Yadda za ku gane nau'in ciwon kan da ke damunku

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Yadda za ku gane nau'in ciwon kan da ke damunku

Ciwon kai na dɗaya daga ciwuka na yau da kullum da ke damun mutane.

Sai dai likitoci sun yi bayanin cewa akwai nau'ikan da dama na ciwon kai, da ake samu sakamakon dalilai daban-daban.

Dr Jamila Aliyu Dikko, Shugabar Asibitin da ke kula da masu ciwon kai zalla a Abuja ta bayyana matsalar yawan shan maganin ciwon kai.

''Akwai na'ikan ciwon kai har kusana 300, amma waɗanda muka fi sani sun haɗa da wanda gefe guda na kan zai riƙa ciwo, akwai kuma wanda za ka ji kan na sarawa akwai kuma wanda za ka ji kamar an ɗaure maka kan gaba ɗayansa, akwai kuma shi ta gaban ido ake jin ciwon'', in ji likitar.

Likitar ta ce nau'in ciwon kai da ya fi matsala shi ne wanda kana zaune za ka ji kamar an buga maka wani abu a tsakiyar kanka.

''Galibi wannan nau'in na zuwa na matsaloli masu yawa'', in ji ta.

Likitar ta kuma yi kira ga jama'a su daina yawan shan maganin ciwon kai kowane iri, ba tare da sanin irin nau'in ciwon kan da ke damunsu ba.