Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ina cikin murna tare da al'ummar jihar Kano da magoya bayana'
'Ina cikin murna tare da al'ummar jihar Kano da magoya bayana'
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce yana cikin murna da farin ciki tare da al'ummar jihar Kano da duka masoyansa na Najeriya da ma duniya baki ɗay bisa nasarar da ya samu a kotun ƙolin ƙasar.
Yayin wata hira da BBC, Abba Kabir Yusuf ya ce yana gayyatar Nasiru Gawuna da sauran ƴan takarar gwamna a Kano su zo a haɗa kai domin gyara jihar.
A ranar Juma'a ne kotun kolin ƙasar ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kano a zaɓen ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023 da aka gudanar