Yadda rashin abinci ke hana yaran Tigray zuwa makaranta

Yadda rashin abinci ke hana yaran Tigray zuwa makaranta

Sama da mutum 100 ne yunwa mai tsanani ta kashe a yankin Tigray na ƙasar Habasha, lamarin da ke tursasa wa yara ficewa daga makarantu domin neman ƴaƴan itace a daji da ganyayyaki domin ci.

Wasu daga cikin yaran kuma sukan yi tafiya mai nisa zuwa rafi domin neman zinare a ƙoƙarin nemo hanyoyin kauce wa yunwa.