Girgizar ƙasar Afghanistan: Abin da ya sa mata da yara da dama suka mutu

Mata 'yar Afganistan ta dawo ganinta bayan raunin da ta samu a girgizar kasar

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Wannan 'yar Afganistan ce, ta dawo da ganinta bayan raunin da ta samu a girgizar kasar, amma sai bayan jiran kwanaki don neman magani
    • Marubuci, By Mahjooba Nowrouzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa kashi 90 cikin 100 na waɗanda girgizar kasar Afganistan ta kashe a ranar 7 ga watan Oktoba mata ne da kananan yara.

Girgizar ƙasar ta afku a lardin Herat da ke yammacin ƙasar, inda ta kashe mutane kusan 1,300 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

BBC ta yi magana da likitoci da shaidu da masu fafutuka waɗanda ke daura alhakin tsauraran takunkumin da Taliban ta sanya a kan yawan mace-macen mata.

Salma, wata likita ce daga Herat, ta iya isa wuraren da abin ya fi shafa don ba da agajin gaggawa ga matan da suka samu raunuka, kuma ta shaida dalilan da suka sa adadin waɗanda suka mutu ya yi yawa.

"Na ziyarci wani kauye da 'yan Taliban suke zaune. Wasu mazan sun ki taba waɗanda suka jikkata ko suka mutu," in ji ta.

Nuna Wariya

Gundumar Zenda Jan, mai tazarar kilomita 40 daga yamma da Herat, ita ce cibiyar girgizar kasa ta farko kuma mafi muni.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa babu gini ko ɗaya da ya tsira a kauyuka 20 masu nisa na tsaunuka.

Galibin mutanen da ke cikin wadannan gine-gine a lokacin da girgizar kasar ta afku mata ne da ƙananan yara.

Mata sun fi kasancewa a gida da rana a cikin karkarar Afganistan, amma lokacin da Taliban suka ƙwace mulki a shekarar 2021, sun sanya wasu tsauraran matakai waɗanda suka haramta wa mata yawancin ayyukan yi da kuma yin karatu bayan makarantar firamare.

Wannan ya la'anci yawancin mata da kasancewa a gida ko da yaushe.

"Maza sun kasance sun fita, ba sa gidajensu, wasu sun yi hijira zuwa Iran don aiki amma matan sune a gida da yaransu kuma sun tsinci kansu a karkashin baraguzan ginin," kamar yadda Salma ta shaida wa BBC.

Girgizar kasar ta mayar da daukacin kauyukan zuwa baraguzan gine-gine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Girgizar kasar ta mayar da daukacin kauyukan zuwa baraguzan gine-gine

Mariam, ƴar shekara 23 kuma mai fafutuka, ta ce ta ga 'yan Taliban suna gargaɗin masu taimakon gaggawa da farko cewa kada su taɓa matan da girgizar kasar ta afku da su.

"Maza na cikin gida ba su da wata matsala game da ceto ko taimakon mata, amma wasu daga cikin 'yan Taliban da ke dauke da makamai ne ba sa barin maza su kusanci su," in ji Mariam.

"Sun kuma hana mata zuwa waɗannan wuraren a cikin kwanaki biyu ko uku da farko, saboda ba sa son haduwar jinsi."

Wani ma'aikacin agaji Abdul ya shaida wa BBC cewa 'yan ta da ƙayar baya ba sa barin maza su taimmakawa mata ko da sun mutu.

Shaidun gani da ido sun shaida wa BBC cewa an binne akasarin matan da suka mutu a rana guda ba tare da an yi wa gawarwakinsu wankan tsarki ba wanda yakan faru a jana'izar musulmi wanda dole ne mace ce za ta yi wa gawar mace wanka kuma iyalai da yawa sun kasa samun wace za ta yi hakan.

Tarnaƙi ga ayyukan agaji

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu fafutuka sun kuma ce takunkumin Taliban ya kawo cikas ga ƙoƙarin da likitocin ke yi na taimaka wa waɗanda suka jikkata.

A ƙarƙashin mulkin masu ta da ƙayar baya, ba a ba wa mata damar zuwa wani wuri ba tare da rakiyar ɗan uwansu ko miji ba.

Fariba, ƴar aikin sa kai mai shekaru 21, tana aiki a sashin gaggawa na asibitin Herat mai gadaje 500. Ta so ta yi gaggawar komawa bakin aiki lokacin da ta samu labarin girgizar kasar.

Shine ta saka doguwar riga da gyale ta bar gida ta nufi asibiti. Amma direbobin tasi suka ƙi kai ta can saboda bat a rufe fuskar ta da niƙabi ba kuma babu safa a ƙafarta, kuma ba ta tare da na miji ɗan rakiya.

Fariba ta ce a makwanni kafin girgizar kasar, 'yan Taliban sun fara ladabtar da direbobin da ke daukan matafiya mata su kadai ko kuma waɗanda suke sanye da kayan kwalliya.

BBC ta samu labarin cewa wasu jami'an Taliban sun ziyarci babban asibitin inda suka buƙaci likitoci mata da su zo bakin aiki, akwai mata da dama da suka samu raunuka kuma likitocin ba su iya jurewa ba, amma ba a san yadda za su yi ba.

Doctors and paramedics treat the injured earthquake survivors in front of the Herat Regional Specialized Hospital

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, "The Taliban has banned male doctors from treating female patients," says Fariba

Shaidun gani da ido a asibitocin bayan girgizar kasar sun ce akwai mata da dama da suka jikkata amma ma’aikatan lafiya kaɗan ne da za su biya bukatunsu, kuma Fariba ta dora alhakin hakan kan masu tayar da ƙayar baya.

"Taliban ta haramtawa likitoci maza yi wa mata marasa lafiya magani. Wannan yana sanya matsin lamba sosai kan gungun likitoci mata da ma'aikatan jinya," in ji ta.

Dr Salma ta kuma ce 'yan Taliban sun hana ta taimakawa wani da ya mutu.

“Na ga wata mata da kanta ya kumbura har sau uku kamar yadda aka saba – tana wurin tare da ɗanta dan shekara 10, likitoci sun ce ta je a duba kan ta domin su ga abin da ya faru da ita. Dr Salma tace.

"Amma ita da ɗanta ba su san inda za su je ko abin da za su yi ba. An samu hargitsi kuma na roki 'yan Taliban a asibiti da su bar ni in shiga don in taimaka, amma ba su yarda ba."

Jawabin Taliban

BBC ta tuntubi 'yan Taliban don jin ta bakinsu, kuma mai magana da yawun ƴan Taliban ya musanta ra'ayin cewa kungiyarsa ta yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa, yana mai cewa zargin yana da alaƙa da ƙa'idojin al'adu a Afghanistan, ba wai ka'idojin kungiyarsa ba.

"Girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 11:00 na safe, maza suna wurin aiki, mata kuma suna gida," in ji kakakin, Zabiullah Mujahid.

"Duk wanda ke da cikakkiyar fahimtar al'ummar Afghanistan ya san cewa kusan kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na mata ba sa aiki kuma suna gida."

Mujahid ya yi iƙirarin cewa tawagogin agaji na Taliban sun isa cikin sa'o'i kadan, wasu kuma jirage masu saukar ungulu ne suka shigo da su, amma sun amince cewa tallafin bai kai ga duk mabuƙata ba.

"Ba shakka wannan babban bala'i ne kuma ya shafi jama'a da dama. Tattalin arziƙin Afganistan bai isa ya biya buƙatun kowa a lokaci guda ba, amma Masarautar Musulunci tana yin iya kokarinta."

Da aka tambaye shi ko sun aika mata da ma’aikatan agaji yankin, bai amsa ba.

Wata mata ta riqe jaririn da aka haifa ba tare da taimakon likita ba ko ma'aikatan jinya ba

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, An haifi wannan jariri ne a wani fili ba tare da taimakon likita ba ko ma'aikatan jinya ba

Dakta Salma ta ce hukumomin agaji sun yi nasarar samar da abinci da barguna, amma har yanzu akwai sauran abubuwa da dama da ya rage ba ayi ba.

Mata da dama da suka jikkata sakamakon girgizar kasar Afganistan na ci gaba da fafutukar ganin an kai musu daukin gaggawa bayan makonni biyu.

“Mata masu juna biyu da yawa sun rasa ‘ya’yansu, wasu kuma sun haihu a fili kuma suna zubar da jini sosai,” in ji Dr Salma.

"'Yan matan sun kasance cikin firgici kuma ba su da tsabtataccen tufafi ko kayan tsafta. Suna matukar bukatar kulawar likita."

(* An canza sunayen masu ba da gudummawa saboda dalilin tsaro.)