Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko jam’iyyun hamayyar Najeriya za su iya shawo kan matsalolinsu gabanin 2027?
A Najeriya, wani sabon salo da ba kasafai aka saba gani ba a fagen siyasar kasar ba, shi ne yadda manyan jam'iyyun siyasar ƙasar ke jajanta wa juna musamman ma ADC da batun shari'ar da ya dabaibaye ta da zargin da suke yi wa jam'iyyar APC mai mulki cewar tana yunƙurin mayar da ƙasar tsarin jam'iyyar siyasa daya.
Shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC sun karbi baƙuncin takwarorinsu na jam'iyyar PDP ƙarkashin shugabancin Kabiru Tanimu Turaki, a Abuja a wata ziyara da bangaren PDPn ya kai wa shugabannin ADC.
Taron da aka gudanar tsakanin shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC da na PDP ƙarkashin Kabiru Tanimu Turaki ya gudana ne, bayan wata zanga-zangar lumana da jam'iyyar ADC ta gudanar a ranar Laraba a ofishin hukumar zaɓen ƙasar, INEC, a Abuja, kan abin da 'yan ADCn suka bayyana da mawuyacin hali da dimokuradiyya ke ciki a Najeriya.
Faisal Kabir, ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya ce 'sun ga akwai buƙatar su jajanta mana tare, a wannan gwagwarmaya da ake yi ta tabbatar da cewar Najeriya ba ta koma tsarin nan na jam'iyya guda ba', in ji shi.
Sannan ya ce shugabanin jam'iyyar ta PDP sun tabbatar musu da cewar ba za su ja da baya ba wajen ganin yanƙurin da shugaban Najeriya Bola Tinubua, na mayar da kasar tsarin siyasar jam'iyya ɗaya ba.
Sai dai tun bayan ɓullar bayanai na cewar shugabancin PDP ɓangaren Tanimu Turaki sun kai wannan ziyara ta jaje ga ADC ɓangaren David Mark aka fara raɗe-raɗin cewar manyan jam'iyyun adawar a Najeriya za su haɗe ne waje guda, don ganin sun yi nasarar kawar da jam'iyyar APC daga mulki.
Sai dai Faisal Kabir ya musanta hakan yana mai cewar "ana ci gaba da tataunawa don ganin abun da zai yiwu, wanda shi ne na ceto Najeriya, duk da dai cewar ana tattaunawa kan yiwuwar hakan" a cewar Faisal Kabir.
Me PDP ke cewa?
Ita ma jam'iyyyar ta PDP ta bakin muƙaddashiyar mai magana da yawunta a Najeriya, ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki, Farida Umar, ta ce ziyarar da suka kawo wa shugabannin na ADC ba komai ba ne face ziyarar jaje.
"Dimokardiya da ake so a yi wa karan-tsaye a lalata ta, mu jam'iyyun adawa ba za mu amince da wannan ba, shi ya sa muka je muka yi musu jaje." In ji Farida Umar.
Haka kuma Farida Umar ta ce saɓanin yadda wasu ke yi wa wannan ziyarar jaje da wani salo ne na haɗewar manyan jam'iyyun adawar biyu, har yanzu dukkan jam'iyyun na nan a matsayin jam'iyya, amma babu batun haɗewa.
"Kasan na jima ina fadar cewa, tilas ne sai jam'iyyun adawa mun haɗa kanmu sannan za mu iya yin nasara kan jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, domin itace kaɗai mafita a wajenmu domin idan ba mu ɗauki wannan mataki ba, wankin hula na iya kai mu dare," In ji muƙaddashiyar mai magana da yawun jam'iyyar PDP.
Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron dai sun haɗa da: Gwamnan jihar Oyo Sheyi Makinde, da Atiku Abubakar da shugaban ADC David Mark, sai Abubakar Malami, da Babangida Aliyu, da Peter Obi, Rabi'u Musa Kwankwaso, da Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyun ADC da PDPn.
Masana harkokin siyasa dai na ganin wannan taro da ya gudana tsakanin jiga-jigan jam'iyyun adawar a Najeriya na ADC da PDP tamkar wata ɗan-ba ne aka fara ɗorawa, wanda a ƙarshe zai iya haifar da wata ƙakƙƙarfar haɗakar jam'iyyun adawa da zu iya taka rawar gaban hantsi a babban zaben da ke tafe a Najeriya.