Robert Prevost ne sabon fafaroma

Fafaroma Leo na 14 zai jagoranci cocin ne bayan sukar da marigayi fafaroma Francis a sha, inda ake masa kallon mai sassaucin ra'ayi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabon fafaroman cocin Katolika, Leo na 14
Lokacin karatu: Minti 2

Fadar Vatican ta sanar da cewa Robert Prevost ne sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.

Shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.

Zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin - wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).

Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

A watan Satumban 2023 aka naɗa shi a muƙamin babban limamin Cocin Katolika wato ''Cardinal'.

Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra'ayin.

An ayyana zaɓarsa a gaban dubban al'ummar da suka halarci fadar Vatican domin shaida zaɓen sabon fafaroman.

Dandazon mutanen sun ɓarke da sowa a lokacin da farin hayaƙi a bayyana wani bututu da ke saman Babban Cocin Kotolikan da ke alamta zaɓar sabon fafaroman.

Manyan limamanin Cocin masu muƙamin Cardinal ne ke zaɓar fafaroma, sannan sai an samu kashi biyu bisa uku na manyan limaman kafin a ayyana wanda ya yi nasara.

A jawabinsa na farko bayan zaɓarsa, Fafaroma Leo 14 ya yi kira da mabiya ɗariƙar Katolika su yi aiki tare ta hanyar amfani da tattaunawa don haɗa kan al'ummar duniya ta hanyar samar da zaman lafiya.

Wane ne sabon Fafaroma Leo na 14

Fafaroma Leo na 14

Asalin hoton, Getty Images

An haifi Fafaroma Leo na 14 a birnin Chicago na Amurka, kodayake asalin iyayensa ƴan Italiya ne, asalin Faransa da Sifaniya.

Robert Prevost ya halarci babbar makarantar sakandire da Cocin St Augustine ke gudanar da ita.

Yayin da ya kai shekara 27 ya tafi birnin Roma domin faɗaɗa karatunsa.

Ya shafe shekaru masu yawa yana ayyukan da suka shafi addini a ƙasar Peru kafin daga baya a ba shi muƙamin archbishop na Chiclayo.

Fafaroma Leo XIV na magana da yaruka da dama ciki har da turancin Ingilishi da Italiyanci.

Waɗanda suka san shi, sun ce yana da ɗabi'ar sauraron jama'a.

Shekara biyu da suka gabata ne marigayi Fafaroma Fransis ya ba naɗa shi muƙamin mai ba shi shawara wajen naɗa sabbin masu muƙaman bishop a faɗin duniya