Yadda na koyi maganar Gwarawa - Ɗangwari

Yadda na koyi maganar Gwarawa - Ɗangwari

A wannan makon muna kawo muku shirin ..Daga Bakin Mai Ita tare da Muhammad Sani Ibrahim wanda aka fi sani da Ɗangwari ko kuma Indiye a shirin gidan 'Badamasi' da ake watsawa a tashar Arewa24.

Muhammad ɗan ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar Katsina ne to amma an haifi Ɗangwari a unguwar Tudun Wada da ke Kaduna, inda kuma ya girma a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi.

Ɗan wasan ya yi karatun firamare a Rigasar sannan ya yi sakandare a Rigachikum.

Maraici ya saka ɗan wasan sana'ar sayar da maganin gargagjiya domin ya samu kuɗin zuwa makaranta.

Jarumin ya ce ya fara wasan kwaikwayo ne tun daga wasan daɓe a garin Kagarko.

Sai dai kuma Ɗangwari ya ce ba shi da alaƙa da Gwarawa duk da yadda yake kwaikwayon irin maganar gwarawan.

"Ba ni da jiɓi da gwarawa kawai dai na yi makaranta da su ne. Mahaifiyata haifaffiyar Gombe ce sannan mahaifina haifaffen Katsina ne. Abin da ya faru ne shi ne firamaren farko da na yi sunanta Mashi Gwari. Na taso da ƴaƴan Gwarawa. Mai makarantar ma Gwari ne. To ta nan ne dai na fara samun kalmomin Gwarawan."