Abubuwa uku da suka fi haifar da cutar cancer a faɗin duniya - Rahoto

Wani mai fama da cutar kansar ƴaƴan hanji a Uganda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai fama da cutar kansar ƴaƴan hanji a Uganda
    • Marubuci, James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 4

Za a iya kare aƙalla miliyan bakwai daga kamuwa da cutar cancer a kowace shekara, kamar yadda nazari na farko da aka gudanar a faɗin duniya ya nuna.

A wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta fitar, masana sun yi ƙiyasin cewa cututtukan da ake kamuwa da su na yau da kullum ne ke zama silar kusan kashi 37% na cutar kansa, sai kuma tsarin rayuwar mutum da kuma abubuwan da aka ɗauka daga muhalli, waɗanda kuma duka da za a iya kiyayewa.

Wannan ya ƙunshi kansar bakin mahaifa, wadda ƙwayar cutar 'Human Papilloma Virus' (HPV) ke haifarwa, wadda kuma tana da riga-kafi, sai kuma waɗanda suka kamu da cutar a sanadiyyar shan taba sigari.

Masu binciken sun ce akwai damar sake bunƙasa binciken, wanda zai taimaka domin ceton rayukan miliyoyin mutane daga kamuwa da cutar.

Wasu na'ukan cutar ba za a iya kauce musu ba, ko dai saboda lalacewar asalin ƙwayar halittar gado ta DNA ta yi saboda tsufa ko kuma saboda gadon ƙwayoyin da aka yi daga iyaye da kakanni.

Mai bincike, Dr Isabelle Soerjomataram ya ce, "mutane sun yi mamaki da suka ji cewa kusan duk mutum huɗu a cikin 10 da suka kamu da cutar kansa za a iya kare su daga kamuwa da ita."

Cibiyar binciken cutar kansa ta duniya, wadda ke ƙarƙashin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi nazari kan abubuwa 30 da suke janyo cutar da za a iya kiyayewa.

Daga ciki sun haɗa da shan sigari da haske mai illa ga lafiya wanda ke iya lalata ƙwayoyin halitta na DNA, da ƙibar da ta wuce ƙima da rashin motsa jiki, wanda ke canja yanayin sinadaran aika saƙo na jiki da shaƙar iska mai gurɓata muhalli.

A person holds a phone to their ear as they walk down a street in Noida while wearing a face mask with tuk tuks in the background driving down the street, taken in November 2025.

Asalin hoton, Hindustan Times via Getty Images

Bayanan hoto, Aƙalla cutar kansa miliyan bakwai ne za a iya kare kai daga kamuwa da su

Daga baya kuma cibiyar ta yi nazari kan ƙananan ƙwayoyin cututtuka da suke jawo cutuka irin su HPV da ƙwayar cutar da ke haifar da ciwon hanta wadda ke kaiwa ga kansar hanta da ƙwayar H. pylori da ke janyo gyambo a ciki.

Masu binciken sun yi amfani da ƙididdigar cutar daga shekarar 2022 da kuma abubuwa 30 da suke jawo cutar daga ƙasashe 185 domin gudanar da nazarinsu.

Bayan binciken ne suka daddale cewa abubuwa uku ne suka fi haifar da cutar kansa, inda su kaɗai ne suka haifar da cutar guda miliyan 18 a faɗin duniya. Waɗannan abubuwan su ne:

  • Shan taba sigari: Ya haifar da kansa miliyan 3.3
  • Ƙananan ƙwayoyin cututtuta: Sun haifar da kansa miliyan 2.3
  • Shan barasa: Ya haifar da kansa 700,000
Shan sigari da barasa na cikin abubuwan da ke haifar da cutar kansa da za a iya kiyayewa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shan sigari da barasa na cikin abubuwan da ke haifar da cutar kansa da za a iya kiyayewa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai wannan ƙididdigar ba za ta zama cikakken alƙaluman cutar a duniya da barazanar da take yi ba.

Haka kuma akwai bambanci a yanayin jinsi, inda kusan kashi 45 na kansar da ke kama maza ne za a iya kiyayewa, mata kuma kashi 30, wanda wataƙila ba zai rasa nasaba da cewa maza sun fi shaye-shaye ba.

Matan da suke rayuwa a turai sun fi kamuwa da kansa a sanadiyar shan sigari, sai kuma ƙananan ƙwayoyin cututtuka da ƙiba da ta wuce ƙima.

A yankin saharar Afirka kuwa, ƙananan ƙwayoyin cuta da ke haifar da cutuka na yau da kullum ne suke zama silar samun kashi 80% na cutar kansa da za a iya kare kai daga kamuwa da ita.

Wannan na nuna cewa duk matakan da za a ɗauka wajen magancewa ko daƙile cutar kansa, dole a yi la'akari da yankuna da ma ƙasashe.

A rahoton, wanda mujallar "Nature Medicine" ta wallafa, an nuna cewa kansar huhu (mai alaƙa da shan sigari da shaƙar gurɓataccen iska) da kansar ciki (mai alaƙa da ƙwayar cutar H. pylori) da kansar bakin mahaifa (mai alaƙa a ƙwayar cutar HPV) ne suke haifar da kusan rabin cututtukan kansa da za a iya kiyayewa.