Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Matan Karkara: 'Ina noma don rufa wa ƴaƴa da jikokina asiri'
Malama Biba Tagambara mazauniyar garin Rimi da ke ƙaramar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa manomiya ce wadda ke fafutukar rufa wa ƴaƴanta da jikoki a asiri ta hanyar ɗan noman da take yi.
Labarin Malama Biba ɗaya daga cikin irin halin da mata da ƙananan mata a karkara ke fuskanta da Majalisar Ɗinkin Duniya ke ƙoƙarin nusar da al'ummar duniya dangane da batutuwansu.
Hakan ne ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ware ranar 15 ga watan Okotoban kowacce shekara a matsayin ranar tuna wa da matan karkara.
Taken ranar ta bana shi ne "Yadda matan karkara ke noma domin samun abinci".
Malama Biba wadda da alama mai gidanta ya rasu, inda yanzu haka take zaune da jikokinta da dama waɗanda take ƙoƙarin rufawa asiri.
"Tun da sanyin safiya nake fitowa gona inda zan ɗauko fartanya da sauran kayan aikin gona domin tafiya gona. Haka muke haɗuwa da yara mu cire ciyawa. Ina noma gero da dawa inda nake samun dami fiye da 30 ko 20. Sannan ina noman shinkafa. Nan kuma ina samun kimanin buhu 20. Da wannan muka samun biya wa yara buƙatunsu. Ko haihuwa ko aure." In ji dattijuwar.
To sai dai wani abun da ke ci wa malama Biba tuwo a ƙwarya shi ne yadda ambaliyar ruwa a wannan shekarar ta lalata masu amfanin gona.
"Amma a bana ba na tunanin zan samu amfani mai yawa kamar a baya saboda irin ambaliyar da muka fuskanta."
Kamar yadda mazauna karkara ke fuskantar matsaloli a harkokin noma, ita Malama Biba ta ce "wani lokacin bashi muke ɗauko irin da za mu shuka sannan shi ma haka takin zamani.
Alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa kaso 60 daga cikin 100 na manoma a yankunan karkara mata ne.
Sai dai kuma alƙaluman sun ce kaso 43 na masu fama da yunwa a karkarar mata ne da ƙananan yara.