Za a yi gwanjon kwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a 1986

Wani kayataccen lokacin a gasar cin kofin duniya
Bayanan hoto, Wani kayataccen lokacin a gasar cin kofin duniya

Za a yi gwanjon kwallon da Diego Maradona ya zura a raga – a biyu daga cikin cin kwallayen da suka fi shahara a tarihi.

An yi wa kwallon da aka yi daya daga cikin fitattun wasan kofin duniya da aka yi tsakanin Ingila da Argentina a 1986 farashi da ya kai fam miliyan 3.

Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci kofin duniyar da aka yi a Mexico.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci kofin duniyar da aka yi a Mexico.

An sayar da kwallon ga Ali Bin Nasser dan kasar Tunisia, wanda shi ne alkalin da ya busa wasan da ya bayar da kwallon da Maradona ya ci wadda ake kira 'Hand of God' a wasan.

Bin Nasser ya ce: "Wannan kwallon na bcikin tarihin kwallon kafa - wannan ne daidai lokacin da ya dace a nunawa duniya ita."

An yi amfani da kwallon na tsawon minti 90 na wasan, wadda ita ce kwallon da aka fi bayyanawa a matsayin mai cike da rudani idan ana maganar tarihin kofin duniya.

Maradona ne ya fara cin kwallo a wasan - ta hanayar naushinta kuma kwallon ta wuce mai tsaron ragar Ingila Peter Shilton.

Bin Nasser bai duba kwallon ba ya bayar da ita, yayin da dan wasan daga baya ya yi bayanin cewa "rabin kwallon ya taba kan dan wasan rabi kuma kan Maradona".

Kwallo ta biyu da ya ci a wasan ta yi sunan da ake kiranta da "kwallon karni", inda ya yanka mutum biyar daga cikin 'yan wasan Ingila sannan ya yanka Shilton ya ci.

Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci kofin duniyar da aka yi a Mexico.