Yadda ɗakunan bahaya ke sauƙaƙa wa yara mata hanyar samun ilimi
Yadda ɗakunan bahaya ke sauƙaƙa wa yara mata hanyar samun ilimi
Yara mata ɗalibai a Zanzibar kan ƙaurace wa makaranta sanadiyyar rashin kyakkywan ɗakin bahaya.
Hakan na faruwa ne sanadiyyar rashin yanayi mai kyau da za su tsafatace kansu idan suna jinin al'ada, wanna ya sa sukan yi zaman su a gida.
Sukan gaza sakin jiki wajen yin cuɗanya da sauran ɗalibai a duk lokacin da suka je makaranta alhalin sun al'ada.
Amma yanzu an samu sauyi, bayan da wata ƙungiya mai zaman kanta da ake kira Africa Adventures ta samar da sabbin ɗakunan bahaya 12 a makarantu.
An kawo muku wannan rahoto ne tare da tallafin gidauniyar Bill and Melinda Gates.



