Ƴar Najeriyar mai jagorantar bincike kan tsaron intanet a Amurka

Ƴar Najeriyar mai jagorantar bincike kan tsaron intanet a Amurka

A'isha Ali Gombe wata ƴar asalin Najeriya ce da ke zama tare da gudanar da bincike a ƙasar Amurka.

Ta shahara ne a fannin tsaron yanar gizo, inda ta jagoranci samo wa makarantar da take koyarwa tallafin gudanar da bincike daga cibiyar tsaro ta Amurka.