Shirin da muke yi don bunƙasa kiwon lafiya a Najeriya - Pate

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Shirin da muke yi don bunƙasa kiwon lafiya a Najeriya - Pate

Ministan Lafiya na Najeriya Muhammad Ali Pate ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya kaɗai ba za ta iya shawo kan matsalolin lafiya ba a ƙasar.

Farfesan wanda ya fara aiki a watan Agusta, ya ce akwai buƙatar gwamnatocin jiha su taimaka wajen kyautata fannin lafiya, yana mai cewa tuni wasu ƙungiyoyi suka fara taimakawa wajen cimma hakan.

A cikin wannan hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, Farfesa Pate ya ce abin da suka saka a gaba shi ne kyautata cibiyoyin lafiya a matakin farko, waɗanda ake da su a lungu da saƙo na Najeriya.