Su wane ne ƴan tawayen da suka ƙwace iko a birnin Aleppo na Syria?

Matasa uku riƙe da makamai, tsaye a kan wata mota. Makaman da suka riƙe sun haɗa da bindiga ƙirar RPG da kuma AK47.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Sebastian Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East regional editor
  • Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Laraba ƴan tawaye sun ƙaddamar da bore mafi girma a kan gwamnatin Syria.

Zuwa ranar Lahadi sun riga sun ƙwace birnin Aleppo, birni na biyu mafi girma a Syria, kuma sun doshi birnin Hama da ke kudanci.

Harin nasu na ba zata ya tunzura harin Rasha na farko a kan Aleppo tun daga shekarar 2016, kuma ya tilastawa dakarun Syria janyewa daga birnin.

Ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) mai iƙirarin jihadi ce ta jagoranci harin, kuma tana da daɗadɗen tarihi a rikicin Syria.

Su waye Hayat Tahrir al-Sham?

Wani mutum sanye da khakin soji a tsaye cikin wata motar sulke a titin Aleppo.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, HTS sun jagoranci hare-hare a kan Aleppo

An fara kafa ƙungiyar HTS ne da sunan Jabhat al-Nusra, a 2011, kuma tana biyayya ne ga ƙungiyar Al Qaeda.

Jagoran ƙungiyar IS mai iƙirarin kafa daular islama a Syria, Abu Bakr al-Baghdadi, na cikin waɗanda suka kafa ta.

Ana ganin ƙungiyar tana daga cikin ƙungiyoyin da suka fi bai wa shugaba Assad matsala a tarihi.

A 2016, jagoran ƙungiyar, Abu Mohammed al-Jawlani, ya fito fili ya sanar da raba gari da Al Qaeda, tare da rushe Jabhat al-Nusra da kuma kafa sabuwar ƙungiya mai suna Hayat Tahrir al-Sham wadda ta haɗe da sauran ƙungiyoyi irin ta a a cikin shekara ɗaya.

Wa ye mai ƙarfin iko a Syria?

c

An shafe tsawon shekaru ana zaton cewa yaƙin Syria ya zo ƙarshe.

Shugaba Bashar al-Assad ba ya fuskantar wata tangarɗa a mulkinsa a manyan biranen ƙasar, amma akwai wuraren da a ƙarƙashin ikonsa suke ba.

S haɗa da yankin gabashi da Kurdawa ke da yawa, wanda kuma ake iya cewa ba ya ƙarƙashin gwamnatin Syria tun farkon rikicin.

Ana kuma ci gaba da samun rikici a kudanci, inda ake bore ga mulkin Assad, duk da cewa ba a cika bayar da rahoton rikicin ba.

A cikin yankin saharar Syria ma, wata ƙungiya mai iƙirarin kafa daular musulumci ta zamo barazanar tsaro, musamman a lokacin da mutanen yankin ke fita domin yin farauta.

A yankin Arewa maso yamma na Idlib kuma, ƙungiyoyin ƴan tawaye ne ke riƙe da iko, bayan an tilasta masu komawa can lokacin da ake tsakiyar yaƙin.

HTS, ita ce ƙungiya mafi ƙarfi a Idlib, kuma ita ce ta ƙaddamar da harin na ba zata a birnin Aleppo.

Yaƙin cikin gida

An shafe shekaru masu yawa ana gwanbza yaƙi a Idlib inda dakarun gwamnatin Syria ke fafutukar ƙwace iko.

Amma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla a 2020 a ƙarƙashin jagorancin Rasha, mai goyon bayan Assad da kuma Turkiyya mai goyon bayan ƴan tawayen ta kawo kwanciyar hankali a yankin.

Mutane aƙalla miliyan huɗu ke rayuwa a yankin, kuma mafi yawan su ƴan gudun hijira ne daga ƙauyuka da biranen da dakarun Assad suka ƙwace daga hannun ƴan tawayen.

Aleppo na daga cikin wuraren da aka fafata yaƙi sosai kuma a nan ne ƴan tawayen suka sha kayi mafi muni a tarihi.

Domin samun nasara, Assad ya dogara ga ƙarfin yaƙin sama na Rasha da kuma tallafin ƙungiyoyi masu samun goyon bayan Iran da ke tallafa masa, cikin su harda ƙungiyar Hezbollah.

Mutane uku tsaye a kan tankar yaƙi, yayin da wani ke tsaye a ƙasa, kusa da su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kafin wannan makon dai HTS ba ta da tarihin wani yunƙuri na sake tayar da rikicin Syria.

HTS ta daɗe da kafa kanta a Idlib inda ta ke gudanar da gwamnati, duk da cewa rahotannin cin zarafin jama'a na kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnatin na neman karɓuwa.

Ta kuma shafe lokaci tana faɗan cikin gida tsakaninta da wasu ƙungiyoyin.

A yanzu kuma sha'awarta ta faɗaɗa ƙarfin iko zuwa sauran wurare bayan Idlib ya bayyana ƙarara.

Tun da ta ɓalle daga Al Qaeda, HTS ta mayar da hankali ne wajen ƙoƙarin kafa shari'ar musulumci a Syria, ba kamar IS da ta yi yunƙurin mamaye wurere amma ta gaza.

Kafin yanzu dai babu wata alamar cewa tana da muradin sake dawo da rikicin Syria, amma tana ƙara jaddada adawarta ga gwamnatin Assad a ƙasar.