Amurka na tuhumar 'yan Najeriya da zamba

Hotunan Shugaba Buhari da Shugaba Trump

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Amurka ta ce lallai sai ta hukunta wadanda ta kama da laifin wadanda wasunsu suna zaune ne a Najeriya

Ma'aikatar shari'ah a Amurka ta tuhumi mutum 80 akasarinsu 'yan Najeriya bisa hannu kan wani gagarumin shirin hada baki don satar miliyoyin dala ta hanyar aikata damfara da kuma halasta kudin haram.

Wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka, wato atoni janar ya wallafa a shafin intanet, ta bayyana tuhuma 252 da aka yi a kan mutanen da ake zargi da ke aiki da wani gungun masu halasta kudin haram da ke da sansani a birnin Los Angeles.

Hukumar ta ce an gabatar da tuhume-tuhumen ne bayan jami'an tsaro a safiyar Alhamis sun kama mutum 14 a fadin Amurka, 11 daga cikinsu a birnin Los Angeles.

Biyu daga cikin wadanda ake zargin dama suna a hannun hukumomi bisa wasu zarge-zargen na daban,inda kuma aka kama daya daga cikinsu a farkon makon nan.

Sauran wadanda ake zargin na zama ne a kasashen ketare, kuma yawancinsu na zaune ne a Najeriya.

Zarge-zargen dai sun hada da cewa mutanen guda 80 da wasu da ke da alaka da su suna amfani da hanyoyin damfara daban-daban.

Hanyoyin da suka hada da tura sakonnin email da sunan kasuwanci, da na soyayya, da kuma wadanda ake tura wa tsofaffi, inda sukan damfari mutane miliyoyin dala.

Bayanan da gwamnatin ta Amurka ta gabatar a gaban kotu sun nuna cewa mazauna Amurka daga cikin wadanda ake zargi da yin damfarar su ne kan karbi miliyoyin dala daga wadanda suka damfara.

Daga nan kuma sai su tura kudaden zuwa abokansu cikin wannan sana'a da ke zaune a Najeriya da kuma wasu kasashen.

Bayanin ya kara da cewa mutum biyu daga cikin wadanda aka kama din na da hannu wajen tura kudi akalla dala miliyan 6, wadanda ake zargin an same su ne ta hanyar damfara.

Sannan kuma ana zargin cewa idan aka hada da sauran wadanda ke cikin wannan harka, sun yi yunkurin damfarar mutane kudi da suka kai dala miliyan 40.

Bayanin ya kara da cewa wadannan mutane kan damfari al'umma ne mazauna Amurka da ma fadin duniya baki daya.

Wadanda suka hada har da kamfanoni manya da kanana da kuma tsofaffin mutane da dama.

Babban alkali na yankin California Nick Hanna ya ce wannan shari'a wani yunkuri ne na kare Amurkawa daga masu damfara ta shafukan intanet, da kuma tabbatar da cewa wadanda aka kama da irin wannan laifi sun fuskanci shari'a.