Ƴan bindiga sun saki mutum 40 da suka sace a Zamfara ranar Asabar

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan sanda sun ce ƴan bindiga sun saki mutum 40 da suka sace a wani ƙauye a Zamfara ranar Asabar.
Ƴan bindigar sun saki mutanen ne bayan da jami'an tsaro da kuma wata ƙungiyar ta 'yan bindigar suka shiga tsakani, waɗanda ke cikin tattaunawar yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke yi, kamar yadda kakakin 'yan sanda Muhammad Shehu ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa ba a biya kuɗin fansa ba.
Ƴan bindiga suna ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya a watannin baya-bayan nan, amma satar mutanen da aka yi a yankin Maru na jihar Zamfara abu ne da ba a faye yin mai girma irinsa ba.
A cikin shekara 10 da ta gabata an kashe fiye da mutum 8,000 a jihohin Kebbi da Sokoto da Niger da kuma Zamfara, a cewar ƙungiyar International Crisis Group.
Hare-haren sun samo asali ne tun tsawon lokacin da aka shafe ana rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman yankin kan albarkatun ƙasa.
Me ya faru ranar Asabar?
A ranar Asabar ne wasu 'yan bindiga suka kai hari tare da sace mutane fiye da 40 a garin Gobirawan Cali, da wasu mutum huɗu a Magami na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a Najeriya.
'Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Asabar da misalin karfe uku da rabi da rana.
Wani da ya tsallake rijiya da baya a yayin harin ya shaida wa BBC cewa, 'yan bindigar sun fara kokarin sace wani mutum ne inda suka yi kokawa da shi daga bisani mutumin ya samu nasara a kan dan bindigar da yake shi ma yana tare da makami a jikinsa.
''Nan da nan sai dan bindigar ya kwace makamin mutumin ya cilla cikin wata gona ya kuma gudu inji mutumin'' in ji wata majiya da ta yiwa BBC karin bayani.
Jim kadan ba a jima ba sai ayarin 'yan bindigar suka shiga garin suka bude wuta suna kuma kora jama'a.
Ganau din ya ce,"Akalla an sace mutum sama da arba'in a yayin wannan hari amma kuma wasu daga cikinsu sun samu sun kubuta".
Ya ce,"Bamu samu mun sanar da jami'an tsaro wannan hari ba saboda duk layukan sadarwar da ake da su basa aiki a garinmu".
Ya kara da cewa "A yanzu garinmu na Gobirawan Cali duk ba kowa an gudu saboda wannan bala'i, don haka mu a yanzu bamu da ranar komawa garinmu har sai gwamnati ta samar mana da jami;an tsaro".











