Croatia: Mutum biyar sun mutu a girgizar ƙasa

..

Asalin hoton, EPA

Wata girgizar kasa mai karfin 6.4 ta afku a kudancin kasar Croatia, inda aka bayar da rahoton jikkatar mutane da dama da mutuwar mutum biyar.

Wata yarinya mai shekara 12 ta hallaka a garin Petrinja, kamar yadda Firaiministan kasar ya ce yayin da ya ziyarci garin da lamarin ya afku.

Magajin garin na Petrinja ya ce kusan rabin garin ne ya lalace ana kuma zakulu mutane daga buraguzan gine-gine.

Ana iya jin alamun karfin girgizar kasar a Zagreb babban birnin kasar ta Croatia, da kasashen Bosnia da Serbia masu makwabtaka, har ma da can kasar Italiya.

"Muna ta zakulo mutane daga cikin motoci, bamu san ko akwai wadanda suka mutu ko samu raunka ba,'' Darinko Dumbovic, magajin garin Petrinja, ya shaida wa kafar yada labaran yankin.

An kuma bayar da rahoton samun wadanda suka jikkata a garin Sisak.

Cibiyar binciken kimiyya ta kasar Jamus GFZ ta bayar da rahoton cewa girgizar kasar ta kai zurfin kilomita 10 ko kuma mil 6.

Hukumar ayyukan ceto ta kasar Croatia ta ce masu aikin ceto daga fadin kasar sun tafi garin na Petrinja don taimakawa wajen bincike da ceto jama'a.

Firaiminista Andrej Plenkovic, wanda ya garzaya garin na Petrinja, ya ce: "Mun samu bayanai cewa yarinya daya ta hallaka. Ba mu da sauran bayanai game da wadanda suka jikkata.''

"An shiga halin firgici a ko ina, mutane na ta neman 'yanuwansu,'' ya kara da cewa.

A kuma bayar da rahoton samun wadanda suka jikkata a garin Sisak.

Cibiyar binciken kimiyya ta kasar Jamus GFZ ta bayar da rahoton cewa girgizar kasar da kai zurfin kilomita 10 ko kuma mil 6.

Hukumar ayyukan ceto ta kasar Croatia ta ce masu aikin ceto daga fadin kasar sun tafi garin na Petrinja don taimakawa wajen bincike da ceto jama'a.

Firai minista Andrej Plenkovic, wanda ya garzaya garin na Petrinja, ya ce: "Mun samu bayanai cewa yarinya daya ta hallaka. Ba mu da sauran bayanai game da wadanda suka jikkata.''