Me jarirai suka yi da Lucy ta kashe bakwai?

Me jarirai suka yi da Lucy ta kashe bakwai?

An yanke wa Lucy Letby hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan an same ta da laifin kashe jariri bakwai da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu shida.

Duk da haka, al'ummar Birtaniya na ta yin tambayoyi game da shari'ar mai kisan gillar ɗauki ɗai-ɗai mafi muni a tarihin baya-bayan nan na ƙasar - ciki har da masu tunanin ko akwia buƙatar sake shari'a ko ana iya ɗaukaka ƙara.

Da gangan, Lucy Letby ta riƙa yi wa jarirai allura da sauran iska a cikin sirinji, kuma ta riƙa yi wa wasu ɗura da ƙarfi, sannan ta bai wa jariri biyu guba da sinadarin insulin.

Bayan yanke mata hukunci, Lucy Letby ba ta nuna wata alamar nadama ba.

British serial killer

Asalin hoton, Cheshire Police