Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aikinmu kare mutane ne ba kashe 'yan ƙasa ba - Babban hafsan tsaron Najeriya
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya ce rundunar sojin Najeriya, ba ta ji daɗin abin da ya faru a garin Tudun Biri na jihar Kaduna ba, inda jirgin sojoji ya jefa bama-bamai a kan fararen hula.
Janar ɗin ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Juma'a a shalkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja.
A ranar Lahadi 3 ga watan Disamba ne, wani jirgi maras matuƙi na sojojin ƙasan Najeriya ya jefa bam sau biyu a kan masu taron Mauludi a ƙaramar hukumar Igabi, lamarin da ya janyo kakkausar suka a faɗin ƙasar.
Babban hafsan tsaron ya ce ba gaskiya ba ne, maganganun da wasu ke yaɗawa cewa dakarun sojin ƙasar sun kai harin ne, saboda wasu dalilai irin na addini.
Janar Christopher Musa ya ce "Allan da ya halicce mu 'yan Najeriya, bai kawo mu don mu hallaka juna ba." A cewarsa, bambancin haɗa al'ummomi masu bambancin addinai da al'adu a ƙasa guda, shi ne su fahimci rayuwa da ni'imomin da Ubangiji ya zuba a banƙasa.
Ya ce suna ɗaukar matakai don ganin sojojin Najeriya ba su sake aikata irin wannan kuskure ba.
Ku saurari hirar a wannan bidiyo.