Shin ko Mourinho zai mayar da Fernabache kan ganiyarta?

Kocin Fernabache Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu magoya bayan ƙungiyar Fernabache na cigaba da hanƙoron ganin nasarorin da ƙungiyarsu za ta samu a ƙarƙashin kulawar fitaccen koci, Jose Mourinho wanda ya karɓi ragamar horar da ƴanwasan ƙungiyar a farkon kakar bara.

Rabon ƙungiyar da lashe kofin gasar Turkiyya tun kakar wasa ta 2013/2014 - kimanin shekara 12 ke nan.

Fernabache ta ƙare a matsayin ta biyu a teburin gasar sau huɗu a jere yayin da a tsawon wannan lokacin kuma babbar abokiyar karawarta a gasar ƙasar wato Galatasaray ta lashe kofin sau uku, lamarin da ke sosa zuciyar magoya bayan Fenerbahchen.

Wannan ya sa ƙungiyar ta yunƙura domin ganin ta koma ganiyarta, tare da rage ƙarfin kaka-gida da Galatasar ta yi gasar, wanda hakan ya sa ta ɗauki fitaccen mai horarwa wanda ake yi wa laƙabi da "Na Musamman" wato Jose Mourinho, domin maye gurbin Ismail Kartal a Yunin 2024.

A lokacin da ta ɗauke shi, magoya bayan ƙungiyar sun yi farin ciki inda dubban mutane suka halarci taron gabatar da shi, kasancewar ƙwararren koci ne wanda ya lashe kofi 21 a Turai.

Kafin komawarsa Fernabache, Mourinho ya jagoranci Roma lashe kofinta na farko a Turai bayan da ta lashe Europa Conference League, ya kuma lashe Eruopa League da Manchester United, sannan ya lashe Champions League a Porto da kuma Inter Milan - shi kaɗai ne kocin da ya taɓa lashe waɗannan kofuna a tarihi.

Rawar da Mourinho ya taka a kakar 2024/2025

Jose Mourinho yayin wani wasan Fernabache

Asalin hoton, Getty Images

Tun kafin ya horar da ƴanwasan ƙungiyar, Mourinho ya bayyana mamakinsa da ƙaunar da aka nuna masa, inda a lokuta da dama magoya bayan ƙungiya na nuna wa koci ƙauna ne bayan ya lashe kofi, amma shi ya fara ganin ƙauna ne daga magoya bayan ƙungiyar tun kafin ma ya lashe komai, don haka ya sha alwashin kawo musu farin ciki.

A kakar wasan Fernabache ta ɗauki sabbin ƴanwasa 18 da Mourinho ke sha'awa, ciki har da fitattu kamar Sofyan Amrabat da Milan Skriniar da Allan Saint-Maximin da Youssef En-Nesyri.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai, duk da cefanen da ta yi, za a iya cewa ƙwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba a kakar farko - saboda ƙungiyar ba ta lashe ko kofi ɗaya ba.

A gasar Turkish Super League, Fernabache ce ta zo ta biyu bayan haɗa maki 84, inda ta yi nasara a wasanni 26 da rashin nasara huɗu sannan canjaras shida.

Ƙungiyar ta yi ƙoƙari a wasanninta da abokiyar hamayya Galatasaray a gasar lig inda ta a filin wasa na Şükrü Saracoğlu da ci 2-0, a gidan Galatasar kuma aka tashi 1-1.

Ɗayar abokiyar hammayar Fernabache wato Besiktas, ita ce ta gagari Mourinho inda suka sha kashi sau biyu hannunsu - Besiktas ta ɗauki maki shida kan Fernabache.

A gasar Europa League, Fernabache ce ta zo ta 24 a teburi kuma hakan ya sa sai da ta buga wasannin cike gurbi da Anderlecht ta Belgium kafin ta tsallake zuwa wasannin ƴan 16.

A zagayen ƴan 16, Fernabache ta fafata ne da Rangers inda a wasansu na farko Rangers ta bi ta har gida ta lallasa ta da ci 3-1.

Ita ma Fernabache dai ta je Scotland ta doke Rangers da ci 2-0, amma da aka je bugun fanariti Rangers ce ta samu nasarar zuwa matakin kwata faynal bayan ci 3-2.

Idan aka duba rawar da ta taka a gasar Turkish Cup, Fernabache ta fita ne a zagayen ƴan 16. Wannan rashin nasara mai ɗaci ne, kasancewar abokiyar hamayyarta Galatasaray ce ta fitar da ita daga gasar. Victor Osimhen ne ya zura ƙwallo biyu yayin da aka tashi 2-1.

'Mourinho na yin nasara ne a kaka ta biyu'

Mourinho ɗauke da kofin Premier League

Asalin hoton, Getty Images

A tarihin Mourinho, yana fi yin nasara ne a kaka ta biyu a ƙungiyoyin da ya je - A kakar sa ta biyu a FC Porto ne ya lashe gasar Primera Liga, haka zalika a wa'adinsa biyu a Chelsea, kaka ta biyu ne ya lashe Premier League sannan a Real Madrid a kakarsa ta biyu ne ya lashe La Liga.

Mourinho dai na fuskantar suka daga masu sharhi da kuma masu kallo kan yawan jawo ce-ce-ku-ce da alƙalan wasa da masu horarwa da sauransu, lamarin da ke sa shi ya samu jan kati a lokuta da dama, inda wasu ke ganin irin waɗannan abubuwa na ɗauke hankalinsa.

Mai sharhi kan wasanni Jonathan Wilson ya ce zuwan Mourinho Fernabache tamkar zuwansa sauran ƙungiyoyin ne.

Jonathan ya ce idan Mourinho ya je ƙungiya, kowa zai fara ƙaunarsa (ƙugiyar da magoya bayanta), sannan ya lashe kofuna a kaka ta biyu, a ta uku kuma a raba gari bayan samun saɓani. Hakan na nufin Mourinho ba ya jagorantar ƙungiya tsawon lokaci yana nasara kamar yadda wasu ke yi.

"Ko da yaushe yana farawa da kyau, ya bar ƙungiya bayan rikici, a tsakiyar zamansa ne ake cin moriya" inji Jonathan.

Mourinho dai na shirin fara kaka ta biyu a Fernabache inda har ƙungiyar ta sayi ɗan wasan Colombia Jhon Duran.

Yanzu kallo ya koma sama, kasancewar an daɗe ana tutiya da cewa kocin ya fi samun nasarori a shekara ta biyu da zuwansa sabuwar ƙungiya, wanda hakan ya sa magoya bayan ƙungiyar suke fatan samun nasara a kakar bana.

Sai dai ita ma Galatassary sake shiri take yi domin cigaba da mamaye sauran ƙungiyoyin gasar.