'Rashin tsaro ya nakasa mu, dusa muke ci domin rayuwa a yanzu'

Asalin hoton, other
Al'ummar wasu yankunan Zamfara da matsalar tsaro ke daɗa rincaɓewa sun ce da dusa da kuma barace-barace suke rayuwa saboda tsananin yunwa.
Rahotanni na bayyana cewa a yanayin da ake ciki a yanzu, matsalar tsaro ta kai bango a Wanke da Magami da 'Yar Tasha da Ɗan Sadau da Ɗan Kurmi da dai sauran sassa na jiha.
Kuma galibin mazauna waɗannan ƙauyuka na cewa suna cikin wani hali irin na ni-'ya-su saboda azaba da hana su sakat da 'yan bindiga ke yi.
Tsawon sama da shekara goma kenan, mazauna sassan jihar Zamfara, na fama da hare-haren 'yan fashin daji waɗanda suke auka wa ƙauyuka da garuruwa, inda suke kashe-kashe da jikkata mutane, tare da sace wasu don neman kuɗin fansa daga danginsu.
Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi ya ce ''Ba ka isa ka taso daga Gusau ka nufi Magami ba, idan babu rakiyar 'yan sa-kai ko sojoji.
"Idan ka taso daga Gusau sai ka sauka a wani gari da ke kan hanya, ka shafe kwanaki amma tsakanin Magami da Janguma kilomita 25, sai dai rashin tsaro ya sa duk wanda ya bi wannan hanya sai ya yi bara''.
'Matsalar tsaro ta nakasa harkokin noma a Zamfara'
Rashin fita gonaki da 'yancin noma, na cikin abubuwan da suka sake kassara mutane yankunan da ma ƙauyukansu.
Monaman da BBC ta tattauna da su, na cewa ba su da ikon yin tafiyar kilomita guda daga garin Magami, sai an sace mutum ko a harbe shi.
''Yanzu haka mutanen garin Magami da ke tsare a hannun 'yan fashin daji sun kai 20, wasu ba za su dawo da rai ba, in ji manomin da ya buƙaci a sakaya sunansa.
"Sannan wasu kuma in an ce a biya kuɗin fansa kafin a sako su, 'yan'uwansu ba su da kuɗin da za su biya, mutane suna shafe tsawon kwana biyu a jere, ba su ci abinci ba".
Manomin ya ce a halin yanzu haka mata da yawa sakin aurensu ake yi saboda rashin abinci, yayin da ƙananan yara suka koma bara.
"Akwai kuma wasu matan da yanzu haka dusar awara suke amfani da ita a matsayin abinci saboda tsananin yunwa".

Asalin hoton, other
Wane mataki ake ɗauka?

Asalin hoton, other
Mazauna garuruwan da suke makotaka da Magami sun bukaci gwamnati ta fara daukar matakan tsaro kan hanyoyin Magami zuwa Gusau da Magami zuwa ɗan Sadau da kuma Magami zuwa dan Kurmi, ta hanyar yiwa jami'an tsaro sansani a gurin don walwalar al'ummar da 'yan kasuwa ta dawo.
Kakakin gwamnan Zamfara Sulaiman Bala Idris ya shaida cewa ana bin matakan da suka kamata domin magance wannan al'amari.
A cewarsa gwamnan jihar, Dauda Lawal ya zauna da shugabannin tsaro na jihar kuma ya gabatar musu da irin bala'in da al'umma suke ciki.
Gwamnan ya na sane da cewa kullum sai 'yan fashi sun tare waɗannan hanyoyi, don haka ya buƙaci su aika jami'an tsaro su dinga sintiri da motoci masu sulke domin samar da zaman lafiya.
Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da matsalar tsaro ya yi wa katutu a tsawon shekaru.











