Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Gara na mutu da wannan rayuwar matsi da muke ciki'
Tsadar rayuwa na ci gaba da tilastawa 'yan Najeriya shiga yanayin da ba su taba tunani ba, inda yanzu suke cin abincin da a baya ko dabbobi ba za a bai wa ba,
A yanzu haka, sakamakon tsadar shinkafa, mutane kan sayi wata shinkafa da ake kira 'Afafata' wadda ta yi kama da damajin kamfani.
Wata mai jego mai cin shinkafar ta ce gwara ta mutu da ta ci gaba da zama cikin matsin rayuwa.
"Wallahi indai zan samu rahamar Allah na gwammace na mutu da wannan rayuwar da muke ciki. Wannan rayuwa ai mutuwarka ce ta fi sauki."
Ana dai sayar da kwanon shinkafa nau'in afafata kan naira dubu daya da dari takwas sabanin lafiyayyar shinkafa wadda farashinta ya wuce haka.
Mai jegon ta ce a hakan ma sai dai su yi awon gwangwani sannan kuma mutum zai kwashe awa biyu zuwa uku yana tsince datti.
"Kana ci za ka ji daci a bakinka.Wallahi ba na iya cinta."