Amurka ta ƙalubalanci Koriya Ta Arewa a taron gaggawa na MDD

Asalin hoton, AFP
Amurka ta bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a samu tattaunawa mai ɗorewa da Koriya Ta Arewa da burin kawo ƙarshen ayyukan nukiliya a tsibirin tekun Korea.
Amurkar ta bayyana haka ne a taron gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya kan tsaro wanda majalisar ta kira kwanaki kaɗan bayan gwajin da Koriya Ta Arewa ta yi na makamai masu linzami.
Jakadar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya LindaThomas Greenfield ta yi ta nanata cewa Washington ba ta da mugun nufi kan Pyongyang kuma a shirye Amurkar take ta tattauna da jami'an Korea Ta Arewa ba tare da saka wasu sharuɗa ba kafin tattaunawar.
Ta Kuma yi Allah wadai da makami mai linzami na baya-bayan nan da Pyongyang ɗin ta yi gwajinsa.
"Wannan ita ce takalar faɗa ta baya-bayanan nan. Tun a farkon watan Satumba, Koriya Ta Arewa ta yi ta harba makamai masu linzami wanda ciki har da wanda ƙasar ta yi iƙirarin cewa ta inganta shi kuma yana tafiya kamar walƙiya. Waɗannan abubuwan sun saɓa wa doka. Sun saɓa wa dokoki da dama da majalisar tsaro ta yi kuma ba a amince da ayyukan ba". in ji Linda Thomas.
Har yanzu dai jakadan Koriya Ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya bai ce komai ba kan kalaman jakadar Amurka. Sai dai sauran mambobin majalisar irinsu Faransa da Estonia da Ireland duk sun buƙaci Koriya Ta Arewar da ta shiga tattaunawar da Amurka da Koriya Ta Kudu suke ta neman a yi da ita.
Shugaban ƙasar Kim Jong-un ya kuma shaida cewa ƙasarsa ta ƙera makamanta ne domin tsaro ba don ta fara yaƙi ba kuma ba ta da niyyar sadaukar da su.






