Kaduna
zuwa Abuja da kuma hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
An kuma zarge
shi da ƙulla alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, tare da haɗa kai da su wajen kafa
sansanoni a waɗannan yankunan.
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta kayade farashin kudin shinkafa a kasuwanin kasar.
Gwamantin tace bayan dogon bincike da ta gudanar tsakanin masu ruwa da tsaki ta tsayar da farashin duba da yadda ba inda ake sayar da shinkafa sama da CFA Jika 13.
Cikin wata sanarwa da ministan harkokin kasuwanci na kasar ya sanya wa hannu, ya gwamnatin kasar ta dauki matakin karyar da farashin shinkafar da ake shigar da ita cikin kasar.
Sanarwar ta kuma kayyade sabon farashin da za a rika sayar da shinkafar a fadin kasar, daga jaka 16 da rabi ko 17, zuwa jaka 13 da rabi ko 14 a wasu jihohin kasar.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne bayan tuntubar 'yan kasuwa da masu saye da sauran masu zirga-zirgar sufurin da sauran masu ruwa da tsaki.
Ga cikakken rahoton daga Tchima Illa Issoufou.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Kalli yadda wasu tagwaye ke rayuwa a manne da juna
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Tun farko masana sun bayyana cewa yaran ba za su wuce tsawon ƴan kwanaki ba bayan haihuwar su, to amma a cikin kwanakin nan ne tagwayen suka yi bikin cika shekara bakwai a duniya.
Ana tunanin cewa su ne kaɗai tagwayen da ke girma a manne da juna a faɗin nahiyar Turai.
Gwamnatin Benue ta bai wa baƙin makiyaya wa'adin mako biyu su fice daga jihar
Gwamnatin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta bai wa Fulani makiyaya da ta ce baki ne da ke kwarara cikin jihar da kuma ake zargin na dauke da makamai wa’adin makonni biyu su fice a jihar ko su fuskanci fushin hukuma.
Gwamnan jihar Hyacinth Alia ya kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da bin umurnin, sannan ya jaddada cewa har yanzu dokar nan da ta haramta kiwon dabbobi a sarari na ci gaba aiki.
To sai dai kungiyar Miyetti Allah reshen jihar ta nesanta kanta da ‘ya’yanta da yin kowane hadin gwiwa da dukan wasu bata garin makiya a cikin jihar.
Ga rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
Majalisar dattawa Najeriya ta amince kafa kwamitin kudi na CBN
Asalin hoton, CBN
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin mutane 12 karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Cardoso,a matsayin mambobin kwamitin da za su kula da harkokin kudi a babban bankin Kasar CBN.
Wannan tabbacin ya zo ne bayan wani rahoton kwamitin kula da harkokin banki da inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na babban bankin ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Alhamis.
Tabbatar da sabbin mambobin MPC ɗin na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin taron tsare-tsaren babban bankin na farko karkashin sabon gwamnan bankin.
An tsara taron ne a ranakun 26 da 27 ga Fabrairu, 2024.
Membobin su ne:
1. Olayemi Cardoso – Shugaba
2. Muhammad Sani Abdullahi – Mamba
3. Bala M. Bello – Mamba
4. Emem Usoro – Mamba
5. Philip Ikeazor - Mamba
6. Lamido Yuguda - Mamba
7.Jafiya Lydia Shehu – Mamba
8. Murtala Sabo Sagagi – Mamba
9. Aloysius Uche Ordu – Mamba
10. Aku Pauline Odinkemelu – Mamba
11. Mustapha Akinwumi – Mamba
12. Bandele A.G. Amoo – Mamba
A watan Nuwambar 2023, Cardoso, wanda shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin gwamnan CBN a watan Satumba na 2023, ya ce taron na MPC bai yi tasiri ba a karkashin magabacinsa Godwin Emefiele.
Wasu jihohin Indiya sun haramta sayar da alewar yara
Asalin hoton, Getty Images
Wasu jihohi a Indiya sun fara haramta sayar da alewar yara ta "Sweet Camfo."
A satin daya gabata ne Jihar Tamil Nadu dake Kudancin ƙasar ta saka dokar hana sayar da alawar bayan tabbatar da samun sinadarin da ke haddasa cutar cancer na Rhodamine-B a ciki yayin gwaji.
Farkon watan nan ne wata ƙungiya a yankin Puducherry ta haramta alewar yayin da da wasu jihohin suka fara gwajin samfuranta.
Alewar ta 'Sweet Camfo' da ake kira da buddi-ka-baal a Indiyance wanda ke nufin gashin tsohuwa sananniya ce tsakanin yara a duk faɗin duniya.
Ana samunta a wajen wasan yara da sauran wuraren bukukuwa da yara kan halarta.
Alewar na da farin jini tsakanin yara saboda yadda take kamar auduga sannan take narkewa da sauri a baki.
Amma wasu hukumomi a Indiya sun ce haɗarinta ya fi yanda ake tsammani.
A satin daya gabata jami'an jamai'a Hukumar Kula da Tsaftar Abin ta kasar suka kai wa masu sayar da alewar samame a bakin teku da ke birnin.
Bincike ya nuna cewa sinadarin na Rhodamine-B da ake samu a alewar na ƙara haɗarin kamuwa da cutar cancer sannan ƙasar Birtaniya da California sun haramta amfani da shi wajen busar da abinci
Shin samamen jami’an tsaro a kasuwannin canji zai farfaɗo da darajar naira?
Karen shugaban Amurka ya ciji jami'an tsaro har sau 24
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Amurka Joe Biden tare da karensa mai suna Kwamanda
Kwamanda, wato karen Shugaban Amurka, Joe Biden ya ciji jami’an Hukumar tattara bayanan sirri na Amurka akalla sau 24, kamar yadda sabbin takardu suka nuna.
Bayanan sirrin Amurka sun nuna yadda karen - wanda daga Jamus aka samo shi - ya haifar da fargaba tsakanin masu tsaron fadar shugaban kasar.
Lamarin da ya haifar da sauye-sauyen dabarun tsaron fadar shugaban kasar.
Wani babban jami'in ya lura cewa cizon ya haifar da gyare-gyare a cikin dabaru, tare da shawarwari.
Lamarin ya faru ne tsakanin Oktoban 2022 da Yuli 2023, wanda ya yi sanadin jikkatar jami'in tsaron a sassan jikinsa daban-daban.
Takardun, wadanda aka samu ta hanyar bukatu na ‘Yancin Bada Labarai, sun nuna irin munin cizon da jami'in ya samu, wanda ya sa aka tsige karen daga Fadar White House a watan Oktoban bara.
NLC ba ta tuntuɓe mu ba kafin ayyana yin zanga-zanga a fadin Najeriya - TUC
Asalin hoton, other
Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi ikirarin cewa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ba ta tuntube ta ba kafin ta kuduri aniyar gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairun 2024.
Babban sakataren kungiyar Nuhu Toro a wata wasiƙa da ya aike wa shugabannin NLC ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kungiyar kwadago karkashin jagorancin Joe Ajaero ba ta tuntuɓi ƙungiyar ‘yan kasuwa da Festus Osifo ke jagoranta ba kafin ta dauki matakin.
Kungiyoyin biyu dai sun bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 da ta aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla kan magance matsalar tattalin arziki da ke kara ta’azzara ƙasar, ko su tafi yajin aiki.
Tuni dai hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta buƙaci kungiyar ƙwadago ta NLC ta jingine yajin aikin da ta shirya yi ta kuma shiga tattaunawa a maimakon daukar matakan da za su iya tayar da zaune-tsaye, amma ƙungiyar da Ajaero ke jagoranta ta dage kan ci gaba da matakin da ta ɗauka na zuwa yajin aiki.
Yadda farashin kayan masarufi ya tashi a lokacin mulkin Tinubu
Kungiyar kwadago ta janye yajin aiki
An koma teburin tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan ƙwadago a Najeriya
Tallafin da gwamnatin Legas za ta yi don sassauta ƙuncin rayuwa
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wasu jerin matakai da gwamnatinsa za ta ɗauka domin kawo
sassauci ga al’ummar jihar sanadiyyar matsin rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar.
Matsin
rayuwar da al’ummar Najeriya ke ciki dai ya janyo zanga-zanga a wasu jihohin
ƙasar, ciki har da Kano da Oyo da kuma Osun.
Ana ɗora
alhakin tsadar rayuwar da mutane ke fuskanta ne a kan matakan da gwamnatin
tarayyar ƙasar ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta
tantance farashin dalar Amurka.
Lamarin
ya haifar da tashin gwauron-zabi na farashin kayan abinci da na masarufi da
kuma rashin albarkar kuɗin da ke hannun al’umma.
Sanadiyyar
hakan ne gwamnan jihar Legas a ranar Alhamis ya gabatar da jawabi ga al’ummar
jihar tare da sanar da ɗaukan wasu matakai, waɗanda ya ce za su
taimaka wajen rage ƙuncin rayuwa da al’umma ke fuskanta.
Wasu daga cikin
matakan su ne:
Rage ranakun aikin
gwamnati zuwa uku a mako
Gwamnan Sanwo-Olu ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnati
daga mataki na 1 har zuwa na 14 za su fara zuwa aiki kwana uku a mako.
Ma’aikata daga mataki na 15 zuwa 17 kuma za su riƙa
zuwa aiki sau huɗu a mako.
To
sai dai matakin bai shafi malaman makaranta ba, inda ya ce su, za su ci gaba da
zuwa aiki na tsawon kawa biyar a mako.
Gwamnan Sanwo-Olu ya
ce gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ƙara wa malaman makarantar
tallafin sufuri.
Ciyar da mutum 1000 a
kowace rana
Gwamnan ya kuma bayyana aniyar gwamnatin ta ciyar da mutanen da ke rayuwa a jihar aƙalla 1000 a kowace rana.
Ya ce “Za
mu zabi masu sayar da abinci (Mama Put) domin samun damar ciyar da aƙalla mutum
1000 a kowace rana a ƙananan hukumomi 20 na jihar tsawon kwana 30 zuwa 60.”
Samar da kasuwannin sayar da abinci cikin rahusa
Gwamnan ya ce
gwamnatin Legas za ta samar da kasuwannin sayar da abinci waɗanda ake yi wa
laƙabi da ‘Sunday Markets.’
A cewar sa: “Za mu buɗe
kasuwanni Lahadi a manyan kasuwanni 42 da aka zaɓo a faɗin jihar.
A irin waɗannan kasuwa
za ku iya sayen abinci cikin farashi mai rangwame.”
Ya ƙara da cewa “za a iya sayen kayan abinci waɗanda ba su zarce na naira 25,000 ba ne kawai.”
Haihuwa kyauta
Gwaman ya ce a yanzu
kuma gwamnati za ta ɗauki nauyin mata masu haihuwa a asibitocin jihar.
Ya ce za a gudanar da
hakan ne a asibitocin gwamnati.
Haihuwa kyautar za ta
haɗa har da waɗanda za a yi wa tiyata a lokacin haihuwa.
Haka nan gwamnati za
ta yi rangwame a kan farashin wasu magunguna a asibitocin gwamnatin jihar.
Rage farashin sufuri
Sanwo-Olu ya kuma
sanar da yin ragowa kan farashin sufuri na kashi 25%.
Rangwamen, wanda zai
fara aiki a ƙarshen makon nan zai shafi masu sufuri ne ta motocin safa da jiragen
ƙasa da na ruwa na gwamnati.
Haka nan gwamnan ya ce
gwamnati na tattaunawa da ƙungiyoyin sufuri domin shawo kansu su rage nasu
farashin.
Gwanman dai ya ce
gwamnati na sane da halin ƙunci da da al’umma ke ciki kuma ba ta manta da su.
Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
'Za a bayyana sabon shirin kawo ƙarshen yaƙi a Sudan'
Asalin hoton, AFP
Mataimakin shugaban kasar Sudan Malik Agar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da wani sabon shiri na kawo karshen yakin kasar, in ji shafin Sudan Tribune da ke birnin Paris a ranar 21 ga watan Fabrairu.
Agar wanda ke magana bayan ya gana da shugaban Uganda Yoweri Museveni a Kampala jiya, bai bayar da cikakken bayani kan shirin ba.
Jami'in na Sudan ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa "ya amince da shugaban Uganda kan "sabon shirin kawo karshen yakin Sudan, wanda za a sanar a cikin kwanaki masu zuwa,"
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da shugaban Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya sha alwashi a ranar 20 ga watan Fabrairu cewa ba za a yi wata tattaunawa da dakarun RSF ba har sai an fatattaki kungiyar.
Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji ƙasar da RSF a cikin wata na 10 a sassa da dama na ƙasar.
Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
Sojojin Mozambik sun daƙile yunƙurin ɗaukar ma'aikata 'yan tsageru
Asalin hoton, AFP
A jiya ne shugaban ƙasar Mozambique Filipe Nyusi ya sanar da cewa sojojin kasar sun dakile yunƙurin da masu tayar da ƙayar baya suka yi na daukar ma'aikata yara kanana a gundumar Chiure da ke arewacin kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai bayan wata ganawa da ya yi da manyan jami'an gwamnatin lardin Cabo Delgado.
Ya ce masu tayar da ƙayar bayan sun koma yankunan kudancin lardin Cabo Delgado ne domin daukar matasa aikinsu.
"A gaskiya, dole a yi tsammanin rikicin Ocua saboda suna son ɗaukar yara aikin ta'addanci," in ji Nyusi.
Yankin ya sami ƙaruwar ayyukan tsageru a 'yan makonnin nan, inda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka danganta shi da wani kamfen na "kashe su a duk inda kuka same su" da kungiyar IS ta kaddamar a ranar 4 ga watan Janairu.
Shugaban Somaliland ya sha alwashin aiwatar da yarjejeniya da ƙasar Habasha
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Somaliland Muse Bihi Abdi ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar aiwatar da yarjejeniyar ruwa da ta rattabawa hannu da ƙasar Habasha a ranar 1 ga watan Janairu.
A karkashin yarjejeniyar, Somaliland za ta yi hayar wani yanki mai nisan kilomita 20 a mashigin tekun Aden zuwa Habasha na tsawon shekaru 50, domin samun amincewa da ita a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Shugaban ya yi wannan tsokaci ne jiya a lokacin da yake halartar wani taron da aka gudanar a babban birnin ƙasar Somaliland, Hargeysa, sa'o'i bayan majalisar ministocin Somaliya ta amince da yarjejeniyar tsaron teku da Turkiyya.
Abdi ya buƙaci shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da ya taƙaita a cikin yankin da ke karkashin ikonsa, yana mai gargadin cewa Turkiyya da Masar "ba za su kai Somaliya ko'ina ba".
Masar dai na nuna adawa da yarjejeniyar da Somaliland ta kulla da ƙasar Habasha.
Somaliland ta kafa dokar hana fyade a karon farko
Akwai yiwuwar fari ya kashe mutum 43,000 a Somalia a bara - MDD
Gwamnati za ta ƙara yawan mutanen da za ta bai wa tallafin kuɗi
Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu /Facebook
Gwamnatin Najeriya na shirin sake fara bai wa talakawan kasar da kuma mafiya rauni miliyan 12 kuɗaɗen tallafi.
A halin yanzu, kusan mutane miliyan uku ne ke amfana da wadannan shirye-shiryen na tallafi, amma saboda tsadar rayuwa, gwamnati na sa ran karin iyalai miliyan 12 za su cancanci karɓan wadannan kudade.
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ne ya sanar da wannan shirin yayin wani taron ma’aikata a Uyo, da ke jihar Akwa-Ibom.
Ministan ya ce manufar ita ce a bayar da tallafin kuɗi ga al'ummar da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da domin magance buƙatunsu na gaggawa, ta yadda za a rage talauci.
Shawarar sanar da shugaba Tinubu kan shawarar kwamitin ɗin kafin a kammala rahoton karshe shi ne a sanar da shi abubuwan da ke faruwa.
Edun ya jaddada yin amfani da fasaha don tabbatar da biyan kuɗi mai inganci da gaskiya, da guje wa ayyukan hannu da jinkiri.
Rabon kuɗin rage raɗaɗin tallafin mai ya janyo taƙaddama a Najeriya
Yadda cire tallafin wutar lantarki a Najeriya zai shafe ku