An gano sabon nau'in sauro da ke zagon-ƙasa ga yaƙi da Maleriya - WHO

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi

    A

    Kotun Shari'ar Musulunci a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

    Wannan mataki dai na nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi a kowanne lokaci za a iya kama shi.

    Barista Ahmad Musa Umar shi ne lauyan da ke kare Dr Idris, ya ce "kotu za ta iya bai wa 'yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci".

    "Kotun ta ce ta ɗage shari'ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami'an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana," in ji Barista Ahmad Musa.

    Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

    Na biyu kuma ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.

    Har yanzu dai ba a fara sauraran wannan shari'a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.

    Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.

  2. Gwamnatin Najeriya za ta mayar da shalkwatar FAAN zuwa Legas

    .

    Asalin hoton, FAAN

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta mayar da shalkwatar hukumar kula da filayen jiragen saman ƙasar (FAAN) zuwa birnin Lagos

    Matakin na ƙunshe cikin wata sanarwa da babbar daraktar hukumar Misis Olubunmi Kuku ta fitar.

    Sanarwar ta ce ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar ne ya bayar da umarnin ɗauke shalkwatar hukumar ta FAAN daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa birnin Legas da ke kudu maso Yammacin ƙasar.

    Matakin na zuwa ne yayin da a farkon makonnan Babban Bankin ƙasar CBN ya sanar da ɗaukar matakin mayar da wasu sassan bankin zuwa birnin na Legas.

    .

    Asalin hoton, FAAN

    • An kori dukkan daraktocin hukumomi kula da sufurin jiragen sama na Najeriya
    • Yadda tsadar tikitin jirgi ta jefa matafiya cikin mawuyacin hali a Najeriya
  3. Wani bam da aka dasa a amalanken Jaki ya kashe ɗan sanda a Kenya

    B

    Wani bam da aka dasa a amalanken jaki da ya fashe a kan iyakar Kenya da Somalia, ya kashe wani jami'in ɗan sada guda kamar yadda rahotanni suka mabata.

    Wasu mutum biyu na daban sun jikkata, kamar yadda jaridar ƙasar suka wallafa a shafukansu na X.

    Rahotanni sun ce jakunan da aka sanya wa amalankensu bam din sun tsallake rijiya da baya.

    Dan sanda da abin ya rutsa da shi, yana kan aikin duba kayayyaki ne da manyan motoci suka ɗauko suka tsallaka Kenya da su daga yankin Mandera, wanda ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Wani bidiyo da aka nuna a kafafen sada zumunta ya nuna yadda hayaƙi ya turnuke sama lokacin da bam ɗin ya fashe.

    Hotunan bayan lamarin sun nuna yadda ɗaya daga cikin jakunan da ya raunata ya tsaya a tsaye.

  4. Kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Nasarawa ranar Juma'a

    .

    Asalin hoton, FACEBOOK/AA SULE, OMBUGADU

    A ranar Juma'a ne kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa da wasu jihohin ƙasar huɗu.

    Sauran jihohin da kotun za ta yanke hukuncinsu gobe sun haɗar da Ogun da Kebbi da Gombe da kuma jihar Delta.

    A watan Oktoba ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamnan jihar Abdullahi Sule na jam'iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.

    To sai dai a watan Nuwamba kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen, inda ta mayar wa Gwamna Abdullahi Sule nasara kamar yadda hukumar INEC ta bayyana a lokacin zaɓen gwamnan jihar na 2023.

    Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri'a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri'a 283,016.

  5. 'Shagunana uku ne suka kone a kasuwar Fanteka'

  6. 'Yan sanda a Kaduna sun kuɓutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi a Abuja

    ..

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kuɓutar da wani mutum da masu garkuwa da mutane suka kama a Abuja suka kuma nufi jihar da shi.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kuɓutar da mutumin wanda aka yi garkuwa da shi a Abuja babban birnin ƙasar ranar Laraba da maraice.

    Rundunar ta ce a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ta samu rahoton yin garkuwa da wani mutum a Abuja, inda aka yi zargin masu garkuwar sun tafi da mutumin da suka sacen zuwa jihar Kaduna.

    Daga nan ne rundunar ta ce jami'anta suka riƙa sanya idanu kan zirga-zirgar motocin da ke shiga jihar daga birnin na Abuja.

    Sanarwar ta kuma ce da misalin ƙarfe 1:00 na rana ne jami'nta suka tare wata mota ƙirar Toyota mai launin ruwan toka, wadda ke ɗauke da mutum huɗu ciki har da direban, inda suka yi zargin masu garkuwar ne a ciki.

    Yayin da mutanen suka ga 'yan sanda sun tare su sai suka yi yunƙurin tserewa, inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe wuta wa 'yan sandan, waɗanda su ma nan take suka mayar da martani.

    Inda ɓangorin biyu suka buɗe wa juna wuta, lamarin da ya sa 'yan sandan suka ƙubutar da wanda aka yi garkuwar da shi mai suna Segun Akinyemi da ke zaune a unguwar Area 3, Garki Abuja, tare da kama ɗaya daga cikin masu garkuwar mai suna Chinaza Philip da ke unguwar Life Camp a Abuja, inda sauran mutum uku suka tsere, waɗanda rundunar ta ce tana ci gaba da farautarsu.

    Rundunar ta kuma ce ta ƙwato motar wadda ta mutumin da aka yi garkuwar da shi ne, da kuma ƙananan bindigogi nau'ikan Pistol da harsasai masu yawa daga wajen masu garkuwar.

    Binciken farko ya nuna cewa maharan sun kama mutumin ne ranar Laraba 17 ga watan Janairu lokacin da ya fita daga gidansa da yamma.

    Maharan na kan hanyarsu ta kai mutumin zuwa Kano a lokacin da 'yan sandan suka kama shi.

  7. Gwamnan Zamfara ya hana sarakunan gargajiya bayar da izinin haƙar ma'adinai

    m
    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Zamfara Dauda LawaL Dare

    Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar da ta haramta wa sarakunan gargajiyar jihar bayar da takardar izinin haƙar ma'adinai a fadin jihar.

    Gwamna Lawal ya sanya hannu kan dokar ne ranar Alhamis a gidan gwamntain jihar da ke Gusau.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ya fitar ya ce gwamnan ya ɗauki matakin ne domin dakatar abin da ya kira ''ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke tarnaƙi ga yaƙi da 'yan bindiga a jihar''.

    Sanarwar ta ce daga yanzu an soke duka takardun izinin haƙar ma'adinai da aka bai wa ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, ko ƙungiyoyin masu haƙar ma'adinai.

    Yayin da yake sanya hannu kan dokar, gwamna Lawal ya ce dokar ta zama dole saboda hatsarin da ke tattare da yawan bayar da takardun izini ga masu haƙar ma'adinan.

    Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne yayin da aka gano cewa bayar da takardun izinin na ƙara dagula al'amuran tsarom jihar, musamman batun 'yan fashin daji.

  8. Somaliya na son Habasha ta janye yarjejeniyar Somaliland

    R

    Asalin hoton, GF

    Ministan harkokin wajen Somaliya ya ce babu maganar sasanci da Habashi har sai ƙasar ta janye yarjejeniyar da ta ƙulla da Somaliland.

    Matakin na zuwa ne bayan Majalisar zaman lafiya da tsaro ta Tarayyar Afirka ta yi kira kan tabbatar da doka da oda sannan ta buƙaci a martaba ƴancin iyakokin ƙasar Somaliya.

    Yarjejeniyar ta 1 ga watan Junairu da aka ƙulla tsakanin Habasha da Somaliland ta fusata Somaliya saboda akwai yiwuwar bai wa Habasha damar amfani da wani ɓangare na iyakar tekun Somaliland.

    Somaliya wadda ke ganin Somaliland a matsayin wani sashe na ƙasarta, ta kira yarjejeniyar a matsayin tsokanar faɗa sannan a ranar Alhamis ƙasar ta ayyana ta da yarjejeniyar da ba kan ƙa'ida.

  9. Yadda Ghana da Masar suka yi atisaye a yau

    Bayanan bidiyo, Yadda Ghana da Masar suka yi atisaye a yau
  10. An cire Sumit Nagal daga Australian Open

    B

    An tisa kyeyar ɗan wasan India Sumit Nagal gida daga gasar Australian Open.

    A zagaye na biyu na gasar ne Sumit ya yi rashin nasara a hannun abokin wasansa na China.

    An kwashe kimanin sa'o'i uku ana gwabza karawar tsakanin 'yan wasan biyu.

    Tun da fari Sumit ne ke taka rawar azo a gani a karawar.

    Amma haka aka yi waje da shi a gasar saboda gazawa da ya yi a zagaye na biyu.

  11. Abin da muka sani kan rikicin Iran da Pakistan

    B

    Da safiyar yau Alhamis ne Pakistan ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya, kwana biyu bayan Iran ta kai hari cikin ƙasarta.

    Ministan harkokin ƙasashen wajen Pakistan ya ce harin ramuwar gayyar ya yi sanadin mutuwar mutane a yankin Sistan na lardin Balushistan.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce mutum tara ne suka mutu sakamakon harin.

    Pakistan ta ce hare-haren sun faɗa kan ''maɓoyar 'yan ta'adda'' a lardin Sistan-Baluchestan na Iran.

    Ta ƙara da cewa tana ''matuƙa martaba'' martabar Iran tare da mutunta ta, to amma abin da ta yi ranar Alhamis ta yi shi ne domin kare martabar tsaron ƙasarta daga kowane irin barazana.

    Ƙasar ta Pakistan ta yi kakkausar suka kan harin ranar Talata da Iran ta kai mata,wanda ya faɗa kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

    Ita dai Iran ta dage cewa ta kai hare-haren ne kan ƙungiyar Jaish al-Adl, wata ƙungiyar 'yan sunni da ke kai hare-hare cikin ƙasarta, ba wai kan mutanen Pakistan ba.

  12. An gano sabon nau'in sauro da ke zagon-ƙasa ga yaƙi da Maleriya - WHO

  13. Rasha ta nemi Iran da Pakistan su kai zuciya nesa

    B

    Rasha ta yi kira ga ƙasashen Iran da Pakistan su yi taka-tsantsan wajen tafiyar da rashin jituwar da ke tsakaninsu sannan su warware rikicin ta hanyoyin "difilomasiyya da siyasa".

    A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta fitar ta ce ta damu da halin rikicin da ke ƙara ƙamari kan iyakar yankin tsakanin Iran da Pakistan.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ƙasashe biyun "ya kamata su haɗa kai wajen ɗaukar matakan yaƙi da ta'addancin da ke addabarsu a wajen iyakokinsu".

    Sanarwar ta jaddada cewa "abin takaici ne rikicin da ke faruwa tsakanin ƙasashen da ke abota da juna".

  14. Sakataren harkokin wajen Amurka zai kai ziyara Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren wajen Amurka, Antony Bliken zai kai ziyara Cabo Verde da Cote d'Ivoire da Najeriya da kuma Angola daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Janairun 2024.

    A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta ƙara inganta haɗin gwiwa tsakaninta da Afirka tun bayan taron shugabannin Amurka da Afirka, wanda ya mayar da hankali kan sauyin yanayi da abinci, da kuma kiwon lafiya.

    Haka kuma, zai jaddada yadda dangantakarsu ta fuskar tattalin arziki da ƙasashen da yake ziyara za ta mayar da hankali nan gaba, da yadda Amurka ke zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka, domin bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi a gida da ma nahiyar, da kuma ƙarfafa Afirka a duniya.

    Bugu da ƙari, Sakataren zai inganta hadin gwiwar tsaro bisa dabi'u iri daya kamar mutunta 'yancin dan Adam, inganta dimokuradiyya, da fadada bin tsarin doka.

    Za a kuma bayyana ƙoƙarin haɗin gwiwa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) don tinkarar kalubalen yankin da kuma goyon bayan shugabannin Afirka wajen warware rikice-rikice, musamman a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

    Wannan ziyarar na nuni da yunƙurin da Amurka ke yi na ci gaba da yin cudanya da Afirka.

  15. Yadda kisan wata matashiya ya fito da ƙiyayyar da ake nuna wa mata a intanet

  16. Hatsarin jirgi a tafkin Vadodara a Gujarat ya kashe yara bakwai

    B

    Yara bakwai sun mutu bayan da wani jirgin ruwa ya nutse a tafkin Harni na Vadodara a jihar Gujarat da ke Indiya.

    A cewar jami’an yankin, jimillar mutane 27 ne ke cikin jirgin, waɗanda yawancin su yara ne su 23, da malamai hudu.

    Bayan afkuwar lamarin, kungiyoyin kashe gobara ta yankin, NDRF da masu ninƙaya suka isa wurin kuma suka fara aikin ceto.

    Kwamishinan ‘yan sandan Vadodara Anupam Singh Gehlot ya ce, “Akwai yara 23 da malamai hudu a cikin jirgin.

    An ceto mutane bakwai. Ana ci gaba da neman mutane shida zuwa bakwai.”

    Vadodara Collector AB Gore ya shaida wa manema labarai cewa kamar yadda bayanai suka ambato ya zuwa yanzu an ceto mutane 11.

    Babban Ministan Gujarat Bhupendra Patel ya bayyana damuwarsa game da lamarin kuma ya umarci jami'ai da su ba da kulawa ga waɗanda abin ya shafa.

  17. Ba a cikin jami'a aka sace ɗalibanmu ba - Jami'ar Al-Qalam

    ...

    Asalin hoton, fb/Al-Qalam

    Jami'ar Al-Qalam da ke Katsina a arewacin Najeriya ta tabbatar da sace wasu ɗalibanta biyu, kwana uku bayan ɓullar labarin, sa'ilin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.

    A cikin wata sanarwa da jami'ar ta fitar a yau Alhamis, ta bayyana cewa duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka yi garkuwa da ɗaliban, amma iyayensu sun tabbatar da sace su a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta daga jihar Neja.

    Sai dai sanarwar ta fayyace cewa "lamarin ba a harabar jami'ar ya faru ba."

    A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne labarin garkuwa da ɗaliban ya karaɗe shafukan sada zumunta na Najeriya, a daidai lokacin da ake jimamin kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata budurwa da suka ɗauke a yankin Abuja, babban birnin ƙasar.

    Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa matsala ce da ke ci gaba da ƙazancewa a Najeriya duk da cewa gwamnati na cewa tana yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan lamarin.

  18. 'Muna cikin tashin hankali bayan ƙarewar wa‘adin karɓo ƴan'uwan Nabeeha'

  19. Gwamnati ta ƙara yawan tuhume-tuhumen da take yi wa Emefiele

    Emiefele

    Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele na fuskantar karin tuhume-tuhume 14, yayin da masu shigar da kara a Najeriya ke kara tsananta shari’ar da aka fara a watan Yunin da ya gabata bayan rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu.

    Lamarin ya sa an dakatar da Emefiele tare da korarsa daga aiki watanni hudu da suka gabata.

    A watan Nuwamba ne dai Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara tuhumar Emefiele da laifuka shida da suka haɗa da zamba da suka kai Naira biliyan 1.2.

    Yayin da aka ci gaba da shari’ar a babbar kotu birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, ya ce an gyara tuhume-tuhumen da suka hada da na jabu, da laifin karya amana, samu ta hanyar karya da kuma bayar da cin hanci da rashawa.

    Sabbin tuhume-tuhumen na zuwa ne bayan rahoton da wata tawagar shugaban kasa ta kafa domin gudanar da bincike a kan zargin aikata ba daidai ba a babban bankin kasar.

    Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya bukaci lokaci domin duba sabbin tuhume-tuhumen kafin shigar da kara.

    Duk da cewa an bayar da belinsa a watan Disamba, tare da takaita zirga-zirgarsa a babban birnin kasar, Abuja kaɗai.

    Amma, a zaman da aka yi na ranar Alhamis, an gyara wadannan takunkumin - kuma a yanzu yana iya tafiya ko'ina cikin kasar.

    • Zanga-zangar nuna adawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya
    • 'Yan Najeriya na kumfar baki a kan 'ɓacewar sabbin takardun naira'
  20. 'Mayar da ma’aikatan CBN Legas zai kawo cikas ga ayyuka'

    ...

    Asalin hoton, CBN/FACEBOOK

    Kungiyar dattawan Arewa ta yi gargadin cewa tafiyar wasu muhimman sassan Babban Bankin Najeriya daga Abuja zuwa jihar Legas na iya haifar da cikas ga ayyukan babban bankin.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne Babban Bankin, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce zai mayar da wasu sassan sa zuwa Legas.

    A cewar wani jami’in bankin wanda ya nemi a sakaya sunansa, shi ne na rage cunkoso a babban ofishin bankin da ke Abuja.

    Da yake mayar da martani game da wannan matakin, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na dattawan arewan NEF, Abdul-Azeez Suleiman, ya bayyana cewa sauya wa wasu sassa na bankin matsuguni, zai haifar da ƙarin farashin kayayyaki da rage haɗin kai da rarrabuwar tattalin arziƙin yanki da tabarbarewar ci gaban tattalin arziki a arewacin Najeriya, da sauransu.

    Sanarwar ta ce, “Zai bukaci zuba jari mai yawa domin CBN na bukatar ware kuɗaɗe domin kafa sabbin ofisoshi da saye ko ba da haya da korar ma’aikata, da sauran buƙatu na samar da ababen more rayuwa"

    “Wannan zai kawo cikas ga kasafin kudin Babban Bankin da kuma karkatar da kayan aiki daga wasu muhimman ayyuka da tsare-tsare.

    • Me ya sa ake ƙarancin takardun naira a sassan Najeriya?
    • Me dawo da canjin dala ga masu shiga da shinkafa Najeriya yake nufi?