Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zakatul Fitr - Yadda ake yin zakkar fidda kai
Zakatul Fitr - Yadda ake yin zakkar fidda kai
Yayin da Musulmai a faɗin duniya ke kammala azumin watan Ramadan, wani aikin ibada da ke gabansu shi ne Zakkar fidda kai.
Zakatul Fitr wata zakka ce da ake fitarwa gabani ko kuma a ranar idin ƙaramar sallah.
Sheikh Ibrahim Khaleel, wanda babban malamin Musulunci ne a jihar Kano da ke Najeriya ya ce: "Babbar aikinta (Zakatul Fitr) shi ne tana rufe dukkan kura-kurai ko sakaci ko giɓi da mutum samu a lokacin azumuni watan Ramadan.
Kalli bidiyo domin ganin cikakken bayani daga bakin Sheikh Ibrahim Khaleel.