Bidiyon yadda mata suke kona hijabansu don bijire wa 'yan Hisbah a Iran

Bidiyon yadda mata suke kona hijabansu don bijire wa 'yan Hisbah a Iran

Mutuwar Mahsa Amini a hannun 'yan hisba Iran ta janyo zanga-zanga a fadin kasar.

'Yan Hisbah sun kama matashiyar, mai shekara 22, saboda ba ta sanya kallabinta yadda ya kamata ba.

Sai dai mutuwar tata ta janwo kakkausan suka daga wasu 'yan kasar.