ICPC ta gargaɗi ƴan majalisar tarayya kan kuɗin aikin mazaɓu

ICPC ta gargaɗi ƴan majalisar tarayya kan kuɗin aikin mazaɓu

Majalisar Dokokin Najeriya kan ware biliyoyin naira a kowace shekara domin gudanar da ayyukan mazaɓu.

Yayin da majalisar ta goma ke fara aiki a Najeriya, hukumar yaƙi da rashawa da ayyuka da suka shafi laifukan kuɗi ta ƙasar, ICPC ta yi tsokaci kan yadda ya kamata a sarrafa kuɗaɗen.