Me ya sa Trump ke son ganawa da Putin a Saudiyya?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Manal Khalil
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 7
Lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin a kasar Saudiyya kan yadda za a kawo karshen yakin Ukraine, mutane da dama sun rika cewa wane dalili ne ya sa ya zabi kasar ta Saudiyya domin yin tattaunawar?
Bai fadi lokacin da za a yi tattaunawar ba, sai dai ya ce yana iya yiwuwa za a yi ta ne nan kusa.
Har ma ya ce yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mogammed bi Salman shi ma zai iya halartar tattaunawar.
Wannan bayani da Trump ya yi ma zuwa ne sa’o’i kadan bayan tattaunawar da ya yi ta waya da shugaban Rasha, Vladimir Putin da kuma na Ukraine, Volodymyr Zelensky, a kokarin lalubo hanyar samar da zaman lafiya.
A wani bayani da ta fitar, Saudiyya ta yaba da tattaunawar waya da aka yi tsakanin Trump da Putin, da ma batun shirin yin taron a kasar.
“Saudiyya na sake tabbatar da konarinta wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa tsakanin Rasha da Ukraine,” in ji sanarwar.
Kasar da ba ta nuna barayi ba
Game da tattaunawa tsakanin Trump da Putin, bayanai sun nuna cewa kasashe kamar China da Hadaddiyar Daular Larabawa sun nuna aniyar zama masu masaukin baki.

Asalin hoton, Reuters
”Akwai basira a zaben da Trump ya yi wa Saudiyya a matsayin inda zai gana da Putin domin za ta zamo wuri ne na ‘yan ba ruwanmu,” in ji Paul Salem, mataimakin shugaban a cibiyar nazarin Gabas ta takiya da ke Washington.
Salem ya ce gudanar da taro a wata kasar nahiyar Turai ba zai yiwu ba sanadiyyar matsayar yankin na goyon bayan Ukraine.
”Wata kila in da za a yi la’akari da al’ada, za a zabi Geneva a matsayin inda za a gudanar da tattaunawar. Sai dai ci gaba da tabarbarewar dangantaka tsakanin Rasha da Switzerland da sauran kasashen Turai, na daga cikin dalilan da suka sanya Trump ya zabi Saudiyya,” in ji Dakta Khattar Abou Diab.
Haka nan ya bayyana cewa Putin ya aminga da Rasha sosai, kuma kasar ba ta sa hannu kan dokar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba, wato ICC.
A 2023 ne kotun ICC ta bayar da sammacen kama Putin, bisa zargin shi da tafka laifukan yaki sanadiyyar mamayen Ukraine. Masana na da yakinin cewa Trump zai iya yin tafiya zuwa China ba tare da shayin ko za a kama shi ba.
Yin sulhu
Saudiyya na cikin kasashen da suka yi kokarin cimma yarjeje tsakanin Rasha da Ukraine domin yin musayar fursunoni, wani abu da ya sanya duka kasashen biyu suka aminta da ita.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
A cikin yan kwanakin nan ne Saudiyya ta shiga tsakani wajen ganin Rasha ta saki wani malamin makaranta ba’amurke, Mark Fogel bayan kwashe kimanin shekara uku yana a tsare.
Yariman Saudiyya ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an sake shi, in ji jakadan Amurka a Gabas ta tsakiya, Steve Witkoff.
Saudiyya ta sha yin maraba da Putin da kuma Zelensky a lokuta daban-daban, kuma ta sha yunkurin ganin an samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
A kan haka ne ma ta taba hada wani tarin sulhu kan lamarin a birnin Jidda tare da gayyatar wakilai daga bangarorin biyu.

Asalin hoton, Reuters
Lokacin da ya kai ziyara a Saudiyya cikin watan Disamban 2023, Yarima MBS ya bayyana Putin a matsayin “bakon girmamawa na musamman ga Saudiyya, ga gwamnati da al’umma baki daya.”
Masani kan lamurran yankin Gulf, Abdullah Baaboud ya ce Saudiyya na son zamewa mai yin sulhu tsakanin kasashen duniya ne, kamar Oman da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma Saudiyyar za ta so yin hakan domin karfafa tasirinta a yankin.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Baaboud ya ce karbar bakuncin Trump da Putin zai iya zama wata alfarmar diflomasiyya ga Saudiyya, musamman yadda hakan zai yi tasiri ga tattaunawa na gaba kan wasu manufofi da suka shafi Saudiyyar da Amurka, kamar batun amincewa da yarjejeniyar da ake kira ‘Abraham Accords’ wadda ta sulhunta kasashen Larabawa hudu da Isra’ila.
Paul Salem kuwa na ganin cewa Trump na hanzari ne wajen karfafa dangantakar Amurka da Saudiyya bisa dalilai na kudi da zuba jari da tattalin arziki, kuma ya ce akwai alamun Trump na da manufar samar da wata yarjejeniya tsakanin Amurka da Saudiyya da kuma Isra’ila ne a nan gaba.
Dr Nisal Choucair, farfesa kan sadarwa, ya bayyana cewa Saudiyya na da muhimmanci ga Trump wajen tabbatar da manufofin Amurka a Gabas ta Tsakiya, musamman ta fannin rikicin Isra’ila da Falasdinawa.
Ya ambato batun matsin da Amurka ke son sanya wa Saudiyya a baya-bayan nan bayan furucin Netanyahu game da kwashe Falasdinawa zuwa Saudiyya, lamarin da Saudiyyar ta yi wancakali da shi.
Batun man fetur
Amurka ce kasar da ta fi kowace a duniya samar da man fetur, inda Saudiyya da Rasha ke a matsayi na biyu da na uku.
Lokacin da yakin Rasha da Ukraine ya shafi bangaren samar da man fetur na duniya, Saudiyya ta taka rawa sosai wajen samar da mafita.

Asalin hoton, Getty Images
A watan Disamban 2024, kasashe takwas daga cikin 22 na kungiyar kasashe masu samar da man fetur ta OPEC+, wadanda suka kunshi Saudiyya da Tasha suka yanke hukunci rage yawan man fetur din da suke samarwa kasancewar suna fuskantar rashin kasuwa da kuma gogayya daga kasashen da ba su a cikin kungiyar.
Saudiyya da Rasha na da manufofin da suka hada su wuri daya a matsayin kasashen masu samar da man fetur, in ji Abdullah Baaboud. Ya ce yana sa ran ganawar Trump da Putin a Saudiyya ba za ta tsaya kan kawo karshen yakin Ukraine kawai ba, amma za ta tabo batun farashin man fetur a duniya da kuma alaka da tattalin arziki.
“Akwai yiwuwar Trump zai nemi sauki kan farashin danyen man fetur domin amfanin kamfanonin Amurka, musamman bayan da a baya ya nemi da a sassauta farashin,” in ji shi.
Ya fito da yadda Trump ya fifita amfani da makamashin da aka saba da shi a maimakon makamashi maras gurbata muhalli, wanda hakan zai yi daidai da matsayin Saudiyya wadda ta kasance daya daga cikin kasashen duniya masu fitar da danyen mai zuwa kasuwannin duniya.
Manufofin kasa da kasa
Tafiya ta farko zuwa wata kasa da Trump ya yi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2017 ta kasance ne zuwa Saudiyya, wanda hakan ya kara daukaka matsayin kasar ta Saudiyya a harkar diflomasiyya ta duniya.

Asalin hoton, EPA/SAUDI PRESS AGENCY HANDOUT
Trump ya nuna alamun cewa akwai yiwuwar tafiyarsa ta farko zuwa kasar waje a wannan wa’adin mulkin nasa za ta iya kasancewa zuwa Saudiyya ne, kuma ya riga ya tabbatar da manufarsa.
“Idan Saudiyya tana sin ta sayi kayanmu na kimanin dala biliyan 450 ko 500, ina ganin zan je can,” kamar yadda ya fada wa manema labaru a ofishin shugaban kasa cikin watan jiya.
Kwanaki kadan bayan haka, yarima mai jiran gafo na Saudiyya ya ce kasarsa na son zuba jarin da ya kai dala biliyan 600 a Amurka cikin shekaru hudu masu zuwa.
Dr Nidal Choucair na ganin cewa Trump na kallon Amurka a matsayin kawa mai muhimmanci a bangaren tattalin arziki
Haka nan kuma Trump na son sake cusa kanta a wurin Saudiyya da kuma yankin baki daya a wani bangare na gasar da ke tsakanin Amurkar da China, in ji Dr Khattar Abou Diab, farfesa a harkar kasa da kasa.
Yayin da ake sukar Saudiyya kan zargin take hakkin bil’adama, Abou Diab da Choucair na ganin cewa sauye-sauyen da kasar ta bullo da su a baya-bayan nan, kamar soke ayyukan hisba da kyale mata su tuka mota, sun daukaka martabar kasar a idon duniya, wanda hakan zai rage mata yiwuwar fuskantar matsi daga gwamnatin Donald Trump.










