Ba na son ko maƙiyina ya shiga halin da na shiga – Ummi Nuhu

Ba na son ko maƙiyina ya shiga halin da na shiga – Ummi Nuhu

Sake bayyanar tsohuwar tauraruwar finafinan Hausa Ummi Nuhu, a baya-bayan nan ya sake bankaɗo wani hali da wasu taurarin harkar wasan Hausa ta Kannywood ke shiga bayan sun yi tashe.

Ummi wadda aka haifa a birnin Kaduna ta bayyana yadda ta yi fama da rashin lafiyar da ya kai ga cire rai da wani ɓangare na jikinta ta bayyana wa BBC kuskuren da take ganin ta yi a rayuwarta, wanda ba za ta so na baya su yi ba.