Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Daga ƙarshe nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.
Korona ta kashe kusan mutum 10,000 a watan da ya gabata - WHO
Asalin hoton, JIDESANWOOLU
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce kimanin mutum 10,000 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu cikin watan Disamban da ya gabata sakamakon cutar korona.
WHO ta ce har yanzu annobar covid na zama wata babbar barazana duk kuwa da wucewarta.
Hukumar ta ce alƙaluma daga wasu majiyoyi sun nuna cewa an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a cikin watan da ya gabata, sakamakon tarukan bukukuwan kirsimeti, inda aka samu ƙarin yaɗuwar cutar nau'in JN.1, wanda a yanzu ya fi kowane nau'in cutar bazuwa a duniya.
Shugaban hukumar Lafiyar ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''duk da cewa a yanzu cutar ba ta yi wa duniya barazana, amma har yanzu cutar na ci gaba da yaɗuwa tare da kashe mutane a duniya''.
Baya ga rahoton kashe kusan mutum 10,000 cikin watan daga ya gabata, an samu ƙarin kashi 42 na mutanen da aka kwantar a asibiti, yayin da aka samu ƙarin kashi 62 na waɗanda aka kwantar a ɗakunan masu buƙatar kulawa ta musamman idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar da ta gabatan.
Dakta Dedros ya ce wani abin tayar da hankali shi ne an tattaro waɗannan alƙaluma ne daga ƙasashe biyar kawai waɗanda mafi yawancinsu daga nahiyar Turai da Amurka.
"Hakan na nufin akwai yiwuwar cewa an samu ƙari a wasu ƙasashen da ba mu samu rahotonsu ba'', in ji Tedros.
Ya ƙara da cewa ya kamata a ɗauki matakan kariya daga sauran cutuka a gwamnatance da ɗaiɗaiku, ya zama wajibi mu ci gaba da ɗaukar matakai kan cutar corona.
"Duk da cewa mutuwar mutum 10,000 a wata guda, bai kai adadin mutanen da suke mutuwa ba a lokacin ganiyar annobar, dole a ɗauki mataki don magance wannan matsalar'', in ji shi.
Dakta Tedros ya buƙaci gwamnatoci su ci gaba da lura da gwaji da riga-kafin cutar da ake yi musu a ƙasashensu, don tabbatar da cewa yana isa ga mutane.
"Ya kamata mu ci gaba da kira ga mutane da su je domin karɓar allurar riga-kafi tare da yi musu gwaji , su kuma ci gaba da sanya takunkumai da tabbatar da cewa ba a riƙa shiga cikin cunkoson jama'a ba'', in ji shi.
A watan Mayun 2023 ne dai WHO ta ayyana kawo ƙarshen annobar corona a duniya, fiye da shekara uku da ɓullar cutar karon farko a birnin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen shekarar 2019.
Al Shabab ta kama helikwaftan Majalisar Dinkin Duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, MDD na amfani da jirage masu saukar ungulu da dama kamar wannan (wanda ba shi ne aka kama ba) domin gudanar da ayyukanta a ƙasashe da dama kamar Somaliya
Kungiyar Al-Shabab ta kama duka fasinjoji takwas tare da ma'aikatan wani jirgi mai saukar ungulu na MDD da ya yi kuskuren sauka a wani yankin da ƙungiyar ke iko da shi.
Ministan tsaron yankin Galmudug, Maxamed Cabdi Aadan ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.
Majiyoyi daga ƙasar na cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa garin Wisil da ke kusa da sansanin yaƙi na Galmudug, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Al-Shabaab.
A watannin baya-bayan nan gwamnatin Somaliya ta zafafa hare-hare kan ƙungiyar mai alaƙa da al-Qaeda.
Ƙafa ta ɗauke a titunan Ecuador bayan 'yan daba sun auka gidan talbijin
Bayanan bidiyo, Ecuador: Bidiyon 'yan bindiga lokacin da suke yi wa mai gabatar da shirye-shirye barazana kai tsaye a gidan talbijin
An baza sojoji a kan tituna cikin biranen ƙasar Ecuador yayin da al'ummar ƙasar suka cikin wata rana mai cike da tarzomar da ba a taɓa gani ba.
'Yan bindiga rufe da fuskoki sun kutsa kai cikin ɗakin gabatar da labarai na gidan talbijin ana tsakiyar shirye-shirye a birnin Guayaquil kuma an yi ta tayar da bama-bamai a faɗin ƙasar ranar Talata.
Fursunoni sun yi garkuwa da gandirobobi fiye da 130 a gidajen yarin ƙasar biyar.
An ayyana dokar ta-ɓaci tsawon kwana 60 bayan a ranar Litinin wani riƙaƙƙen shugaban 'yan daba ya ɓata ɓat a ɗakinsa da yake tsare.
Babu masaniya a fayyace ko hari kan gidan talbijin ɗin a birni mafi girma na Ecuador yana da alaƙa ɓacewar shugaban 'yan daban na gungun Choneros, Adolfo Macías Villamar, ko kuma Fito, kamar yadda aka fi saninsa da shi.
Bayanai kan gasar AFCON
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Kotu ta aika matashi da babansa a gidan yari bisa zargin kashe limam a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotun majlistare a Kano ta ba da umarnin tsare wani matashi da mahaifinsa, bisa hannu a zargin kashe wani fitaccen limami mai suna Mallam Sani Muhammad.
Yayin da ɗan Yusuf Haruna aka gurfanar da shi gaban shari'a kan tuhumar kisan kai, mahaifin kuma an gurfanar da shi ne gaban alƙali bisa zargin ɓoye ɗan, da kuma kare shi daga fuskantar kamu.
Da aka karanto shari'ar a gaban kotu yau Laraba, lauya mai gabatar da ƙara Barista Fatima Ado Ahmad ta yi zargin cewa a ranar 31 ga watan Disamban 2023 da misalin ƙrfe 7 na yamma, wanda ake ƙara ya far wa limamin mai shekara 45, inda ya caka masa wuƙa mai kaifi a baya, lamarin da kuma ya yi sanadin mutuwarsa.
“Sakamakon haka, Mallam Sani Muhammad ya ji mugun rauni, inda aka garzaya da shi Asibin Ƙwararru na Murtala Muhammad, kafin wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Lauya mai gabatar da ƙara, Fatima Ado Ahmad ta kuma yi zargin cewa a dai wannan ranar, 31 ga watan Disamba, an zargi mutum na biyu da ake ƙara, Haruna Sani da ɓoye ɗansa, bayan ya soki Mallam Sani har ya riga mu gidan gaskiya, abin da ya saɓ wa sashe na 167 na kundin fenal.
Ɗan gidan shugaban ƙasa ya je majalisa don fuskantar bincike a Amurka
An yanke wa tsohuwar babbar mai shari'a ta Laberiya hukuncin rai-da-rai
An yanke wa tsohuwar babbar alkaliyar Labaeriya da wasu mutum uku daga cikin danginta hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samun su da laifin kisan-kai.
An kama su tare da tuhumarsu a watan Yunin 2023 bayan mutuwar Charlotte Musu wadda ta kasance yar'uwar babbar Alkaliyar.
Tsohuwar mai shari'ar ta dage cewar ɓata-gari ne suka kutsa gidanta tare da kashe matar.
To amma a watan da ya gabata yayin da ake yi mata shari'a a birnin Monrovia an gano ita ce ta yi kisan kan tare da taimakon wasu daga cikin danginta.
Lauyoyin da suke kare Misis Scott wadda ta riƙe muƙamin babbar alƙaliyar daga shekara ta 1997 zuwa 2003, sun ce za su ɗaukaka ƙara.
Kotu ta tura tsohon ministan lantarkin Najeriya gidan yari kan badaƙalar dala biliyan shida
Asalin hoton, Facebook/Olu Agunloye
Wata babbar kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta aike da tsohon ministan lantarki da ƙarafa na ƙasar, Olu Agunloye a gidan yarin Kuje zuwa lokacin da za ta kammala nazarin sharuɗan belinsa
Hukumar yai da cin hanci da Rashawa ta ƙasar, EFCC ce ta gurfanar da Mista Agunloye a gaban kotun bisa zargin almundana kudin da ya kai dala biliyan shida a badaƙalar kwangilar wutar Mambila.
A ranar Laraba ne tsohon ministan ya gurfana a gaban mai shari'a Donatus Okorowo, inda ya musanta zargin da ake yi masa.
A ranar 13 ga watan Disamba ne, hukumar EFCC ta ayyana Agunloye a matsayin mutumin da take nema ruwa-a-jallo kan zargin almundahana. Inda daga baya rahotonni suka ce ya miƙa kansa ga hukumar domin gudanar da bincike.
Batun Agunloye ya soma ne tun lokacin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ƙalubalance shi da ya shaida wa 'yan Najeriya inda ya samu izinin hukuma na bai wa kamfanin Sunsire kwangilar dala biliyan shida na aikin tashar wutar lantarki ta Mambila a shekarar 2003.
Yayin da yake mayar da martani ga tsohon ubangidan nasa, Mista Agunloye ya ce ba a tilasta wa gwamnati biyan kuɗaɗen ga kamfanin Sunrise ba ƙarƙashin yarjejeniyar ''ginawa da amfani da kuma miƙa wa hukuma'' ba.
Ya ƙara da cewa an kammala tsare-tsaren kuma wani sabon kamfani ne ya yi aikin, wanda a lokacin ya bayyana cewa yana da jarin ƙasa da dala 2,000.
Matar da ke neman shawara kan yadda za ta rabar da kuɗin gado yuro miliyan 25
Asalin hoton, HANNA FASCHING
Wata 'yar Austria amma asalinta daga Jamus, ta nemi 'yan ƙasar su ba ta shawara kan yadda za ta rabar da ɗumbin dukiyar da ta ci gado daga wajen kakarta.
Marlene Engelhorn, mai shekara 31 ta zaune ne a birnin Vienna, na son mutum 50 'yan ƙasar Austria su tsaida shawara kan yadda za ta rabar da kuɗin da ta ci gado yuro miliyan 25.
"Na ci gadon dukiya mai tarin yawa, da kuma iko, ba tare da na yarfe gumina ba," in ji ta.
"Kuma gwamnati ko haraji ba ta son cirewa a ciki."
Ƙasar Austria ta rushe karɓar haraji a kan kuɗin gado a 2008, ɗaya daga cikin ƙasashen Turai ƙalilan da ba sa karɓar haraji kan kuɗin gado - ko haraji kan dukiyar mamaci.
Misis Engelhorn ta yi imani hakan ba adalci ba ne.
Ita, jinin Friedrich Engelhorn, mutumin da ya kafa kamfanin sarrafa sinadarai da haɗa magunguna na ƙasar Jamus, BASF, kuma ta gaji miliyoyin kuɗi bayan mutuwar kakarta a watan Satumban 2022.
Mujallar Forbes ta Amurka ta yi ƙiyasin cewa dukiyar Traudl Engelhorn-Vechiatto ta kai dala biliyan 4.2, kuma tun kafin mutuwar kakar, Marlene ta bayyana cewa tana son ta rabar da kimanin kashi 90 na kuɗin gadon.
A ranar Larabar nan ne, gayyatar da aka aikawa mutum 10,000 ta fara isa akwatunan wasiƙunsu a Austria.
Ɗan wasan tsakiya na West Ham Luca Paqueta za yi jinya aƙalla ta wata biyu.
Ɗan wasn Brazil ɗin ya ji rauni ne a ranar Lahadi a wasan da suka yi da Bristol na kofin FA, bayan kammala jinyar da ya yi fama da ita a watan Disamba inda ya ji rauni a wasan Arsenal.
Bai buga wasan da suka yi da Brighton ba da aka fafata ba a ranar 2 gawatan Janairu, kuma ya buga minti 14 ne kacal a wasan da suka fafata da Bristol City.
An shirya Paqueta zai ga ƙwararru kan raunin domin su bayyana tsananin halin da yake ciki.
Rashin dan wasan zai zama gagarumin koma baya ga Kocin ƙungiyar David Moyes, ganin irin rawar da ya taka a ƙungiyar a 2023.
Kalli rufa-rufar da aka yi kan ruftawar ginin cocin T.B Joshua
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
BBC ta bankaɗo sabbin hujjoji da ke nuna cewa mai katafaren cocin nan na Najeriya, TB Joshua ya ɓoye gawawwaki, kuma ya razana dangin mutanen da lamarin ya ritsa da su, don yin rufa-rufa kan batun rugujewar ginin wanda ya hallaka aƙalla mutum 114 a shekarar 2014.
Failatu Abdul-Razak: Gwanar da ta kwana goma tana girki ba sauke tukunya
Asalin hoton, PRINCE HAMDAN BANANG
Bayanan hoto, Gwanar girkin Failatu Abdul-Razak ta zama abar ƙauna ga al'ummar ƙasar bayan ta karya tarihin duniya
Gwanar girkin ƙasar Ghana Failatu Abdul-Razak ga alama ta karya tarihin duniya, bayan ta kwashe tsawon fiye da sa'a 227 tana zuba girki babu ƙaƙƙautawa.
Lulluɓe da tutar ƙasar, Failatu Abdul-Razak ta kawo ƙarshen girkin tsawon kwana goma, cikin jinjina da yabo daga cincirindon mutane a ranar Laraba.
Gabanin ta fara girkin nata, ta bayyana fafutukar da ta sanya gaba a matsayin "aikin ƙasa", inda ta ce tana yi ne domin Ghana.
Mutane sun yi ta sowa lokacin da ta fito daga ɗakin girke-girke na otel ɗin da ta yi bajintar a birnin Tamale.
Jami'an da ta yi aiki da su, sun ce za ta aika shaidar aikinta ga kundin bajinta na duniya Guinness World Records don tabbatarwa bisa ƙa'ida cewa ta karya tarihin da aka taɓa kafawa a baya.
Mai riƙe da kambin tarihin na yanzu ɗan ƙasar Ireland Alan Fisher, ya yi girki tsawon sa'a 113 da minti 57.
Gwanar girkin ta Ghana ta ce tana so ne ta tabbatar cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin karya tarihinta, sai ya sha matuƙar "wahala".
'Yan siyasa, ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia, da ɗumbin fitattun mutane kai har da rundunar sojojin Ghana sun bayyana goyon bayansu ga gwanar girkin a tsawon lokacin da ta ɗora sanwa.
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa ta karɓe fasfon tafiye-tafiye na ministar jin ƙai da aka dakatar, da kuma na wadda ta gabace ta, wato Sadiya Umar Farouq, waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu kan zargin aikata ba daidai ba, da dukiyar al'umma.
Haka kuma, EFCC ta kwace fasfo ɗin Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai NSIPA - wadda ita ma aka dakatar bisa zargin almubazaranci da kuɗin da suka kai naira biliyan 44 da miliyan 800 a ƙarƙashin ma'aikatar jin ƙai,.
EFCC ta ce ta kwato naira biliyan 39.8 cikin biliyan 44.8 da ake zargin Halima ta yi sama da faɗi da su.
A ranar Talata ne, hukumar ta tsare Betta Edu tare da yi mata tambayoyi tsawon kusan awa 10 a Abuja. An yi mata tambaya ne kan kuɗin da suka kai miliyan 585 na hukumar.
A yau Laraba ne ake tsammanin Sadiya da Betta da kuma Halima za su sake gurfana gaban hukumar domin ci gaba da yi musu tambayoyi.
Ana fargabar mutum 20 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Rivers
Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutum 20 ake fargabar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya faru a kogin Andoni cikin ƙaramar hukumar Andoni ta jihar Rivers.
Wata sanarwa da shugaban ƙaramar hukumar Andoni, Erastus Awortu ya fitar ce ta bayyana haka, har ma a ciki ya nuna kaɗuwarsa game da faruwar lamarin.
Mummunan hatsarin wanda ya faru ranar Talata da dare, an ce ya ritsa da kwale-kwalen fasinjoji guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa Bonny.
Erastus Awortu ya bayyana ƙoƙarin ƙaramar hukumar tasa na ceto masu sauran kwana da kula da waɗanda suka ji raunuka da kuma gano gawawwakin mamatan da suka riga mu gidan gaskiya.
A Najeriya, hatsarin jirgin kwale-kwale, abu ne da ya zama ruwan dare musamman a yankunan da ke amfani da koguna wajen sufuri.
Hotunan yadda aka ci abinci tsakanin Super Eagles da gwamnan Legas
Gwamnan Jihar Legas ya yi fatan nasara ga tawagar Super Eagles a yayin da take shirin tafiya Cote d'Ivoire domin buga gsar kofin Afrika na 2023.
Gwamnan ya yi fatan nasarar ne yayin da suke cin abinci tare da 'yan wasan Najeriya da kuma jami'an NFF a Legas.
Ya yi fatan haɗin kai da juriya har a kai ga nasara a wannan tafiya da za su yi.
Asalin hoton, @jidesanwoolu
Asalin hoton, @jidesanwoolu
Asalin hoton, @jidesanwoolu X
Asalin hoton, @jidesanwoolu X
'Ba a sako matar Bazoum daga daurin talala ba'
Asalin hoton, Niamey.com
Majiyoyi daga jamhuriyar
Nijar sun tabbatar wa da BBC cewa ba a sako maiɗakin hamɓararen shugaban ƙasar daga daurin talala.
Waɗansu kafafen yada
labarai ne suka ce an sako Hajiya Khadija Bazoum Mohammed kwana guda bayan
sakin dan tsohon shugaban ƙasar Salem.
Tun bayan hambarar da Bazoum a kan mulki, matarsa da dansa suke tare da shi a
inda ake masa daurin talala kafin sako Salem ɗin a ranar Litinin.
Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa har yanzu matar tsohon shugaban ƙasar tana tare da shi a fadar shugabancin ƙasar tun bayan
juyin mulkin soji a cikin watan Yulin bara.
Hakan na zuwa ne bayan da Salem Bazoum mai shekaru 23 a duniya a
shaƙi iskar ‘yanci a farkon wannan makon, daga nan kuma aka garzaya da shi ƙasar
Togo.
Waɗansu majiyoyi a Nijar sun shaida wa BBC cewa hukumomin soji ba su hana
matar Bazoum ta fita daga inda ake tsare da mijinta ba, saboda shi Bazoum kadai
suke tuhuma.
Amma a cewarsu, bisa raɗin kanta ne ita uwargidan Bazoum take zaune
a inda ake tsare da shi.
Juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a cikin watan Yulin 2023 ya janyo
kakkausar suka daga ƙasashen duniya, lamarin da ya sa kungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi, abin da kuma ke ci gaba da mummunan tasiri kan
tattalin arzikinta kenan.
Sai dai a cikin watan da ya wuce ne wata kotun Ecowas da ke zaune a Abuja
ta yanke hukuncin cewa, ci gaba da tsare Bazoum da iyalansa ya saɓa wa doka, kuma
ta bayar da umurnin a mayar da Bazoum din a kan karagar mulki.
China ta shaida wa Amurka ba za ta ba da kai bori ya hau ba kan Taiwan
China ta ce ba za ta bayar da kai bori ya hau ba game da sha'anin Taiwan.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da China ta fitar lokacin da take tattaunawar soji da Amurka bayan kwashe dogon lokaci.
Tun 2021 rabon da China da Amurka su tattauna kan lamuran soji..
Chiuna ta nemi Amurka ta daina 'kai wa Taiwan makamai' kuma ta ɗauki hakan a matsayin abu mai muhimmanci.
Sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da ake sa ran gudanar da zaɓuka a Taiwan nan da kwanaki masu zuwa.
An yi amannar wannan sanarwa za ta iya kara haifar da tankiya tsakanin China da Taiwan.
China na kallon Taiwan a matsayin wani lardi da ke mallakinta, yayin da ita kuma Taiwan take nesanta kanta da zama mallakin Taiwan.
2023 ta fi kowacce shekara zafi a tarihi
Asalin hoton, Global Warming
Masu bincike sun ce shekarar 2023 ta fi kowacce za fi tun lokacin da aka fara bibiyar tarihin zafi a duniya, wanda suka dora alhakin hakan kan matsalar dumamar yanayi.
A cewar hukumar lura da sauyin yanayi ta hukumar Turai, a bara dumamar yanayi takai 1.8 a ma'aunin yanayi na Celsius sama da wanda aka gani a bayan gabanin a fara fitar da hayaki mai bata muhalli da yawa kamar yanzu.
Fashin baƙin BBC ya nuna tun a watan Yuli, a kowacce rana duniya na fuskantar ɗumamar yanayi sama da na baya.
Haka yanayin dumamar cikin teku ya wuce yadda aka taba gani a tarihi.
Yadda ƴar TB Joshua ta tona asirin abubuwan da mahaifinta ya aikata