Ranar Hausa: 'Yadda Hausa ke aro kalmomi tare da sauya musu ma'ana'

Ranar Hausa: 'Yadda Hausa ke aro kalmomi tare da sauya musu ma'ana'

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce harshe tamkar abu ne mai rai da ke buƙatar , amfani da sabbin abubuwan da ya ci karo da su a fagen rayuwa.

''Harshe abu ne da ke mirganawa, yake arowa ya kuma ke bayar da aro ga wasu harsunan'', in ji shi.

Ya bayar da misali da wasu kalmomi da harshen ya aro su daga wasu yaruka ya kuma mayar da su nasa, ta hanyar saya musu ma'ana.

Tace bidiyo: Umar Ladu