Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mace mahauciya mai sana'ar nama a Najeriya
Mace mahauciya mai sana'ar nama a Najeriya
Ba abin mamaki ba ne a ga mace tana harkar fawa a kudancin Najeriya a kasuwa. Amma zai zamo matuƙar abin mamaki a ga irin hakan a arewacin ƙasar, inda aka san maza kaɗai ke wannan sana’a.
Abokin aikinmu Abdussalam Ibrahim Ahmed ya yi kiciɓus da wata mata da ke harkar fawa a tsakiyar inda maza ke sana’ar don neman na rufin asiri.
Ku kalli yadda take aikin a wannan bidiyon: