Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Me ya kai sansanin sojin Amurka Gabas ta Tsakiya ?

    Sansanin sojin da aka kai wa hari da jirgi maras matuƙi a arewa maso yammacin Jordan ɗaya ne daga cikin sama da 10 da sojin Amurka ke aiki a cikinsu a Iraƙi da Jordan da Syria.

    A 'yan watannin nan, sansanonin - da suke da dama daga Syria zuwa yammacin Iraƙi na fuskantar hare-haren mayakan da Iran ta bai wa horo take ba su kuɗi da kayan aiki.

    Akwai kimanin sojoji 3,000 a Jordan, wata babbar ƙawar Amurka, akwai 2,500 a Iraƙi - sun je wurin ne tun lokacin da mayaƙan IS masu iƙirarin jihadi suka kai mamaya, wadanda har yanzu suna nan, kuma ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta ke yaƙarsu.

    Akwai kuma kimanin sojin Amurka 900 a Syria, suna yankin ne domin taya masu yaƙi da IS fada.

    Cikin mintina 30 Amurka ta kai wa wurare bakwai hari a Syria da Iraƙi.

    Biden ya ce ya yanke shawarar yadda zai yi da Jordan kan wannan lamari.

  2. An ɗage zaɓen shugaban ƙasar Senegal

    Shugaban Senegal Macky Sall ya ɗaga zaɓen ƙasar da aka tsara yi a wannan watan, biyo bayan koken da wasu 'yan takara suka yi na hana su tsayawa takarar.

    Shugaban ƙasar Senegal ɗin bai sanya sabon wa'adin da za a gudanar da zaɓen ba.

    Mista Sall dai ya sha nanata cewa ba shi da niyyar sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar.

    Amma babu shakka mutane da dama za su yi zargin ɗage zaɓen na da alaƙa da yunƙurin ci gaba da jagorantar ƙasar da uake son yi.

    Sall ya ce ya ɗage zaɓen ne domin rikicin siyasar da ya ɓarke kan wanene zai yi takara da kuma wanene ba zai yi ba.

    Hukumar zaɓe ta ƙasar ta haramtawa mutane da dama tsayawa takarar - ciki har da Karim Wade wanda ta ce yana da shaidar zama ɗan ƙasa biyu.

  3. Yadda dusar ƙanƙara ta yi wa Kashmir

  4. Mayakan ISWAP sun kashe 'yan sanda hudu a harin da suka kai a Borno

    Aƙalla 'yan sanda hudu ne suka rasa ransu sannan aka kwashe dimbin harsasai masu yawa a wani hari da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka kai ofishin 'yan sanda a Ƙaramar Hukumar Nganzai da ke Borno.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mayakan ISWAP sun kutsa kai ne cikin ofishin 'yan sandan tare da buɗe wuta kan jami'an da suke aiki.

    A cewar majiyar tsaro, mahairan sun ƙona wani ɓangare na ofishin 'yan sandan lokacin da abin ya faru a ranar Juma'a.

    "An samu ruɗani a garinmu a daren jiya. MMayaƙan ISWAP sun kai wa ofishin 'yan sanda hari a Gajiram. Kuma gaskiya sun fi ƙarfin jami'an da suke kan aiki."

    "Mun samu gawar 'yan sanda hudu a yashe a inda abin ya faru da safiyar yau, har yanzu ba a ga wasu 'yan sandan da suka tsere ba," in ji wani jami'in 'yan sa-kai.

    Rahotanni sun ce maharan sun bar wurin tun gabanin sojoji su isa.

  5. Harin da Isra'ila ta kai Rafah da Deir al-Balah ya kashe Falasɗinawa 18

    Harin saman da Isra'ila ta kai a biranen Rafah da Deir al-Balah ya kashe Falasdinawa 18, kamar yadda ma'aikatar lafita ta Gaza ta bayyana.

    Wannan na zuwa ne lokacin da mazauna Gaza ke cikin fargabar Isra'ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta zuwa yankunan da mutane ke tserewa domin neman mafana.

    Rafah dai na yankin KUdancin Gaza inda ta yi iyaka da Masar, kuma kimanin rabin mutanen zirin gaza da suka kai miliyan biyu da dari uku suna neman mafaka a yankin a lokaci guda, yayin da dakarun Isra'ila su kuma ke ci gaba da kai hare-harensu, wanda yanzu aka shiga wata na hudu da farawa.

    Hukumomin lafiya a Gaza sun ce wani harin da Israila ta kai wani gida ya yi sanadin mutuwar mutane 14, ciki har da yara da mata, kamar yadda kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

    Kakakin sojin Isra'ila ya ce suna kiyayen dokokin duniya domin kare fararen hula daga cutuwa.

  6. Rasha ta yi tir da hare-haren Amurka a Iraƙi da Syria

    Maimagana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta ce, ƙasarta ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka ta kai Iraƙi da Syria, kuma akwai buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya ta nazarci lamarin.

    "A bayyana yake cewa ana sane aka kai hare-haren domin rura wutar rikicin," in ji Maria. "Harin da aka kai kan mutane da wuraren Iran a Iraƙi da Syria, na nuna yadda Amurka ke neman jefa manyan ƙasashen yankin cikin rikici."

    Amurka ta ƙaddamar da hare-hare ta sama kan Iraƙi da Syria a wurare sama da 85 da ke da alaka da dakarun juyin juya halin Iran da masu goya musu baya, inda ta kashe sama da mutum 40, a wani mataki na ramuwar harin da aka kai wa dakarunta a yankin.

  7. Syria ta zargi Amurka da iza wutar rikici a Gabas ta Tsakiya

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Syria ta yi Allah-wadai da harin da Amurka ta kai da daren jiya a Iraƙi da Syria.

    Cikin wata sanarwa da aka wallafa a kamfanin dillancin labarai na ƙasar SANA, ta ce harin da Amurka ta kai ya sake tabbatar da abin da ake zargi na cewa, dakarunta na barazana ga zaman lafiyar duniya, kuma ita take iza wutar rikicin da yake faruwa a yakin Gabas ta Tsakiya."

    Gwamnatin Syria dai na adawa da kasancewar Amurka a cikinta kuma tana ɗaukar hakan a matsayin mamaya.

    A bara ne Syria ta koma cikin ƙungiyar ƙasahen Larabawa, bayan sama da shekara 10 da aka koreta daga ƙungiyar saboda muguntar da ta nuna kan masu rajin dimokraɗiyya lokacin da suke zanga-zanga, wani abu da ya tayar da rikicin basasa.

    Amurka da Burtaniya da wasu sauran ƙasashen yamma sun soki komawar Syria cikin ƙungiyar, kuma a bayan nan sun jaddada cewa ba za su dawo hulɗar diflomasiyya ba da shugaban Syrian Shugaba Bashar al-Assad.

  8. An kai hari tashar jirgin ƙasa a Faransa

    Aƙalla mutum uku sun jikkata sakamakon wani harin wuƙa da aka kai tashar jirgin ƙasa a birnin Paris na ƙasar Faransa.

    Jami'ai sun ce mutum guda ya samu munanan raunuka bayan da aka daɓa masa wuƙa a ciki a harin da ya auku a unguwar Gare Lyon.

    'Yan sandan Faransa sun ce sun kama wani mutum da suke zargi da hannu a harin.

    Rahotonni sun ce asalin mutumin ɗan kasar Mali ne, to amma ya gabatar wa 'yan sanda takardun Italiya.

    Ba a dai danganta harin nasa da na ta'addanci ba.

    Tuni dai aka dakatar da jigilar jiragen ƙasa tsakanin tsakiya da kudancin birnin Paris zuwa ƙasashen Italiya da Switzerland.

  9. INEC ta dakatar da zaɓen cike giɓi a wasu rumfunan Kano da Enugu da Akwa Ibom

    Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da dakatar da zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin da aka samu na satar da kayan zaɓe da yin garkuwa da wasu jami'an zaɓe a jihohin.

    Sanarwar ta ce wuraren da lamarin ya shafa sun haɗar da rumfuna biyu a mazaɓar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, inda INEC din ta ce aka samu wasu ɓata-gari suka lalata kayan zaɓen.

    A jihar Enugu kuwa da ke kudu maso gabashin ƙasar, hukumar zaɓen ta ce an fitar da takardun sakamako tun kafin fara zaɓe a rumfuna takwas.

    A ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa kuma, INEc din ta ce an samu hatsaniya a rumfunan zaɓe 10, inda 'yan daba suka lalata kayan zaɓe tare da hana gudanar da zaɓen.

    Hukumar zaɓen ta ce ta yi aiki da sashen dokar zaɓen na 24 wajen dakatar da zaɓen.

    Hukumar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike kan lamurran, inda hukumar ta ce tana gudanar da cikakken bincike daga nata ɓangare, don gano ko jami'anta sun saɓa doka a ayyukansu.

  10. CBN ya musanta musanya kuɗaɗen waje da mutane suka ajiye a bankuna zuwa naira

    Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta wasu rahotonni da ke cewa yana shirin musanya kuɗaɗen waje da mutane suka ajiye a bankuna zuwa naira.

    Wasu kafofin yaɗa labarai a ƙasar ne suka yi zargin cewa gwamnatin ƙasar na shirin musanya kuɗaɗen waje da mutane ke ajiyewa a bankunan ƙasar zuwa naira.

    To amma cikin wata sanarwa CBN ɗin ya fitar, ya ce labarin ba shi da ƙanshin gaskiya, kuma an yaɗa shi da nufin haifar da ruɗani a kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta ƙasar, wadda babban bankin ya ce yake ƙoƙarin ganin ta daidaita.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a 'yan watannin da suka gabat ma a an yaɗa irin wadannan ƙarairayi, kuma bankin ya ce ana yin hakan ne da nufin yin zagon-ƙasa ga ƙoƙarin da yake yi.

    "Muna tabbatar wa da al'umma cewa, CBN na bakin ƙoƙarinsa don samar wa mutane ƙwarin gwiwwa, kuma bankin ba zai taɓa yin abin da zai rage darajar kuɗaɗe da tattalin arzikin mutane ba'', in ji sanarwar.

    CBN ɗin ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su yi watsi da waɗancan labaran da ya ce na ''ƙoƙarin kawo ruɗani ga tsarin ajiyar kuɗaɗen waje'', wanda CBN ya ce ana ƙirƙirarsu ne don yin zagon-ƙasa ga tsare-tsarensa.

    Babban Bankin ya kuma gargaɗi masu ƙirƙirar irin waɗannan labaran da cewa hakan ka iya haifar da durƙushewar tattalin arzikin ƙasar.

  11. Zaɓen cike giɓi: INEC ta ce ta samu rahoton hatsaniya a Kano da Akwa Ibom da Enugu

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana sanya idanu tare da gudanar da bincike kan wasu rahotonnin samun hatsaniya a zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwa wasu jihohin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta samu rahoton cewa wasu ɓata gari sun sace kayayyakin zaɓe a wasu wurare a jihohin Kano da Akwa Ibom da kuma Enugu.

    Sanarwar INEC ɗin ta ce an samu tsaiko a rumfuna 10 na ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa a jihar Kano, inda ake gudanar da zaɓen 'yan majalisun dokokin jihar.

  12. Mafi ƙarancin sadaki a Najeriya ya koma kusan naira 100,000

    Kwamitin ganin wata na mai alfarma sarkin musulmin Najeriya ya ce mafi ƙarancin kuɗin sadaki a ƙasar ya koma 99,241.

    Cikin wata sanarwar da kwamitin ke wallafawa a kowace rana a shafukansa na sada zumunta ya nuna cewa a yanzu mafi ƙarancin kudin sadakin shi ne 99,241.

    Ƙaruwar kuɗin sadakin ba ya rasa nasaba da faɗuwar darajar kuɗin Najeriya, wani abu da ke ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mummunan hali.

    Shi dai kuɗin sadaki ana lissafa shi da darajar zinare da azurfa a kasuwannin duniya.

    A watan da ya gabata mafi ƙarancin sadaki a ƙasar bai haura naira 70,000 ba.

  13. Zaɓen cike giɓi: Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a Kaduna

    Wasu al'umomin ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna na gudanar da zaɓen cike giɓi na ɗan majalisar wakilan yankin.

    Wakilin BBC da ya ziyarci garin Rigachikun a ƙaramar hukumar ta Igabi ya ce mutane da dama ciki har da mata da matasa da tsofaffi duka sun fito wajen kaɗa ƙuri'in.

    Ya ƙara da cewa zaɓen ba shi da bambanci da lokacin da aka gudanar da babban zaɓe ta fuskar fitowar jama'a.

    An dai jibge tarin jami'an tsaro a rumfunan da ake gudanar da zaɓukan, don tabbatar da gudanar da zaɓen cuikin kwanciyar hankali da lumana.

  14. Gane Mini Hanya tare da maso lalurar laka

  15. Zaɓen cike giɓi: Mutane na ci gaba da kaɗa ƙuri'a

    Al'ummar da ake gudanar da zabukan cike giɓi a yankunansu, na ci gaba da kaɗa ƙuri'unsu.

    Rahotonni sun ce an samu fitowar masu zaɓe ciki har da mata da dama a wasu yankunan.

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce fiye mutum miliyan 4.5 ne suka karɓi katunan zaɓe a yankunan da ake zaɓen cike giɓi a ranar Asabar, domin maye gurbin 'yan majalisun dokoki na ƙasa da na jihohi da suka mutu, ko kotu umarci a sake zaɓen a wasu yankunan.

    Ana gudanar da zaɓen ne jihohin ƙasar 26, ciki har da jihohi tara da ake sake zaɓen sanatoci biyi, da 'yan majalisar wakilai huɗu, da 'yan majalisun dokokin jihohi uku, don maye gurbin wasu.

    Shugaban hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ana gudanar da zaɓukan ne cikin ƙananan hukumomi 80 na ƙasar, mazaɓu 575, akwatuna 8,934.

  16. A Faɗa A Cika tare da gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi

  17. Hajj 2024: Maniyyatan Najeriya za su biya naira miliyan 4.9

    Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON), ta tsayar da naira miliyan 4.9 a matsayin kuɗin da maniyyatan bana za su biya, domin sauke farali.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Fatima Sanda Usara, ta maniyyata daga jihohin kudancin ƙasar za su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan arewacin ƙasar za su biya naira miliyan 4,699,000.

    Tun da farko hukumar Alhazan ta buƙaci maniyyatan su biya naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin ajiya.

    A shekarar da ta gabata ne alhazan ƙasar sun biya sama da miliyan uku.

    Hukumar ta ce an samu ƙarin kuɗin aikin hajin ne sakamakon tashin farashin dala, wani babban al'amari da ke ci wa tattalin arzikin arzikin ƙasar tuwo a ƙwarya.

    Haka kuma sanarwar ta buƙaci maniyyatan su tabbatar da kammala biyan kuɗaɗensu daga ranar 12 ga watan Fabrairun da muke ciki zuwa ranar 29 ga watan, wanda shi ne wa'adin ƙarshe na karɓar kuɗin.

  18. Blinken zai je Gabas ta Tsakiya karo na biyar bayan fara yaƙin Isra'ila da Hamas

    A gobe Lahadi ne ake sa ran sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken zai kai ziyara yankin Gabas ta tsakiya.

    Wannan dai ita ce ziyararsa ta biyar zuwa yankin tun bayan da Israila ta kai farmaki zirin Gaza domin maida martani kan hare-haren da mayaan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

    Mista Blinken zai ziyarci ƙasashen Saudiyya da Masar da Qatar da Israila da kuma Yamacin Kogin Jordan.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce zai kuma mayar da hankali wajen ganin an sako sauran mutanen da ake garkuwa da su a Gaza tare da ganin an tsagaita wuta domin a kai wa Falasɗinawa kayan agaji

  19. Shugabar babban bankin Turkiyya ta ajiye aiki don 'kare mutuncin iyalinta'

    Gwamnatin Turkiya ta naɗa sabon shugaban babban bankin ƙasar bayan Hafize Gaye Erkan wadda ita ce mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami ta yi murabus ba zato ba tsamani.

    Mrs Erkan wadda tsohuwar ma'aikaciyyar bankin Wall Street ce - da aka ɗorawa alhakin tayar da komaɗar tattalin arzikin ƙasar - ta ce ta ajiye muƙaminta ne domin kare mutuncin iyalinta daga waɗanda ke ƙoƙarin ɓata musu suna

    Rahotonni sun ce wani tsohon ma'aikacin babban bankin ƙasar ya zargi mahaifin Mrs Erkan da nuna son kai kan wasu zarge zarge da aka yi mata.

    A yanzu an naɗa mataimakin shugaba babban bankin ƙasar, Fatih Karaham a matsayin wanda zai maye gurbinta.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan kun wayi gari lafiya, inda zan kasance da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Mu je zuwa...