Abu huɗu da Shugaba Buhari ya gaya wa ƴan Majalisar Dokoki a wajen liyafa

Buhari da yan majalisar dokoki

Asalin hoton, Presidency

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi liyafar cin abinci da ƴan majalisar dattijai da majalisar wakilan Najeriya a Abuja babban birnin ƙasar.

An yi liyafar ne a ranar Talata da yamma, a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasar.

Dukkan ƴan majalisar dattijai 109 da na majalisar wakilai 360 ne suka halarci liyafar.

A yayin liyafar, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan matsalolin da Najeriya ke fama da su a wannan lokaci.

Ga dai wasu muhimman abubuwa da shugaban ya faɗa a yayin liyafar.

Rashin tsaro

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Shugaba Buhari ya yi magana a kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya, inda ya ce ita ce matsala ɗaya tilo mafi wahala da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro take shafar ayyukan gwamnati na yin abubuwan more rayuwa, da samar wa mutane buƙatunsu da kuma hana masu zuba jari walwala da samar da masana'antu da samar da ayyukan yi.

''Wasu daga cikin mutanen da suke jawo matsalar rashin tsaron nan suna yi ne bisa son ransu, ba tare da wani dalili ba.

''Ko ma dai mece ce manufarsu, to ayyukansu barazana ne ga ƙasarmu.

Wasu labaran da za ku so

Short presentational grey line

Zan yi komai don kawo ƙarshen matsalar tsaro

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Shugaban ya jaddada cewa gwamnatinsa a shirye take ta yi komai don kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar tare da gurfanar da masu laifin a gaban hukuma.

''A wannan yanayin, dole ne mu yi komai da za mu iya, ba tare da mun bari wani abu ya ɗauke min hankali ba, don kawo ƙarshen ayyukansu.

''Ba za mu bari wani abu ya ɗauke mana hankali daga wannan muradin ko daƙile ƙoƙarinmu ba, kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa za mu yi nasara tare a wannan ƙoƙarin," a cewarsa.

Ya yabi Majalisar Dokoki

A wajen taron Shugaba Buhari ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin ƙasar ta tara kan yadda take gudanar da ayyukanta cikin "nuna girma da ƙwarewa, yana mai bayyana ƴan majalisar da "abokan hulɗa wajen gina ƙasa."

Sannan ya yabi jam'iyyun adawa a majalisar kan hadin kan da suke bayar wa wajen shirye-shiryen gwamnati.

''Samun damar shugabancinmu don kyautata wa ƴan Najeriya ya danganta ne da irin hadin gwiwa da za mu yi da ɓangaren dokoki da ɓangaren zartarwa.

''Sa ido kan duba abin da kowane ɓangare ke ciki ba zai zama gayyatar faɗa ba, kuma ba zai zama cacar baki a lokacin tattaunawa don neman shawara ba.

Short presentational grey line

Nasarorin da Majalisar Dokoki ta samu

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Haka kuma shugaban ƙasar ya bayyana wasu nasarori da Majalisar Dokokin ta tara ta samu, kamar dawo da lokacin kasafin kuɗi daga watan Janairu zuwa na Disamba.

Da yin kwaskwarima ga ƙudurin dokar kamfanoni CAMA, da dokar ƴan sanda da dokar kuɗi da sauransu.

Sannan ya yabi shugabancin majalisun biyu ƙarƙashin jagorancin shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan da shugaban Mjalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, saboda sadaukarwarsu a lokacin da ake fusantar matsaloli.

''Kun kuma yi nasara a wajen shawo kan matsalolin da suka yi wa siyasa dabaibayi tsawon shekaru.

''Ina taya ku murna, kuma na gode da dukkan gudunmowarku kan taimaka wa wajen gina ƙasa duk da cewa aiki ne mai wahala," kamar yadda Shugaba Buhari ya ƙara da cewa.

Buhari ya ce dukkan ɓangarorin zartarwa da na majalisa sun hau mulki ne a lokutan da ƙasar ke fama da rashin tsaro sosai.

''Shawo kan wadannan matsaloli na buƙatar tunkarar tambayoyi da dama da aka sha kawar da kai a kansu da suka shafi tattalin arziki da siyasa da shari'a da tarihi wadanda su ne tushen matsalar ƙasarmu.

A ƙarshe ya ce yana fatan ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ɓangaren zartarwa da majalisun ƙasar don ci gaba.

Short presentational grey line

Saƙon shugabannin majalisun

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Taron Majalisar Dokoki

Asalin hoton, Presidency

Tun da fari shugabannin majalisun, Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila sun gode wa shugaban ƙasar kan ci gaban da ya kawo na haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Dokokiu da bangaren zartarwa don ci gaban al'umma.

Sun kuma ce a shirye suke su gaggauta amincewa da kasafin kuɗin 2022 idan shugaban ƙasar ya gabatar da shi a watan Satumba.

Kazalika shugaban majalisar dattaijan ya nemi a samar da ƙarin abubuwan da ake buƙata dan magance matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

Wannan layi ne