Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Syria sun haɗe da ma'aikatar tsaron ƙasar

Asalin hoton, Syrian News Agency - SANA
Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke hamayya da juna a Syria sun cimma yarjejeniya na rushe shugabancinsu tare da yin aiki tare da ma'aikatar tsaron ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai ta Syria (SANA) ya rawaito cewa sabon shugaban na Syria, Ahmed al-Sharaa ya gana da ɓangarorin bayan sun amince da rushewa domin haɗewa da ma'aikatar ta tsaro.
Tattaunawar wadda ta samu halartar wakilan ƙungiyar tawaye ta ƙurdawa ta Syrian Democratic Forces da wadda Amurka ke goyawa baya da ke iko da arewa maso gabashin Syria, kamar yadda AFP ta rawaito.
A farkon makon nan ne Sharaa ya ce ba zai ƙyale makamai zai shiga Syria ba " domin kasancewa a hannun waɗanda ba hukuma ba," inda ya ƙara da cewa dokar ta hau kan ƙungiyar ta SDF.
Sharaa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a makon da ya gabata cewa yankin da ƙurdawa ke iko da shi "zai haɗe ƙarsƙashin sabon jagorancin ƙasar" sannan Syria "ba za ta kasance a rabe ba".
'Dole ne Iran ta martaba ra'ayinmu'

Asalin hoton, Getty Images
Sabon ministan harkokin ƙasashen waje na Syria na riƙon ƙwarya, Asaad al-Sheibani ya yi kira ga ƙasar Iran da ta martaba "hukuncin da al'ummar Syria.'
Al-Shaibani a wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Syria, SANA ya rawaito ya ce "dole ne ƙasar Iran ta martaba ƴanci da martabar al'ummar ƙasar Syria.
Ya kuma gargadi Iran ɗin da ta kaucewa "haifar da rikici a Syria" inda ya zarge ta da hannu a "rikicin da ƙasar ta Syria ta yi fama da shi."
To sai dai ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghci ya ce ya yi wuri a fara yanke hukunci kan abin da ke faruwa a Syria, sannan abubuwa za su faru da dama a ƙasar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai jagoran addinin ƙasar Iran, Ali Khamenei ya faɗa a shafinsa na intanet cewa wani gungun "masu son tayar da zaune tsaye," sun yi amfani da yanayin da ake ciki a Syria "suka sake tsunduma ta a wani sabon rikici" bisa haɗin gwiwar wasu ƙasashen waje.
Khamenei ya ƙara da cewa ya yi zaton cewa al'umma Syria za su yi tsaye wajen tunkarar duk mai neman haddasa fitina a ƙasar.
Ƙasar Iran dai ta kasance wadda ke goyon bayan tsohon shugaban ƙasar, bashar al-Assad a lokacin yaƙin basasar da ƙasar ta yi fama da shi a tsawon shekaru 13.
Dakarun Syria sun fara kutsawa cikin Syria
Sojoji Isra'ila sun fara kutsa wa zuwa yankin Suwaysa a Quneitra da ke kudu maso yammacin Syria a ranar Laraba, kamar yadda gidan talbijin na Syria ya rawaito.
Motocin katafila na Isra'ila da sauran kayan ruguzau sun shiga yankin ne sannan dakarun na Isra'ila sun kakkafa shingaye a kudan da madatsar ruwa ta Mantara Dam.
A ranar Talata ne motoci masu sulke suka yi wa sojojin rakiya waɗanda suka shiga tuddan al-Haramoun inda suka kafa wani sansani da zai ba su dmar ganin abin da ke faruwa a kudu maso yammacin Damascus.











