Ku San Malamanku tare da Sheikh Bello Doma

Ku San Malamanku tare da Sheikh Bello Doma

An haifi Sheikh Bello Doma ranar 16 ga watan Janairun 1960 a garin Jeka-da-fari da ke jihar jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

Mahaifinsa Mai'unguwa Doma shi ne hakimin garin Jeka-da-fari.

Malamin ya fara karatun addini a garin Jeka - da - fari a makarantar Baffansa Malam Bello da aka fi sani da Malam Baffa Ali.

Karatunsa Boko

Ya shiga makarantar Furamare ta Jan Kai Furamare School, inda ya kammala a shekarar 1974.

Daga nan ya wuce makarantar Government Secondary School Gwoza, a jihar Borno domin ci gaba da karatun Sakandire, sannan ya zarce Kwalejin Art and Science da ke Bauchi inda ya kamma a 1981.

A shekarar ne kuma ya zarce jami'ar Bayero da ke dake inda ya yi rajista, duk da bai smu damar fara karatun a wanna shekarar ba.

Sheikh Bello Doma ya samu damar zuwa jami'ar Al-Azhar da ke kasar masar, kodayake bai kammala ba.

Ya kuma tafi kasar Saudiyya inda ya yi karatu a harami a wajen malamai daban-daban da ke karantarwa a Haramin.

'Malaman da na tasirantu da su'

Malamin ya ce ya yi karatu a wajen manyan malamai wadan kuma ya tasirantu da su a ciki da wajen Najeriya daga ciki akwai Dakta Bashir Aliyu Umar da Dakta Sani Umar Rijiyar Lemo da Modibbo Hassanb Marwa - wanda ya ce mahaifinsa ma ya yi karatu a wajensa, da kuma malam Sa'idu Imam, da Modibbo Tukur, da Usman Isa Taliyawa

Daga cikin malaman ketare kuwa akwai Sheikh Muhammdul Amin mutumin Ethipioa, da Sheikh Adam Albazi mutumin Nijar, sai Ali Hindi da sauran malamai.

'Abin da ke farata min rai'

Malamin ya ce babban abin ke faranta masa rai shi ne ya ga mutane suna kayutata wa wadansu mutanen.

'Darasin da ke ba ni wahala'

Shehin malamin ya ce darasin da ya fi ba shi wahala a lokacin karatu shi ne darasin Nahawu

'Wasan da na fi so lokacin kuruciya'

Sheikh Bello Doma ya ce wasan kwallon kafa shi ne wasan ya fi burge shi a lokacin da yake kan ganiyar kuruciyarsa.

Ya ce a lokacin da yake makarantar sakandire wasan kwallon kafa ya kasance wasan da ya fi bugawa.

Ya kara da cewa ya kai matakin da har ana tafiya da shi idn tawagar kwallon kafar makaratrasu za ta je wasa da wata makarantar.