'Matasan arewa mu rungumi ɗumbin hanyoyin samu na kwamfuta'

'Matasan arewa mu rungumi ɗumbin hanyoyin samu na kwamfuta'

Akwai ɗumbin hanyoyin samun rufin asirin rayuwa, da kuma ƙirƙire-ƙirƙire a fannin fasahar kwamfuta, waɗanda za su bai wa matasa damammakin inganta rayuwarsu, matuƙar suka tashi tsaye.

Fannin ƙwarewar kwamfuta da ƙirƙirarriyar basira ko Artificial Intelligence (AI) na iya samar damammakin dogaro da kai ga matasa mata da maza.

Don haka matashi, Yusuf Muhammad Abdullahi, wanda jami'i ne da ke aiki da wani hamshaƙin kamfanin ƙera kayan lantarki a duniya, Lenovo ke kira ga matasan arewacin Najeriya su tashi su karanci fannonin fasahar kwamfuta.

Ya ce hakan zai bai wa al'umma damar rage ɗumbin masu zaman kashe wando, tare da bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga a tsakanin al'umma.

Ku kalli bidiyon matashin a nan.