Al-Shabaab ta An kai wa sojin Amurka hari a Kenya

Asalin hoton, AFP
Mayakan Islama na al-Shabab sun kai hari a sansanin sojin ruwan Amurka da ke kasar Kenya.
Mazauna yankin gabar Lamu sun wayi gari ranar Asabar da jin harbe-harbe a sansanin sojin na Simba, wanda sojojin Amurka da takwarorinsu na Kenya ke amfani da shi.
Sojojin kasar sun ce sun fatattaki maharan daga sansanin.
Kungiyar al-Shabaab mai hedikwata a Somaliya makwabciyar Kenya na da alaka da kungiyar al-Qa'ida.
Al-Shabaab ta kashe sama da mutum 80 a harin bam din da ta kai a Mogadishu babban birnin Somaliya a ranar 28 ga watan Disamba.
Hare-haren kungiyar na ci gaba da karuwa a yankin gabashin Afirka a tsawon shekaru fiye da goma da suka gabata.
Me ya faru a sansanin Simba?
Rundunar tsaron Kenya ta ce maharan sun yi kokarin kutsawa cikin sansanin amma sojoji suka kora su.
Kakakin rundunar ya ce dakarun sun kashe hudu daga cikin mayakan kungiyar kafin sauran su ranta a na kare.
Ya ce an yi nasarar kashe wutar da ta tashi a lokacin harin, kuma al'amura sun daidaita a sansanin.
Al-Shabab ta ce ta yi "nasarar kutsawa cikin sansanin mai tsattsauran tsaro" har "ta kwace ikon wani yanki", kafin jami'an tsaron Kenya su yi amfani da jiragen yaki a kansu.
Barnar da harin ya haifar
Maharan sun lalata jiragen saman sojin Amurka guda biyu da motoci da dama a sansanin, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Al-Shabaab ta ce mayakanta sun kashe wasu sojojin Amurka da na Kenya kuma sun lalata jiragen sojojin guda bakwai a harin.
Wani dan jarida na Muryar Amurka ya wallafa wasu hutuna da ya ce na jiragen sojin da kungiyar ta lalata ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Amurka a Afirka ta ce harin ya dauki sabon salo amma an yi nasarar dakile shi.
Ta ce maharan sun lalata kayan yaki da gine-gine, amma ba ta yi magana game da adadin wadanda harin ya ritsa da su ba.
Amurka ta tsananta ayyukanta na soji a Somaliya tun bayan hawa mulkin shugaba Trump a 2017.
Hare-haren saman da Amurka ta kai a 2019 su ne mafiya yawa.










