Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya attajiran duniya ke gurɓata muhalli?
Ta yaya attajiran duniya ke gurɓata muhalli?
Ƙungiyar Oxfam wadda ta yi nazari a kan mutanen da ayyukan su suka fi samar da hayaƙin carbon mai gurɓata muhalli.
Oxfam ta duba yawan hayaƙin Carbon da attajirai 41 ke samarwa, inda ta gano cewa a cikin minti 96 kacal, attajiri ɗaya na fitar da sinadarin Carbon da talaka zai fitar a tsawon rayuwarsa.
Ƙungiyar ta nemi a sanya haraji mai tsauri kan kayyaƙin attajirai masu gurɓata muhalli domin amfani da kuɗin wajen yaƙi da sauyin yanayi.