Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
...Daga Bakin Mai Ita tare da Ikram ta Labarina
A wannan mako cikin shirin ...Daga Bakin Mai Ita mun kawo muku tattaunawa da tauraruwa a masana'antar finafinan Hausa, Amina Muhammed Rabi'u.
An haifi Amina a garin Malumfashi da ke jihar Katsina.
Ikram - kamar yadda aka santa a shirin Labarina - ta ca kodayake film ɗin ne ya fito da ita amma film na farko da ta fara yi shi ne Lubna.
Ta kuma fito a fina-finai da dama kamar Jamilun Jidda da Mu'amala da Hujja da Izzar So da kuma wasu.
Amina ta ce wurin da kuɗinta suka fi tafiya shi ne wajen kula da mahaifiyarta da kuma ƴan'unwanta.
Tauraruwa ta ce film din Hausa da ta so a rayuwarta shi ne Mujadala, ''saboda na sha kallon film ɗin sosai''.
Ikram ta ce gwanarta a Kannywood ita ce Zahra Diamond.
Jarumar ta ce babban burinta shi ne yadda ta fara film lafiya ta ƙare lafiya ta kuma yi aure ta haifi ƴaƴa.