Yadda aka ajiye gawar Fafaroma Francis a bainar jama'a

Yadda aka ajiye gawar Fafaroma Francis a bainar jama'a

Fadar Vatican ta fitar da hotunan marigayi Fafaroma Francis a wani buɗaɗɗen akwatin gawa, an sanya masa jar alkyabba da hular Fafaroma.

An ajiye gawar a cocin Casa Santa Marta, wato gidan Fafaroman da ke Vatican.

Da safiyar ranar Laraba ne za a ɗauki gawar zuwa cocin St Peter's Basilica, inda za a ajiye gawar domin mutane su yi mata ban-kwana har zuwa lokacin da za a yi jana'iza.